https://mobile.facebook.com/Eloquence-Writers-266267857577087/?ref=opera_speed_dial&_rd
✨✨✨✨✨✨✨
KUDURI KO MANUFA
✨✨✨✨✨✨✨BY JANNAH JAY
*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*
© 2018
Follow me on wattpad @jannahjay8
*DEDICATED TO MY VERY OWN SIS MERMA*
123-124
Cikin yanayi na tsantsar kewa yake kallonta, itama anata bangaren hakane tana tuna moments dinsu na baya, bata taba sabo da saurayiba irin yanda tayi da MUJAHID, suna zaune cikin hut suna hira sosai yakejin nishadi, SA'ADATY tadabance acikin mata awajanshi baya ita,cikin yanayin sauya fara'arsa zuwa daurewa kadan yace "SA'ADATY na dade ina sanarmiki akan ki kasance tare dani duk wahala kuma duk runtsi hakane? "Jinjina kai tayi yacigaba "Ganin alakarki da JADAR itace tasa gaba daya nakeji kamar zaki watsa min kasa a ido, SA'ADATY ina matukar sonki shiyasa bana kishinki da wasa, ban kyaleki dan kawai nadaina sonki bane bani da choice ne" shiru tayi shikuwa tuni idonsa yayi ja kishine dashi nadaban, sosai taji faduwar gaba bataso yakejin haka akanta ya za'ayi akan kawai zargi yaji zai iya rabuwa da ita bayan yasan yakoyamata sabo dashi. Sun kai 3 minutes kowa na sake-sake aransa kafin tace " baikamata kaji zaka yanke hulda daniba, koyaushe kana yawaita furta karna bada hanyar da zamu rabu amma sai ya kasance kaine kake fara kawowa, baka da tabbas akan ina soyayya da JADAR, yakamata ka sani ko bakai bazan iya auran JADAR ba kuma koda na aureshi bazan iya rayuwa dashiba" maganganunta na farko sun yayemashi wani takaici amma na karshe ya tsaya masa "koda kin aureshi! Me kike nufi da hakan? " murmushi tayi tace " ina nufin koda kaddara ta hadani dashi kasa aranka saina dawo gareka" bahaka yaso jiba, amma koma mene ne yanaji ajikinsa zai iya yiwuwa ahana shi JADAR din auran SA'ADATY duba da yanayin status dinsu, basarwa da abun yayi suka cigaba da hirarsu cikin nutsuwa bai bar wajanba kiran ZAINAB ya shigo wayarshi, kin dagawa yayi SA'ADATY tace "wayanka fa" kalla yayi tare da dan yatsina fuska " no wani ke takuramin kan wani plot da yakeso nasayar mashi, kuma nace bazani saida ba, amma yaki ya daina" ahankali ta furta "Allah ya kyauta"
Bayan sallar magriba SA'ADATY na zaune kan plastic chair tana tunani, yanayin abunda ke wakana tsakaninta da MUJAHID yana daure mata kai, taji labarin ana son hadashi da wata inda aka sanar mata mahaifiyarshi keso amma shi bai yardaba, kirannan da tagani ta zargi wani abu, kauri tafaraji na stew din da take "kashh" ta furta tare da sauke pot din
MARISCO ta dawo nan fa dakinsu ya birkice da hayaniya saida suka nutsu sannan kuma sukaci abinci. Karfe 9 na dare JADAR ya kirata wannan karon bata koreshiba saima waremashi da tayi sukasha hirarsu har wasan tsokana da suke gida sukayi, sosai tadinga jin nutsuwa da farinciki alokacin da suke wayar 10:pm nayi ya mata sallama saboda lectures, adaidai lokacinne kuma kuma JAHEED suke tsaka da waya da ZAINAB anan take sanar mashi wednesday zata dawo daga kaduna agidansu zata sauka
SA'ADATY sai da tagama shirin bacci cike da mamaki MUJAHID bai kirataba lokacin sha daya saura, tana kwance sai kiransa yashigo wayarta sakin ajiyar zuciya tayi, ta dauka sai past 12 tayi bacci
Amakare ta tashi still da message din JADAR tayi arba har yana mata addu'ar sa'a akaratunta, batason meyasa ba kawai duk wani abu dayayi sai takejinta acikin annashuwa da nishadi,adan tsawon week din da suka shirya da zaman jinyar da tayi tana jin tayi sabo dashi, replying message din tayi da "morning hw u?" ta wuce toilet yin wanka, tuni MERMA da MARISCO sun fito daga wanka suna shafa, ita kuma TEEMAH na cikin toilet, itace yau kenan zata ja masu makara, jan tsaki tayi kallonta MERMA tayi tace "Ai duk laifin JAHEED ne,mijinki JADAR ya barki ki kwanta da wuri amma kika biyeshi" SA'ADATY tace " Shit! Mijina kikace fa, huh kwanan nan na lura sam baki kaunata da JAHEED" hmnn MERMA tayi ta bude kayanta ta fito da kayanda zatasa, alokacinne TEEMAH ta fito sannan SA'ADATY ta shiga
Tana tsakiyar shiryawa MERMA tace mukam bari muyi gaba JAHEED yazo ya taimakeki wajan DR UMAR, gaba daya suka kwashe da dariya MARISCO ce kawai tace ni bari na tsayata kar ya tsaidata ita kadai, marairaicewa SA'ADATY tayi tace "haba don Allah duk akan my hubby kuke min haka" ohh har ma hubby ko? Cewar MERMA zakiga hubby don Allah TEEMAH muje, aikuwa suka juya suka tafi tana tsaka dasa rigarta, cikin sauri ta shafa lip gloss ta zari handbag dinta suka wuce. Akofar lecture hall din DR UMAR ya umarcesu da su tsaya saida aka gama attendence tsaf yace su shiga, shidama haka tsarinshi yake daya shiga za'a fara attendence duk wanda ya makara bazai samuba don zai tsaidakai har sai naciki sungama sannan zaku shiga
Yana gama masu lecture wasu suka fito daga hall din yazama saura kadan, yawanci hira suke na yaushe gamo kasancewar shine lecture na farko bayan dawowarsu, zolayarsu SA'ADATY MERMA tayi anan SA'ADATY take ta ciccika tana batsewa wai tayi missing 1 mark, anan MERMA tace "Ai cin amanar mijinki JADAR da kikayine yasa hakan, meye namu ciki" haka yinin ranar ya kasance motsi kadan su tsokaneta wai nan gaba ta kara biyeshi, shi da har masters dinshi ya hada yanzu yana yin PHD ne
MUHD JADAR kam ya dage dason kafa kanshi wajan SA'ADATY message na soyayya akai akai bana safe bana dare ga tsantsar nuna kulawa, hakan yasa ta kara sakewa dashi ita kanta tagano bakaramin so yake mata ba, gefe daya kuma itada MUJAHID kowa yana kokarin ganin ya dasawa dan uwansa sonshi saboda dukansu sunsan akwai matsala akasa, wadda kowanne acikinsu bai sanarwa da dan uwansaba
Satinta daya da dawowa kenan yau yakama sunday tagama,fitar da wasu kaya tayi na abinci da wasu turare harda turmin atampa ta kira wata maaiki ta tayata fita dasu gate, bayan taje ta shiga napep sai kofar gidan HAJJU, dama su MERMA sun shiga cikin gari green house dinko hijabs don ALQALAM kullum sune abun sawar students ba'a saka mayafi, tana tsayawa kofar gidan taga mahaifin KAUSAR yayi parking yar motarshi ta karasa wajansa suka gaisa,ya tambayeta saukar yaushe? Tace satinta daya kenan, bayan tashiga gidan yaran unguwar suka tayata da shigo da kaya,binsu da ido HAJJU ta dingayi, bayan sun gama SA'ADATY ta zaro dari biyu ta basu, su biyune daman, kallonta HAJJU yayi tace "ina kika samo wadannan kayan" tace " yaron gidanne ya sayamin ahakama nadau nawa, su taliyane da macroni harda ledar basmati rice medium da su madara ta ruwa gasunan dai tarkace, da carton din maltina guda biyu cikin lemunan daya sayamin baki iyashan ko daya" kama baki HAJJU tayi, SA'ADATY dinga irga mata abubuwan ita kuwa HAJJU tana tafa hannu tace "kice basusan ciwon kudiba, wadannan kaya ace baifi rabi kika dauko ba shikuwa dubu nawa yakashe? Sai kace garar kai amarya" murmushi SA'ADARTY tayi tace " Ai su suna da alkairine ba rowa, ga atampopi zan baki kudin dinki ga kuma 10 ki rike ahannunki, wannan akudin watana ne da ake biyana na jiyemiki, don har yanzu da banfiya aiki gidanba ana sakamin shi duk wata" cikin al'ajabi HAJJU tace " Ubangiji ya sakawa mutanen nan da Alkhairi, yaraba su da sharrin mutum" itadai SA'ADATY kasa kasa take cewa "Ameen "sun danyi shiru na lokaci sannan HAJJU tace "SA'ADATU tun yaushe kika fuskanci asalin labarin mahaifinki? " kwalla ta taru a idon HAJJU, cikin rawar murya nashirin kuka SA'ADATY tace "Tun banfi wata da fara aiki agidan COINS ba,naji ranar kawu yazo, banji dadi ba da kuka boyemin, maiyasa bazaku sanarminba yanda ko addu'ar sa'ar fitowa ai nake mashi ko, kuma idan naji wanda yasan matsala irin tasa zai iya taimaka mana? Gaba daya sunyi laushi "SA'ADATU banajin akwai wanda zai kwaceshi, sauki daya munganshi wannan wata yasamu yar nutsuwa sannan baya shan wahala sosai, kullum in mukaje bashi da aiki sai tambayar mahaifiyarki dake, na sanar masa kin fara karatu bakiga farin cikin dayakeyiba" kuka SA'ADATY tasa itama HAJJU kuka take bilhakki, abunda bataso kenan, har yau bansanarwa da mahaifinki HALIMA batanan ba, kusan wannan karom ne suka sami zaman jajantawa kansu matsalar komi daya shafesu, shiyasa wancan zuwan da SA'ADATY tayi HAJJU takasa tuntubarta da zancan tunda tazo da kawayenta, raya daren sukayi da nafilfili, itakam HAJJU kafafuwanta har ciwo suka fara SA'ADATY tashafa mata ANACONDA tace ta huta....
#TEAM KKM
JANNAH JAY.. Much love to wattpadians❤

YOU ARE READING
KUDURI KO MANUFA
General FictionLabarine daya kunshi daukar fansa hade da son zuciya wanda dalilin hakan ya kawo canjin rayuwa ga sa'adarty da muhd jadar