CHAPTER 37

457 36 10
                                    

https://mobile.facebook.com/Eloquence-Writers-266267857577087/?ref=opera_speed_dial&_rd

✨✨✨✨✨✨✨
KUDURI KO MANUFA
✨✨✨✨✨✨✨

BY JANNAH JAY

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

©2018

Follow me on wattpad @jannahjay8

*DEDICATED TO MY VERY OWN SIS MERMA*

119-120

MUJAHEED kam abunda SA'ARDATY tace mashi amessage yayi masifan daure mashi kai, anan ya gano wautar da yayi na daina kiranta, dalilin hakane zaisa JAD yasamu kafa kanshi da har take tunanin cemashi ta mantashi ina!! Yasan har yau yana da matsayi azuciyarta, tunowa yayi yana da number KAUSAR tabbas zai mata wasu tambayoyi

JADAR da wuri ya tashi ya shirya tsaf cikin kaftan na coffe yard mai laushi wanda ya mashi kyau ba kadanba, daukar briefcase dinshi yayi ya nufi part din MAMI, so yake kafin ya tafi yaga SA'ADARTY saboda kar yaje ya kasa samun damar fitowa lokacin tafiyarta, luckily ya ji muryarta akitchen na central parlour din tana dariyarta mai sashi nishadi, wani irin dadi yaji saboda aduniya yanzu farin cikinta yakan share masa duk wata damuwa aransa, so yake mata bana wasaba wanda saboda tsabar abun da yakeji kanta at times har in ya tunata kwalla na taruwa a idonsa, ajiye case din yayi kan centre table ya nufi kitchen din, saboda rashin sakewar da yakeyi dasu lawisa yasa su yin dif tare da neman hanyar fita, ganin haka yasa SA'ADATY tace "kardai har kin gama dafa doyan? Gyada kai lawisa tayi alamar eh, bai tanka musuba sai ma wucewa yayi kusada coffee maker ya zari cup ya filling dinshi, sukam tuni suka fice, gaidashi tayi tacigaba da juya sauce din da takeyi, binta yake da ido cike da tsananin kauna, tasan kallonta yake tuni taji wani iri don bataso yaganta cikin rigar ba armless ce gata rubber kanta ba dankwali, batayi zaton zai shigoba haka duka lokacin bai wuce 7:40 ba ya saba zuwane 9 haka

Duk ta takura da yanayin kallon dayake mata saboda haka kashe cooker tayi batare da ta juye sauce din cikin container ba kawai ta fice, tana ficewa yaji bai iya cigaba da shan coffe din dama itane yakeson gani, kuma ta fita ajiye mug din yayi tare da daukan chicken escalope dake cike cikin warmer adan bude  ya fita, yafi 20 minutes azaune yana jiran ko zata fito dan yasan bata gama abunda zatayiba amma shiru kake ji ganin 8 tayine yasashi fita, ita kuwa SA'ADATY zuwa ta dingayi corridor da dakinta ke ciki take lekowa har sai da ya fita sannan taje ta karasa komi

Karfe goma daidai tagama duk abunda ya dace har karamin meeting suka gabatar itada MAMI, yana da tabbacin sammako zasuyi don haka tunda yaje office idonshi nakan agogo, jefi jefi ake kawo masa files yana dubawa yana signing a idan ya dace bai ankaraba yaga half past 10 cikin azama yama secretary dinshi magana  ya fito sai gida

SA'ADATY tuni ta fitarda komi waje suna cikin boot, zaune take tana cin plantain chips suna dan hira da MAMI, sallama yayi ya shiga, baiyi tunanin zai ganta ba ya zaci ta tafi, baisan sanda ajiyar zuciya ta kwacemashiba har sai da sukaji, murmushi MAMI tayi najin dadi tare da kallonshi tace "karaso ciki mana  JADAR, dama yanzu nagama tambaya ya akayi baka zauna yin break ba" cikin fara'a ya ce " MAMI na yau akwai aiki mai muhimmancine yasa nayi sammako." batayi maganaba saima jan kujera tayi tace "bari na dauko veil dina mu wuce karna makara" yazatamin haka, ni dana dawo dan muyi sallama na musamman da ita, azuciya JADAR yake fadar hakan,cewa yayi " to kanwata Allah ya taimaka banda kula samari dan  asamu abunda yakamata,kiban account no dinki" cikin sakin fuska tace " laaa banda shopping din da kamin, nikam nagode sosai" anan MAMI tasa baki tace "Haba SA'ADATY ai kya bawa yayan naki, kuma students ai kudi baya masu yawa" murmushi sukayi gaba daya, da hanzari SA'ADATY ta shiga daki ta saka mayafinta ta fito har bakin mota JADAR ya rakata, kafin ta shiga ciki yace mata " karki manta da maganarmu please"motar su na juyawa hanyar fita ta juyo ta bayan motar tana kallon yanda yabi motar da wani irin marayan kallo, cikin sanyin jiki ta daga mashi hannu bye..

Tana sauka a hostel  drivern ya wuce kano, tuni MERMA da TEEMA sundawo sai ihu da hayaniya kaman wasu yan secondary, sai da suka gama murnar dawowarsu sannan sukai shirin wanka, bayan sun fito gaba dayansu kowa yasa kayan shan iska suka fara hira, labari kala kala dai rabi na samarine sai suka fada kan JADAR, su kansu sun jinjina kayan da aka dinga ajiyewa kofar dakinsu tace sayayyan JADAR ne suka tafe tare da cewa "Allah yaja da ran MRS COINS" hade rai tayi tace " Kardai kunfison JADAR akan MY JAHEED" cikin dariyar shakiyanci TEEMAH tace "yarinya J na kaunarki, JADAR COINS ga JAHEED KAITA" turbune fuska tayi ta fuzge chocolate dake hannun TEEMAH tace bakishan wannan  nan suka fara guje guje cikin room din

Bayan sallar ISHA'I JADAR ya kagu 9 tayi saboda SA'ADATY tace zata bashi amsa ranar, ita kuwa SA'ADATY tsara mata kwalliya MERMA tayi tace saboda ya tabbatar har zuciyarta take nufi, video call zasuyi dashi and anan zata fada mashi, black gown ne jikinta aka mata arab rolling da maroon chiffon veil, lips dinta sun dau maroon luquid matte na classic,  giranta agyare sai kwalli da charcole black liner asaman idonta daya kara fidda farin idonta, bayan haka ba'asa komiba so kwalliyan bamai cikan fuskarnan bane, abun dariya sai kace afili zasuyi zancan

Agogonshi yana sawa 8:58 yagama zama ready sai kura  ido yayi kan screen na wayarshi, da 59 yashiga call logs ya dora hannunshi kan sunanta 9 diiiii kawai taji vibe na wayarta, hada ido su MERMA sukayi sukace fama!! ahankali cikin faduwar gaba SA'ADATY tadau wayar tayi picking tare da saita nutsuwarta, kasancewar data dauka can sama zai gano fuskarta sai yazamanto ya fara arba da idonta dayayi kyau, ahankali ya furta tabarakallahhu  ahsanul khalikin, yanzun tagama daidaita komi sukuwa su MERMA yan karawa wuta fetur tuni suka kara light na dakin nasu, aikuwa tas JADAR yake ganin SA'ADATY, dakyar ya tattaro dauriya yamata sallama itama ta amsa, muryarshi tayi sanyi saboda fargabar answer yace " ya hanya?  tace "Alhamdulillah normal" gaba dayansu shiru sukayi tacan gefe TEEMAH take daga mata ido akan karta bari fa suyi missing opputunity din, acan shima karfafa gwuiwarshi yake akan yatada maganar

" SA'ADATY about that issue please" yanzu ta tabbatar yana kallonta sosai tunda shi da ipad dinshi yakeyi,sunkuyar da kanta tayi tare da saita muryarta ta zama very calm and sexy tace " YA JAD you got all the trait that everyone would love to have you in his lifetime companionship, but im afraid" wani irin sanyi yakeji saidai yaji tsoro karshen furucinta, kara saita nutsuwarshi yace " afraid of what? Please tell me" wasa da yatsunta take tace " Kana iya ganin class dinmu daya i mean yanayin family na dakai? Kasan bazai taba yiwuwa kahada kanka daniba shiyasa nakeso mu hakura kawai, banaso nasaka cikin wani hali" dan takura fuska yayi yace " please karki damu, this is not a big deal all i want is your love and support .SA'ADATY i truly love you i dont want lose you please dont spoil my happines" dake batasa earpiece ba sunajin komi, tausayinshi sukaji gaba dayansu, shiru tayi shikuma yacigaba da kafa kansa inda ya nuna mata ba wata matsala da za'a samu amma ya maganarta da MUJAHEED anan tace zaiyi wuya abunsu ya dore, yaso ya tambayeta akan me? Amma sai yaji tsoron kar kwabarshi tayi ruwa tun yanzu, gara ya bari ahankali in ta waremashi sai yasamu yaji yanda za'ayi, ammafa in banda so ya rufe mashi ido yamanta tasha fadin tana son JAHEED, amma bari yagani

Sai wajen 11 sukayi sallama shima gani yayi tayi tafiya dole akwai gajiya atare da ita,ranshi fari kal bai gaji dajin maganartaba, kwantawa yayi flat kan rug yan zuba murmushi kamn sabon kamun hauka, daga baya sai ya tashi yayi alwala yayi nafilar godiya ga Allah SA'ADATY ta fara samuwa duk da kai tsaye batace tana sonshiba

itakuwa SA'ADATY sai da ta sanarwa MAMI ta amsa mashi aranar domin ita kanta HAJIYA SAKINA kin bacci tayi tana jiran sweet news daga SA'ADATY. Bayan SA'ADATY ta kwanta fadawa tayi tunanin yanayin rayuwarta anya bazatayiwa sakiyar da ba ruwaba, karta rasa JAHEED fa ko kuma JADAR yaki sakinta, tab amma da ta tarwatsa farin cikinta karshentama ashare babin rayuwar zuriyarsu. Hawayene ya fara ambaliya afuskarta tabbas an yiwa rayuwarta gwuibi


#TEAM KKM
#TEAM JAHEED

FIRDAUSI JANNAH JAY

KUDURI KO MANUFATahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon