CHAPTER 40

501 37 7
                                    

https://mobile.facebook.com/Eloquence-Writers-266267857577087/?ref=opera_speed_dial&_rd

✨✨✨✨✨✨✨
KUDURI KO MANUFA
✨✨✨✨✨✨✨

BY JANNAH JAY

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

©2018

Follow me on wattpad@  jannahjay8

*DEDICATED TO MY VERY OWN SIS MERMA*

125-126

Da safe SA'ADATY tashi tayi ta hada masu break mai rai da lafiya, bata lecture ranar monday.Bayan tashirya ta shiga gidansu KAUSAR sukasha hira, bayan ta bata cosmetics ta bawa UMMAN su atamfa harta ummi kanwarta saida ta bata undiess.

Da yamma ta koma hostel kasancewar TUESDAY morning lecture garesu

ZAINAB ta shigo katsina inda anan ne mahaifiyar MUJAHID tadinga sakata acikin kowanne uzuri nasa, har hakan ya janyo baya iya waya da SA'ADATY akai-akai, hakan shiyasa ta kara sakankancewa da JADAR.Itakuwa HAJIYA SAKINA abun sai yasata take kara warewa da SA'ADATY saboda bataso ko sau data tasamu matsala acikin plan dinta

ALHAJI SALIS DA RABI'U ne zaune cikin jirgi zasu LAGOS, yanzunma wani suka lakawa sharrin alguus din da suka zuba cikin kayan ALHAJI KHAMIS,  da sukaga za'a ganosu sai sukayi munumunu yazamanto shi za'akama, haka tsarin rayuwarsu yake duk wanda sukaga zai iya tona asirinsu awajan COINS  ko yafara gano sudin macutane to tabbas shi zai kwana aciki, hira suke cikin kwanciyar hankali suna tsara cewa jira suke nanda wasu watanni sugama da ALHAJI KHAMIS, da zarar ya gama hada jiragensa lokacin suke ganin yagama tara masu dukiyar da zata ishesu wadaka gaba dayansu, sai su shareshi dagashi har iyalinsa, suka kwashe da wata dariya

Bayan sun je, sai da suka saka aka zagaya dasu wurin wadanda sukayi sanadin rufewa, can sai RABI'U yace ka tuna da MUHAMMADU DAN FILLO suka barke da dariya sai SALIS yace " kwarai kuwa, wanda yaso ya kawo cikas ajindadin muba, kai bantaba ganin mutum mai kafiya irinsaba, muje maganshi" dariya RABI'U yayi yace " kwarai kuwa aikaga yanzu yaga yanda taurin kai da zafin akida yakaishi" har daki aka kaisu inda anan naga wani kyakkyawan dattijo wanda zai iya kaiwa shekara 50 dan wahala kadan shiyasa yajeme amma duk da haka bazai hana ka gano kyau da haiba atare dashiba, ga wata kama dayake da HAJJU  hade da SA'ADATY, kura masu ido yayi yana jinjina me sukazo yi kuma saboda jarumta irintasa murmushi yayi tare da mika masu hannu "ALHAJI SALIS kune atafe sannunku da zuwa" kallon juna sukayi kafin ALHAJI SALIS ya mika masa hannu yace " kana nan yanda kake, ya kakejin rayuwar nan din? "Ya karasa maganar da wani kallo mai cike da izgili, ware hannunshi yayi yace "As you can see its full of enjoyment" dama ko agefenshi sunga wani saurayi ne yana yanke mashi kumba(farce)  shiru sukayi kafin SALIS ya barke da dariya yace " kwarai kam zakayi enjoying dinshi tunda dama koda ka koma daidai kake da gauro cikakken mara mata" wannan karon da mamaki ya kallesu mai suke nufi? Meye yasami HALIMARSHI HALIMARSHI? Amma afili sai yace " mutum irina bai fiya rasa matarda zai auraba, kudai ku saurari fitowa ta kwana kusa, ina tausayin fura ba nono" tunzura SALIS yayi ya daga hannu kaman zai mari MUHD SAFANA caraf saurayin nan ya tarbe hannun, inda cikin tsoro SALIS ya ke karewa saurayin kallo irin dirka dirkan yarannan ne masu zubin yanfashi, kallo daya yamasa ya tabbatar da zai gwada marinsa la shakka sai hakoransa sun zube, kalar thugs gareshi, aikuwa hannu yasa zai dorawa SALIS mari MUHD SAFANA yace "KAMALA barshi ba yanzune lokacin hukuntasuba" cikin yanayin maganar wanda giya ta budewa murya yace "BABA dama ka bari na dan sassama masa kashi na lura akwai gyara afuskarsa" cikin borin kunya suka fita suna cewa "zakuga abinda zai biyo baya"

Bayan fitarsu KAMALA ya dubeshi yace "BABA wadannan sune ko? Daga dukkan alamu rashin kirkinsu ya bayyana" jinjina masa kai yayi yace " Kwarai kuwa sune SALIS da RABI'U, biyu daga cikin masuyiwa KHAMIS zagon kasa, na tabbata yanzuma wani sukayiwa silar zuwa gidannan, amma bakomai zan bincika waye suka kawo zamu iya wani abun akai"

    Tun bayan kawo MUHD SAFANA gidan kurku bai dade ba mutane suka fahimci kyawawan halayensa, yanzu haka akwai matasan da yake ilmantarwa aciki, kowa na ganin girmansa acikinsu wasu har yasa sun tuba daga kura kuren da suka aikata abaya, baya cikin matsala tun bayan tafarko da yasha wadda su SALIS sukasa akayi tamashi, shi KUMA KAMALA yana daya daga cikin wadanda suke masa kallon mahaifi kuma yafi waremashi, ayanzu haka yasan silar kawoshi kurkuku.... Wannan kenan

Ahanyarsu komawa gida zagin MUHD sukayi tayi, shikuma acan dakyar bacci da daddare yayi nasarar saceshi bayan nafiloli daya saba gabatarwa domin iyalinshi, akullum ya tuno su sai ya kwana idonshi naja kuka ne ke gagararsa

Abangaren MUHD JADAR kuwa sati biyu da SA'ADATY bata nan ji yake sam ABUJA bata mashi dadi, bai kara tabbatarwa sonta ya masifan kamashiba sai yanzu, har kwalla ke taruwar masa aido aduk sonda sonta ke ratsa masa zuciya, ganin tayi 2 weeks a school yasa yaje har wajan MAMI yace ta bashi account number na SA'ADATY, domin wancan karon daya tambayeta bata bashiba, tuni ranar da SA'ADATY tabar gidan ya fadawa MAMI son dayake mata shiyasa ma yanzun kai tsaye yaje wajanta, cikin murmushi MAMI ta rubuta mashi shi kuma take ya mata transfer through mobile banking

SA'ADATY na zaune tana warema MERMA kitso (tsifa) , taji alamar message ya shigo phone dinta, sharewa tayi tace "MTN ne" sai da tagama mata sannan tamike suka  shirya gaba dayansu, kasancewar dukansune zasu wash and set a saloon,kira ya shigo wayarta MU'AZZAM ne, sai da tagama waya dashi taga CREDIT ALERT tayi mamaki waye hakan, tasan dai zuwa yanzun MAMI barata turo mata kudiba, kuma JAHEED baida account numberta, shaf ta manta sunyi maganar account number da JADAR, cikin zaro ido tace "nashiga uku! " kamota MERMA tayi  tace "meye ya faru? "Mika mata wayar tayi tace kalli ki gani " 200k what asuprise JAD COINS" Cewar MERMA, TEEMAH dake gefe tace "What! Yes this is dating with rich kid, gunsu wagga kudi kaman 2000 nepa just to buy sweets" MARISCO dake gefe ta kwashe da dariya tace "TEEMAH and money" zama SA'ADATY kawai tayi kan bakin bed dinta tare da dafe goshi, can kuma tayi dialling no MAMI ta fada mata nan MAMI tace "kinganiba sam baida rowa sannan yagaji COINS basu iya son abuba, haka zaita mallaka maki kadara da zarar kinzama tasa, kiyi enjoying kudinki kawai" warewa tayi tace ladies kuzo kawai mu wuce....

#TEAM SA'ADATY
#TEAM KKM
#MUCH LOVE..THANKS VOTERS

BY JANNAH JAY

KUDURI KO MANUFAWhere stories live. Discover now