https://mobile.facebook.com/Eloquence-Writers-266267857577087/?ref=opera_speed_dial&_rd
✨✨✨✨✨✨✨
KUDURI KO MANUFA
✨✨✨✨✨✨✨BY JANNAH JAY
*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*
© 2018
Follow me on wattpad @jannahjay8
*DEDICATED TO MY VERY OWN SIS MERMA*
181-182
Cikin karkarwa UMMI tace "Don Allah KAWU ka rufamin asiri, wannan tamkar jefa kai cikin masifane, in suka zama macizai kuma ai k'ara cutar da mutane zasuyi, kayi hak'uri abunda ya faru ya riga ya faru" KAWU yanajin haka yace " Eh to in macizaine zasu cutar da mutane, amman bari amaidasu k'adangaru (lizard) su k'are rayuwarsu a cikin bango" ba alamar wasa atare dashi, tuni suka zube kasa suna kama k'afar KHAMIS akan yasa baki, kuka SA'ADATY takama yi abun sam ba burgewa tsofinda suka ba shekara sittin baya ace sunyi goho suna rok'o ga hawaye a idonsu, hatta JADAR da da yakejin bawanda ya tsana aduniya bayansu sai yaji hawaye ya taru a idanunsa, ya kama rigar SA'ADATY da take tsaye shidake yana zaune yace " Don Allah kisa baki kar ya aikata hakan" kallonshi tayi takasa magana, ahankali ta taka kusa da KAWU daya sauya salon kiran aljanun dayake tafurta KAWU,amman ina bai jiba ya cigaba dayi can sai sukaji wata irin k'ara ta fara tunkaro d'akin,durkushewa HALIMA tayi akan gwuiwarta tana karkarwa hatta AFFA dai yaji tsoro ya tunkaroshi, fargabarsu kar suyi ido hud'u da aljanu, SALIS saboda tsabar tsoro ruwa ya fara biyo k'afafuwansu suna wani irin karkarwa suna gunjin kuka, zuwa SA'ADATY tayi ta kamo hannun KAWU UMMARU tace " KAWU don Allah amatsayina na wadda baka taba yiwa alfarma ina rok'onka daka sassautawa mutanen nan" sai kuka don Allah kayi hak'uri.. Ta fad'a tare da yin baya kaman zata fad'i gaba d'aya kowa hankalinsa ya tashi sukayi kanta harda JADAR dayake fama da ciwo akafad'arsa, ganin hakan ne yasa KAWU ya dakatar da abunda yake, take sukaji k'arar mai kama da guguwa ta tsaya daidai flower vase dake gefen TV, ajikin JADAR ta fad'i, agigice KAWU yazo yana fad'in " SA'ADATU tashi ki gani suna nan, basu komaba don Allah kiyi hakuri, nashiga uku ranar farko danaganta nayi sanadi mafi muni arayuwarta" SA'ADATY da dama dabara tayi take ta d'ago idonta ad'an juye kamar wanda ta farfad'o yanzu, ahankali JADAR yace " SA'ADATY kina jina? Tashi kigani suna nan" sukuwa su SALIS sun riga sun saduda zasu zama k'adangaru, don haka sun kife kansune akasa sunyi goho kaman zasuyi sujjada, suna jin komi da ake amma basa fahimta tsabar tashin hankali, jin shirune yasa suka dago suna uwar gumi kaman agidan biredi aka rufesu, sukaga gaba d'aya an zagaye SA'ADATY sannan suka dan gayyato sauran nutsuwar da ta rage masu, suka shiga bada hak'uri, SA'ADATY cikin muryar ciwo take bawa KAWU baki, yace shikenan ya hak'ura amma dai yakamata abarsu agidan horo ko na shekarane saboda laifin dasukayi
Yanzu ta mik'e tana zaune akan kujera, kowa ya samu waje ya zauna sukuma su SALIS suna tsugunne dai, anan suka nemi yafiyar kowa sannan kowa yace ya yafe masu, sai alokacin SALIS yakalli KAWU yace " malam yanzu aljanun suna d'akin nan don Allah kasa su koma" murmushi yayi na tsofin bokaye yace karka damu zasu zauna in naga anyi ba daidai ba zan sasuyi aiki kawai, yanda idon SALIS yayi sai da COINS ya dara
Daukar waya AFFA yayi yakira MUNEERA yace su taho da MUMMY tare da matar KAWU RABI'U, yana gama wayar yace FA'IZ yarakasu su shirya apart dinshi dama duk zasu iya saka kayanshi
Suna tafiya hira ta b'arke tsakanin AFFA da BABA, sai da COINS ya k'ara neman yafiyar shi shikuwa BABA yace bakomai k'addarace kuma dama Allah yayi hakan zai faru, basu da tsumi da dabara
IG ne ya kira AFFA yace bayan la'asar zanzo na tafi dasu, bai musa masaba yayi shiru, amman kasan zuciyarsa yasa zai shawo kansa ak'yale yan uwan nasa kodan yaransu ga tsufa
Sai wajan uku suka ci abinci, sannan kowa ya hallara da iyalansa, bayan kowa ya huta sai COINS ya sa duka 'yan uwansa da 'ya'ya su had'u atattauna
Yanzu suna zaune gaba d'aya 'yan uwansa suna gabanshi harda matan, akai ganawa ta 'yan uwa inda su SABI'U sukace suma sun saba d'iban dukiyarsa amma sun tuba ya yafe masu, duk aka yafi juna, shima yace duk abunda suka san yamasu na laifi su yafe mashi, shikuwa UNCLE SADI sai kuka yake abun ba dad'i 'yan uwanka uwa d'aya uba d'aya suyi haka har wani jin kunyar KHAMIS yake, sai duk yanuna masu su ware kowa yayi uzurinsa kamar ba abunda ya faru, gaba d'aya yaran ma da suke kukan sai suka share hawayensu
SA'ADATY lokacin ita kuma tana zaune apart d'in JADAR tare da iyayenta suna hirarsu, yanzu dariya suke KAWU UMMARU yana cewa "dama barazana nayi bayanda za'ayi na maidasu hakan, domin na riga na tuba" cikin dariya SA'ADATY tace " amman ai munji k'arar zuwan aljanu ya akai haka" yace " Eh dagaske aljani yazo amman salihine, bazaiyi komaiba barazana ce kawai" sosai sukayi labarin 'yan uwan, daga baya sai su UMMI da HAJJU suka koma part d'in MAMI dake anan aka saukesu a bedroom na SA'ADATY na da, ita kuma SA'ADATY ta gyara wajan mijin nata ta shirya wajan mijin nata tayi kwalliyarta tsaf
Bayan sun gama hirarsu na family kowa ya wuce gidansa, IG yazo an kalallameshi ya tafi, kowa zuciyarshi cike da jindadi da burin sake sabuwar rayuwa. Bayan tafiyarsune AFFA suka kebe da BABA kasancewar shi anan part d'in zai kwana, gashi bayan tonon asirinsu komi ya dawo kan AFFA kan rayuwarshi da BABA suka shiga hirarsu ta sahibai
FA'IZ ne yayi sallama ya rako JADAR part d'inshi, ya tayashi zama daidai saboda ciwon hannunshi, saboda tsabar k'aguwar da JADAR yayi bai jira FA'IZ yagama fita daga parlour ba yace " CUTIE PIE come to me" shareshi tayi ganin LAWISA ta shigo da tray mai d'auke da bowls sai bayan ta ajiyene ta k'arasa kusa dashi, ta zauna gefenshi tare da rungumar bangarenshi mara ciwo ta mashi peck agefen kumatunshi tace " i missed you " da muryarshi da tayi low full of lust yace " i missed you too" shafa sumar kanshi tayi tace " yanzu za'ayi wanka ko? " murmushi yayi yace " kinga ni banma san meyasa d'ayan hannun ked'an zafi ba may be dan d'an uwanshi baida lafiyane" kanne ido tayi irin naganoka tace " Eh kam da alama amma maybe sunaso ake moving d'insu ne zasu ware" wata shak'iyar dariya sukayi gaba d'aya, zuwa tayi ta had'a komi na wanka sannan suka nufi toilet d'in gaba d'aya anan yaga take tajenta bazata mashiba kenan, kawai dai ta tayashi rage kayan jikinsane yace " wai dagaske cutie ni zaki bari nayi wanka dakaina" jijjina masa kai tayi alamar eh yace " shikenan bari na kira MAMI ta min ko AFFANA" dariya tayi tace bari na d'auko maka phone d'inka ka k'irashi, ta juya ta barshi tsaye k'ofar toilet kwafa yayi
Bayan ya fito tazo zata tayashi shafa, ya turb'une fuska kallonshi tayi tace " ya za'ai kace dole sai hakan, nanfa gidan surikanmune fa ni gaskiya baran iyaba" dan ware fuska yayi yace " bakeba nikaina an takuranifa, gara ak'yaleni nakoma gidanmu haba, anan ba sakewane kuma gaskiya ni fa na jima bana tare da matana fa" tace " wannan k'orafin wakake yiwa? " baiyi magana ba sai yasa hannu yake shafa cikinta dake tana kusa dashi yace " yakamata shima ak'yaleshi yake samun kulawar iyayenshi" mitar da yayi tayi kenan ranar, ga hannu d'aya da ciwo dole duk jarabar da ya tanada ya hak'ura, gashi sam SA'ADATY da taga zai k'ok'arin wani abun zata nuna masa kar yaja ciwonshi yay famu, kawai dai tayi k'ok'arin dabarun kwantar da masa hankali batare da an sab'a ka'idar DR ba
Dama tun ranar da zasu taho ABUJA dan wajan KAWU UMMARU ya koma NIJAR, saboda haka suma washegari suna tashi sai BABA yace zasu koma katsina, AFFA ya rok'esu akan su k'ara koda kwana d'aya, kuma dama ai baisan d'akin d'iyarsa ba, saboda haka suka yarda zasu zauna, ranar da misalin k'arfe shabiyu na rana suka tafi gaba d'aya da SA'ADATY suga muhallinta, suna gidan su MERMA suka kirata akan zasuzo da iyayensu su gaisa da BABA, saboda haka tace su sameta agidanta
Bayan iyayen sunzo suka gaisa sun dad'e anan kafin su tafi, inda alokacin zaka d'auka su UMMI sun dad'e da sanin juna, sai da suka zo zasu koma gidan COINS bayan su MERMA sun tafi kiran JADAR ya shigo phone d'inta yace " karki manta da abunda na fad'a maki" tana magana bai jira me zatacr ba ya kashe, bata damuba ta shiga motar suka dawo gidan
Sai wajan la'asar aka nemi JADAR baya nan koda aka k'ira no dinshi sai yak'i dagawa, da MAMI taga haka kawai sai tayi murmushi tace " SA'ADATY jeki kitchen ki shiryawa JADAR abinci bayan magriba zaki koma gidanki, dama kowacce darajarta da aikij ladanta na gidan miji ninkine" kunyace ta dabaibayeta saboda ga UMMI awajan, ita kuwa sai tayi kaman bata jiba#TEAM KKM
#TEAM JADARFIRDAUSI JANNAH JAY

YOU ARE READING
KUDURI KO MANUFA
General FictionLabarine daya kunshi daukar fansa hade da son zuciya wanda dalilin hakan ya kawo canjin rayuwa ga sa'adarty da muhd jadar