https://mobile.facebook.com/Eloquence-Writers-266267857577087/?ref=opera_speed_dial&_rd
✨✨✨✨✨✨✨
KUDURI KO MANUFA
✨✨✨✨✨✨✨BY JANNAH JAY
*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*
© 2018
Follow me on wattpad @jannahjay8
*DEDICATED TO MY VERY OWN SIS MERMA*
179-180
Sai wajen 8 SA'ADATY ta dawo hankalinta, koda ta bud'e idonta ganin JADAR tayi ya rik'e mata hannu, sakarmasa lallausan murmushi tayi, shima ya maida mata martani, bai damu da rashin kwarin jikin dayake jiba ya saki hannun nata sannan ya mik'e tsaye ya karaso jikin gadonta, kafin ya zauna ta mik'e zaune tace " baka ganin halin da kake ciki please ka koma ka zauna" bai damuba saima murmushi daya cigaba dayi ya zauna had'e da kamo fuskarta da hannu daya ya had'eta da tashi yace " bazan iya jiraba, nadade inason naji d'umin jikinki balle kuma yanzu yazama na abu biyu" murmushi tayi kafin tayi karfin halin janye fuskar tashi tace " godiya ta tabbata ga Allah da ya dawomin da mijina" daidai lokacin MAMI ta shigo da abinci domin kuwa likitan yace yunwace da damuwa suka saka SA'ADATY din suma, sai da aka kawo masu container da brush sukayi sannan suka ci atare ita da JADAR
AFFA kuwa sai fama yake da amsa wayoyin mutane yanzu hankali ya kwanta, yana iya dagawa, so yake ya kira IG yaji halinda su SALIS suke ciki amman dayayi kokarin kiran sai kaga wani kiran ya shigo, tuni yasa su SABI'U suyi magana da DR suna son komawa ABUJA yanzun, akarasa treatment can
Haka suka had'a kayansu, suka nufi can, yanzu SA'ADATY ta dawo normal hartayi kwalliyarta ga miji ya dawo, sai wani takurata yake akan tazauna inda yake, yanzuma ta shigo masa da nono ne daki zata fice saboda yan jaje da suke zuwa, ya tubure shi bazai shaba har sai ta zauna tabashi da kanta, dole ta zauna take bashi yana b'aci da shagwaba
Dake agidan COINS gaba d'aya suka sauka duka sun samu sun huta, BABA yana tare da AFFA afalo sunci abinci, anan hira ta barke masu sai alokacin AFFA yake tunano rayuwarsu ahankali ahankali sai dai baigama tuna komaiba, sai AFFA yace ya kamata yasa iyalansa suzo ko hankalinsu zai kwanta tunda yace ya kasa samunsu awaya, kiran FA'IZ yayi yace yasa ashirya komi ad'auko iyayen SA'ADATY
ANTY SUWAIBA tazo tare da kannan FA'IZ guda biyu, shiga daki tayi ita da ANTY RABI suke hawayen abun kunya dasu SALIS suka jamusu, saboda cikinsu d'aya koda ANTY SUWAIBA sukayi ido hud'u da AFFA sai taji kunyarsa, yagane hakan yace mata " wannan abun bai kai hakaba, gaba dayanmu yan uwane fata zamuyi Allah ya rabasu su da sharrin shaid'an, wannan duk yana cikin k'addarane" tadanji dad'i sannan yakoma part din MAMI
MUNEERA ma tazo inda tadinga kuka, kowa sai da yaji tausayinta, sai alokacinne KHAMIS yasan an jigata yan uwannasa yayi ta kiran IG amman yak'i picking calls din, raka MUNEERA akayi wajan JADAR ta dubashi take hawaye ya fara zubomata, tabbas babanta yayi abun kunya, kenan wannan shine tanadin dayake fad'in yayi, wato share babin rayuwar gidan UNCLE KHAMIS yayi niya kenan, gaba d'aya sai taji ta muzanta, takasa zama agidan 4 na la'asar ta bar gidan, mummy kam takasa zuwa saboda tsoron kar ayi awungaba da ita zuwa cell
Iyalan RABI'U da basu da yawa dama yaranshi biyu duka basa kasar, matar sa da batasan dabar garinba kuka tadingayi, ta taho gidan COINS tunda taji labarin sun dawo cikin ABUJA, ta tsugunna gaba COINS tana bashi hakuri, ai lallai RABI'U ba halinsa bane zugar SALIS ce, don ita baitaba wata mummunar magana agabanta ga KHAMIS d'inba, alokacin ne ya rarrasheta yace insha Allah ba abunda zai faru, yace shi baisan ma an dauki mataki kansuba, jiya kuma da suke SULEJA hankalinsu bai kanma TV balle waya bare suga ana nuna sun
Mutane sai tururuwn zuwa gidan suke, waima ahaka ba KATSINA bace, dakyar ya samu IG ya daga wayar yace masa don Allah asarara masu ya kyalesu, sai IG yace " koba kai sukayiwa laifiba dama sun karya dokar k'asa, sunyi garkuwa da d'an adam, sannan kuma sunyi amfani da makami wajan kokarin kisa" sai da KHAMIS yayi ta bashi baki, sannan yace "meyasa kuka daga maganar nan har zuwa waje, abunda family issue ne" yace "Ai kasan aduniya ALHAJI TANKO baya k'aunar yaga abunda zai dameka, kuma ni na k'ara zugashi, saboda masu irin halin su shiga taitayinsu" cikin rashin jin dad'i COINS yace " Ai duk da haka tamkar mutum ya tsinka zuriyarshine, ni kaina abun zai zamo tamkar abun kunya garenine, sam banji dad'in hakan ba"

YOU ARE READING
KUDURI KO MANUFA
General FictionLabarine daya kunshi daukar fansa hade da son zuciya wanda dalilin hakan ya kawo canjin rayuwa ga sa'adarty da muhd jadar