CHAPTER 69

1.2K 51 3
                                    

https://mobile.facebook.com/Eloquence-Writers-266267857577087/?ref=opera_speed_dial&_rd

✨✨✨✨✨✨✨
KUDURI KO MANUFA
✨✨✨✨✨✨✨

BY JANNAH JAY

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

© 2018

Follow me on wattpad@ jannahjay8

*DEDICATED TO MY VERY OWN SIS MERMA*

Nasan zakuga wannan so long chapter, kuma gashi nak'arasa book d'in agurguje,  hakan yafarune saboda banaso nadau lokaci banamaba don zan shiga busy nan gaba, kuma nayi alkawarin zangama kafin zabe, ina fata za'ayi hak'urin karantashi ahakan

183-END

Sai da tagama shirya komi sai MAMI tace mata " kije kiyi wanka ki shirya man" sunkuyar dakai tayi tace " MAMI idan naje can sai nayi" suna maganar ne kiran JADAR ya k'ara shigowa wayarta dama tun tana girki yake aikin kiranta taki dagawa, ganin haka yasa MAMI tace tashi kije su SALAMATU zasu taho daga baya saboda gyaran gidan

Kafin taje yagama shak'a shi zatayiwa taurin kai, kawai don ya kawo masu mafita, yaja tsaki tare da naushin pillow couch d'in dayake zaune, har saida kafad'arshi  mai ciwo ta amsa, ya d'anyi k'ara daidai lokacinne SA'ADATY ta shigo, da d'an hanzari ta k'arasa kusa dashi tace " what happen?  did you hurt your shoulder? " harara ya mata, tasan dabar garin sai ta basar tace " sannu everlasting" yace " banaso ai baki damuba tunda tun d'azun kinsan ina nan and you  leave me alone u dont even care whether i can need something" kama bakinta tayi irin na mamkin tace " yanzu baka ganin ka janyo mana jin kunya, agabansu su UMMI sai aga na zagaye mun taho gidanmu kawai don rashin kunya" wani kallo yamata yace " dad'ina da mata gulman tsiya kunaso kuna kaiwa kasuwa, yunwa nakeji kuma" dariya tayi tace " naga alama ai irin wannan d'aukar zafi haka, ai daga gani ansan akwai ta" d'an murmushi yayi, daga nan ta shirya masu table

Kwanansu uku da komawa gidansu su UMMI suka koma katsina, kafin tafiyarsu sai kayi mamakin yanda suka saba sosai, shikuwa AFFA wani k'ara son BABA yayi  kuma darajarshi ta k'aru a idonsa, yanzun haka sun gama magana akan za'asaki yaran BABA guda 10 na kurkuku,  duk wad'anda su SALIS sukasa aka d'aure sai da sukasa aka fito dasu sannan kuma suka nemi yafiyars, MUMMY MUNEERA an k'ara shiga taitayi har gidan tazo suka jima dasu UMMI, abangaran alak'arsu MUNEERA da DADDY sai daga baya da JADAR yamata nasiha sannan ta daina jin zafinshi, kuma alokacinne tagama saduda ta rasa JADAR na har abada, don haka ta yanke shawarar bawa ROCKCY dama, sai bayan abun ya faru da kwanaki sannan 'yan LEBNON sukaji labari sosai suka damu inda aka masu dabara aka juya labarin saboda gudun zubewar k'imar 'yan uwan COINS, domin shi baya k'aunar aga laifin zuriyarshi

MUJAHID takanas ya kira SA'ADATY yamata jaje, inda kuma yace sunyi kuskure abaya ita dashi yana fatan zata rik'i mijinta su zauna lafiya, anan ya had'ata da ZAINAB suka gaisa..

Haka ranaku suka cigaba da shud'ewa, har ZAMFARA BABA yaje tare da tulin alkhairai gasu UWANI. Yanzu har an koma school su MERMA sun koma anma banda SA'ADATY sai nextweek, basu gama angwancewa ba acewar JADAR

*******                *************

Kamar kullum tunda yasamu sauk'i sosai basu da aiki sai outing da soyayya, kamar yanzune suke amarci, kuma sunyi sa'a cikinta baida laulayi, sai d'an karan ci dayasata, har yazamanto abincin da JADAR ke iyaci tana iyaci, haka zai tasata agaba da tsokana, ita kuma tana kare kanta. Suna zaune suna cin abinci bayan ISHA'I yaga bayan sungama, ta mik'e ta nufi fridge ta d'auko snacks, zuba mata ido yayi yaga ina zata sai yaga ta nufi d'aki dashi, bin bayanta yayi yaga tazauna kan lazyman tana ci tana canza channel da remote, zuwa yayi ya k'wace plate d'in, dago ido tayi tace " give it to me" yace " i wont, kinasonYaran mu ya fito mai ci kenan" harararshi tayi ta mik'e tare da k'ara kai hannunta don ta karbi plate d'in, take ya janye ta fara binshi suna kewaya d'akin, ganin ta k'ureshi abangone yasashi fad'awa toilet, tana ganin haka tasa kukan shagwaba, sai da yafito yakama lallashinta, tak'i ji harda hawaye ido d'aya, yace " to yanzun mekike so ayi? "Tace " wani nakeso, dan bazanci wanda aka shiga toilet dashiba" yace " in nayi haka shikenan? "Ta gyad'a masa kai, ya fice koda yaje sai ya tarar babu wasu gaba d'aya sun k'are, dawowa yayi ya fad'a mata, dama tasan da hakan, tace ita kuwa sai ya fita ya sayo mata, gashi baison fita at times bayan ISHA'I, dole ya fita yaje yasayo mata tarkacen su, abun takaici meat pie d'aya taci sai cup cake guda d'aya, ta mik'e kan gado, shiyagama gyara wajan, koda yagama ta shige toilet, haka ya gyara gadon, tana dakinta acan ta shirya sai da ya biyo bayanta sannan ta dawo d'akinsa, anan salo ya canza suka shiga rud'a juna da salon soyayya tamkar ba itace d'azun take fushiba, ranar JADAR har ji yake anya akwai wanda yai dacen mace mai iya sarrafa namiji kamarshi, don koda suka dawo nutsuwarsu haka ya zauna jikin gado ya dorata kan cinyarshi yana samata albarka, itakuma hajiyar sai ta shiga nuna masa bakomai  bane hakan she can do even better for his happines, tace kuma ita duk abunda take shes just following his steps batama isa kamo shiba, sun dad'e ahakan baccine ya saceta akan cinyarshi, ya tsaya yana kallon cutie d'in tashi, daga baya shima bacci ya d'ebeshi har ya bingire don haka sai jinsu sukayi gaba d'aya sunyi luwww zasu fad'a gefen gado, tarota yayi inda shikuma goshinsa yad'an bugu da bedside drawer, atake SA'ADATY tasa nata hannun take shafa masa wajan lokaci daya tana mashi sannu, dawo dasu yayi kwance inda still yana rik'e da ita, sai tazama akan k'irjinshi, hura masa wajan tadingayi da bakinta, take wannan iskar dake fita bakinta ta shiga tadamasa duk wasu fitina na jijiyoyin jikinsa, daga nan dai suka k'ara yamutsa junansu.  ... Bayan sun dawo normal ne suka shiga wanka, sannan yajasu salloli.. Suna cikin karatun alqur'ani ladan yayi kiran sallar asuba, bayan sunyi suka koma bacci
*******             **************
"Everlasting yakamata fa nakoma school" shiru yayi kaman bazai tanka mataba, lek'a fuskarshi tayi tace " ko baka jini ba? " yace "naji mana alhuda huda basai kin nunamin kin gaji dani ba" cewa tayi "daga magana, Allah ya bada hak'uri" ta karasa tare da danne dariyar da ta taso mata, har ya ajiye comb dayake taje mata kai, sai kuma yaga bari ya rama kawai ya janyo comb d'in ya ja gashin nata da k'arfi take tayi 'yar k'ara, tana yarfa hannu take " cewa sorry sorry" d'aga hannun da tayine yasa t-shirt ta jikinta ta daga har ya hango cikinta yana d'an motsi, tuni kuma suka koma kan shafa cikin wai ya fara motsi, inda ana suka lalata hours suna surutai kan yaronsu

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 15, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KUDURI KO MANUFAWhere stories live. Discover now