CHAPTER 32

568 64 10
                                    

Facebook page: https://mobile.facebook.com/Eloquence-Writers-266267857577087/?ref=opera_speed_dial&_rd

✨✨✨✨✨✨✨
KUDURI KO MANUFA
✨✨✨✨✨✨✨

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

©2018

FOLLOW ME ON WATTPAD@JANNAH JAY8

*DEDICATED TO MY VERY OWN SIS MERMA*

109-110

Har aka Kira sallar la'asar  basuji bayanin komiba daga bakin DR'S din hakan shiyayi nasarar Kara dagula lissafinsu dakyar suka wuce masallaci

JAHEED tunda ya bar asibitin sai sallar la'asar ya fito dashi don  haka baisamu damar kiran SA'ADARTY ba itama Sam tamanta da kiransa ADDU'O'I kam yashasu daga bangarensu,  suna fitowa sukaga  UNCLE SERLIS da MUNEERA sunzo dubashi ta dawo daga NYSC CAMP idonta taf da kwalla tana sharesu da handky dake hannunta, kamota COINS yayi yana buga bayanta na  rarrashi ganin damuwarta kan yaronshi abun yamashi dadi

Sai karfe 5:30 na yamma JAD yasami nutsuwa sosai DR  SADIA tace zasu iya ganin sa amma karsu bari yayi abu dakarfi kaman dariya ko magana dakarfi sosai cikin farin ciki suka shiga AFFA da MAMI Sai UNCLE SERLIS suna shiga MUNEERA dake cike da takaicin komi sai ayitayi da SA'ADARTY kaman wata yar uwarsu ko magana takiyi mata saima harararta da take sai da iyayen suka jima sannan sai AFFA ya kirasu yace suzo su Ganshi

Ba abunda JAD yake muradin gani irin SA'ADARTY duk da kuwa tabada gudummuwa wajan shiga cikin halin dayake amma zuciyarshi daya alakanta da mara sanin masoyi sai kara ingizarsa take kan mahaukacin sonta,yana tsaka da tunani ya tsinkayi muryar MUNEERA tana cewa " YA JAD ya jikin naka" ta fada tare da matsowa kusa dashi iyayen kuma sun matsa can gefe inda AFFA ke shaidawa SERLIS abunda ya faru MAMI kuma nagefe tana kallon su

MUNEERA saka hannu tayi tana shafa kwantaccen sumar dake kan hannunshi tayi cike da marairaicewa tace " YA JAD meye ya faru haka yake wahalar mana dakai ? Kodai akwai abunda bakaso ne acikin gidan" ta karasa fada tana kallon side din SA'ADARTY

Itakam SA'ADARTY tunda suka shiga banda sannu bata kara cemashi komiba saima sunkuyawa da tayi tana danne2 da phone dinta tamkar batasan da komi agabantaba

Wannan shariyar da tayi bakaramin batawa JAD rai tayiba, lokaci daya yaji karaya akan bazata taba sonshiba da alama wancan jakus din yaron ya hure mata kunne

MUNEERA so tayi ya tankamata tace kila ko zaman SA'ADARTY ne yasashi, baisamu daman yimata magana saima shiru da yayi saboda damuwa data addabeshi

A OFFICE DIN DR SADIA

Agaskiya AFFA matsalar JAD guda biyuce dama kunsanshi da ASTHMA yanzu ga zuciyarshi na shirin tabuwa, damuwa tana iya tadawa dan adam kowanne irin ciwo dake jikinsa shiyasa ASTHMA din ke tashi kuma ta hade da awan jini dukansu masu barazana ne da numfashin dan Adam, tabuwar numfashi kuma bakaramar gagarumar matsala bace

Ba wanda ya iya furta komi acikinsu, shikam COINS kama habarshi yayi cike da damuwa. Magana DR tacigaba dayi tace " yana dakyau asan meye yake tada masa hankali lokaci daya yake burkicewa yasami attack" itakam HAJIYA SAKEENA shiru tayi tunda zaton son SA'ADARTY da sukeyi baizama lallaiba tunda har yau bai budi baki yace komiba, sun tambayeshi tun ranar farko yace shi bakomi kawai yana yawan faduwar gabane, haka suka fito sukuku gaba dayansu bamai magana saboda rashin sanin madafa

MUNEERA kuwa daga tace wancam sai tace wancan, yayinda SAADARTY take chart da su MERMA hankali kwance kuma duka akan mahaifintane sosai hankalinta ya dauke ga typing sai ji tayi wuf an fuzge wayar JAD ne, cikin hade rai tace " give my phone back" bai damuba sai ma danna home na wayar yayi dayasa tafita daga cikin whatsapp din ya zirata gaban Aljihun farar jallabiyar dake jikinshi,da ido MUNEERA tabishi cike da mamaki tace " ya za'ayi kake irin wannan wasa da housemaid din gidanku" takarasa tareda yamutse bakinta wani kallo JAD ya bita dashi yace " MUNEERA ki kiyayeni, banason shiga abunda baruwanki" zaro ido tayi cike da firgici ta dafa kirji " YA JAD ni kake gwalewa awajan wannan halittar da batada maraba da dab...  Kafin takarasa ya dauketa da mari

KUDURI KO MANUFAWhere stories live. Discover now