CHAPTER 50

534 37 5
                                    

https://mobile.facebook.com/Eloquence-Writers-266267857577087/?ref=opera_speed_dial&_rd

✨✨✨✨✨✨✨
KUDURI KO MANUFA
✨✨✨✨✨✨✨

BY JANNAH JAY

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

© 2018

Follow me on wattpad@ jannahjay8

*DEDICATED TO MY VERY OWN SIS MERMA*

145-146

Suna isa gidan HAJJU SA'ADATY ta shiga ta sanar masu zasu shigo da baki, bayan nan ta fito suka shiga gaba daya, cikin mutuntawa suka gaisawa sannan ne HAJJU tace " Halima wannan sune mijin SA'ADATY da mahaifiyarsa" murmushi tayi ta sunkuyar dakai irin kunyar nan, shima JADAR din sai ya kus dashi duk ya dubulbule, ita kuwa MAMI sai taji hankalinta ya kwanta da ita, bai jimaba ya fita dakin dake tsakar gidan itama SA'ADATY  ta bishi, anan ne MAMI take taso taja HALIMA ajikinta domin su saba ita kuma tana dan kasa magana, sai sannan ta nuna mata dama koba amaganar auran JADAR tanason SA'ADATY taje UMRA bakaramin dadin zama taji da itaba, ta dora da yabon SA'ADATY har tana cewa gaskiya kun yiwa diyar ku tarbiyya sosai da azamanin nan kafin asameta za'a dade, ga amana na dade ina gwadata kan kudi amma daidai da naira biyar bata taba min runtoba" wannan yabo yayiwa su HAJJU dadi suka shiga godiya sukace suma basu taba ganin ahalin mai kudi masu karamci irin nasuba, kuma sune da godiya wanda yaso naka.

HAJIYA SAKINA bakaramin barin ciki tajiba tagama da wannan kenan

Bayan SA'ADATY sun zauna da JADAR, kura mata ido yayi yaki magana tace mashi "meye hakan kenan? tare da wani salon harara " murmushi yayi yace "mijinki zan zama soon anma kike min wannan tsiwar harda harara, baran kalli matata son raina ba" tace " Ai dai da saura sannan ni ba harara nayiba haka idona yake" kama baki yayi irin na mamaki yace "oh yaushe yakoma kenan ai bansaniba, amma bari na duba ko an samu changes ne" takowa yayi ya matso daf da ita, take taji gabanta ya fadi ta matsa can jikin bango miko hannu yayi kaman zai kama fuskarta ta bude baki kaman zata mashi ihu, kyalkyalewa yayi da dariya yace " matsoraciya kawai sai rashin kunya, look at you har wani shaking jikinki yakeyi,  i wont touch you im planning something" kallonshi tayi da idonta da suka dan tara kwalla wanda sun kara fitowa tace " planning.. Like what? " komawa yayi ya zauna kan plastic chair da yake yayi shiru bai bata amsaba, sunfi minti 5 bawanda yayi magana daga nan ya kalleta yace " Dama tuntuni MUJAHID bai zo gidaba kike cikamin baki akan soyayarku, ko daman kece ke sonshi?yanzun yana ina? " yanayin maganar dayake kasan akwai alamun kishi atare dashi sannan kuma ba alamar wasa afuskarshi, batayi maganaba, sai daya kara daukar wasu minutes kafin yace " ko dama yaudararshi kike? dagowa tayi ta kalleshi amamakance, yagane hakan shiyasa yaji wani kishinsa ya taso mar amma ya kanne yace "Ko kuma darajar MAMI naci kika yarda akazo nema min auranki? Idan hakane bakimin adalciba ba abunda nakeso aduniya illa na auri wadda takesona tsakani da Allah don koya na gano da wata MANUFA mace ta aureni tabbas zan dau mataki mara dadi" jikinta bakaramin sanyi yayiba, kodai JADAR yagano wani abu kantane? Tab aikuwa da tashiga uku,cigaba da magana yayi yace "idan kinsan har yanzu kina son JAHEED karki cutar da kanki ki cuceni, kina iya min text" karfim haline yazo mata tace "wanne irin magana kake haka? Da duk bakayi irin maganarba sai yanzun, ohhk kanaso ka nunamin kaima kana da akidar wasu rich kids kenan kuna kallon mu talakawa zalamammune ko me? Bari kaji nafi karfin na auri namiji dan kudi ko dan wani abu" SA'ADATY ta tashi nade tabar mar kunya da hauka ta dunga maganaganu hawaye yana saukowa a kumatunta, tuni JADAR yaji hankalinshi ya tashi, shin meye yasa yamata wadannan maganganu? Kishine ko me? Baya burin kuntatawa mace? Kama bata hakuri yayi ita kuwa ta basar dashi tana share hawayenda suka kasa sauka a idonta, cikin zuciyarta kuwa tana Addu'a Allah yasa bai gano wani abu ba

Haka suka nufi kano zuciyar kowa acikinsu ba walwala, daga kano suka bi flight sai Abuja..

kwanan su biyu suka wuce UMRA har lokacin SA'ADATY bata waremashiba wanda tayi hakane saboda tsaro karya kara gigin wannan tunanin, bataso yasama mata matsala.

ALSAFA suka sauka, sun gabatar da ibadar su, suka dawo masauki suka huta hatta ita dakinta daban, tana kwance kan gado tana chat dasu MERMA, suna tambayarta ya ALBAIK ya koma shaguna dayawa dai saboda su suna zuwa itace dai yaune farkon shigarta kasar, bata taba zuwa wani wajeba sai ranar

Yau kwanan su uku amakka sun shiga mota zuwa jiddah sun kwashi laces, abubuwa dai suna komawa suka wuce restaurant cin abinci anan ne JADAR yayi ta janta da magana har saida ta sauko suka koma normal, ranar kam MAMI ajiyeta akayi gefe inda yayita yawo da SA'ADATY suka cika akwatina uku kawai na oil perfumes, satinsu daya suka wuce MALAYSIA acewar MAMI sun iya takalmi mai tudu tunda SA'ADATY tafi sasu acan 3 days sukayi suka dawo DUBAI aka saya mata gowns abubuwa dai komi na lefe anan ta hadosu, mai karatu ya fasalta yanda lefen one and only son na third mai kudin NAIJA abun basai na tsaya fadarshiba, balle HAJIYA SAKINA so take SA'ADATY ta kwadaitu da dukiyarsu yanda zata tsaya da JADAR su mallaki manyan shares da companies nashi, shima JADAR balle ATM kawai yake tamkar ba'asan zafin kudiba, itakam SA'ADATY har abun yadaina bata sha'awa saima wani tsoro

Suna dawowa da kwana biyu midterm ya kare dama kadanne hakama ta kara, tayiyo KT cike da tsarabar yan uwanta da abokai ko kudin tsaraba bakadan aka bataba both MAMI da JADAR, aduk sanda MAMI take kwadaita mata kudi ita abu dayane ke zuwa kanta, batasan cewa ita don fito da mahaifinta take biyetaba amma kokusa dukiyarsu ta mata yawa duk da kowa nason ya huta

Tana zuwa gida su HAJJU suka tare ta da fara'a akwatina uku suka gani ta shigo dasu na tsarabane, akasa ta kawo driver ciki yaci abinci daga nan ya koma, sun bude kaya dukansu sai da ta sayo masu set na gwal abundai ba'a fada hatta KAUSAR sai da ta sayomata banda kaya wadanda ta siyo masu wasu iri daya,washegari ta hada kayanta takai school ta wuce cikin gari tayi shopping na foodstuff,na gidansu, aranar su MERMA suka dawo,  amakare ta koma gida

Washegari ta tatara tayi hostel saboda fuskantar karatun exams, dan 2 weeks din da basu gantaba sunga tayi wani irin fresh, da ta raba masu tsarabansu murna sosai sukayi harda nasu mamansu, adaren ne kuma take fada masu ansa date da zarar sun koma hutu da 2 weeks za'ayi biki tunda tace batason bid'a, zaro ido TEEMAH tayi tace "gaskiya ki barmu mu wala musan munje biki gidan ALHAJI KHAMIS SULALLA (COINS )" suka saka dariya, SA'ADATY tace "karki manta auran wucin gadine, banaso duniya tasan anyi shine kawai" shiru sukayi sukace "hakan kuma fa gaskiyane, yamaganar MUJAHID? " dif SA'ADATY tayi tace " narasa taya zan fara sanar mashi, banaso hakan ya datse alakarmu gaba daya" kamo hannunta MERMA tayi tace " SA'ADATY yakamata ki cire shakkar komi, karki manta shimafa yamaki laifi abunda zakiyi kawai shine ki gaya masa  zaki aure dan gidan kaman yanda MAMI ta umarceki, amma zaki fito tunda kinsan baya sonki bazai iya zama da diyar talaka irin kiba, kiyi nazari idan kika bari ya tsinci maganar agari zakisha mamaki kishinsa zaifi yawa" itama TEEMAH hakan ta nunawa SA'ADATY aranar tace masu dama zamanta ayawon da sukayi basu fiya wayaba har yana cemata shi yana zarginta da wani abu, jan tsaki TEEMAH tayi tace " maza nada karfin hali shi baya ganin yanzun Auransa za'ayi da wata nextweek, kuma kedin kina damunshi kantane" da mitar JAHEED dai ranar suka  rufe hirarsu kafin dare yayi kowacce ta dukufa wajan abunda aka kawosu, don duk iya shegensu da son fita yawo basu wasa da karatu

Da safe wajan misalin karfe 11 MUJAHID yakirata, kafin tadau wayar har wani karkarwa hannunta keyi, ji take duk wasu kalamai na bakinta na kafewa, kasancewar hakan yasa muryarta tayi kasa, shikuma MUJAHID anasa bangaren bakaramin shiga muryar ta mashiba tuni yaji sonta ya kara nunkuwa azuciyarsa, taya zai daina son wannan diyar? Ya tambayi kansa, bayan sun gaisa tace mashi zan sanar dakai wani abu amma inaso kamashi duba ta fuskar fahimta, hakanan yaji wani irin faduwar gaba tace " Ahalin da ake ciki yanzun JADAR dan gidan da nake aiki iyayensa sun gabatar da kansu wajan KAWUNA kuma komai ya daidaita" cikin wani irin zabura da baisan yayiba yace "what.... Meaning an bashi ke kome?  SA'ADATY me kikeso kicemin har wani haki haki yake yi, kishi yataso ya danne mar kirji..

#TEAM JAHEED
#TEAM KKM

FIRDAUSI.... JANNAH JAY

KUDURI KO MANUFAWhere stories live. Discover now