chapter 9

685 45 3
                                    

    Da misalin karfe hudu wayarta ta farqar da ita daga barcin da ya dauketa, kanta ta dafa saboda ciwon da yake mata duk ya mata nauyi.

Num insp ta gani dauka tayi ta kara a kunnen ta

Hello!

Hello! Madam kina ina ne?

Erm ina gida amma yanzu zaj fito pls ka dan bani time kadan.

Ok ina jiran ki a hotel din

Ok nagode.

     Cikin doguwar riga baka ta fito ta sha nadin veil din ta karamar jaka ta dauka ta dau key ta fita

Mama na fita se anjima ki mun addu'ar samun nasara.

Allah ya tsaya miki mih se kin dawo.

A dawo lafiya.

   Cikin ksnkanin lokaci ta karasa hotel din.

A harabar hotel ta same sa ya mata iso kamin su je dakin ta kunna wayarta a wayance tasa vedio recording ta na yi

Dakin suka shiga wanda aks kulle shi saboda investigation,  dakin tsaf tsaf sedai gun da aka ga gawar maryam cikin jini kuma jinin na nan har yanzu ba a goge ba.

Dakin ta dinga bi da kallo a tsanake kamim ta bude kofan toilet ta shiga ta yi kusan minti uku a ciki sannsn ta fito dama hannun ta da akwai safar hannu, drower ta bude nsn ma normal ba komai ta tsuguna ta leqa karkashin gado ta haska wata er fitila yayin da ta hango wani zobe a fakaice cikin wayo da dabara tayi wuf ta dauke shi dan kar insp ya gani kuma cikin ikon Allah hankalinsa baya gun ta hakan yasa ta cilla shi a jaka, mikewa tayi tana murmusawa ta ce insp.

Uhm madam,

Ina wukar da aka kasheta?

Tana can off kinsan murder weapon ne so da extra care zamu adsna shi.

A ina kuka ga abdool?

Ya ce dan daidaita tsayuwanki kidauke kece maryam ni kuma ni ne abdool

Ok ta fada tana gyada kanta

Ts tsaya daidai inda ya mata nuni, ya tsaya daga bangaren daman ta ya yi kamsr ze kwada mata abu a gefan wuya.

Ta ce wow wato ta bangaren dama aka soketa da wukar?

Eh haka ne

Ohk ta fada tana gyada kanta.

Agogon hannun ta, ta kalla ta ce nagode insp muje.

A wajaj mota suks rabu ta ce mu hadu a court.

Ya murmsa mata shima yace all the best

A nan suka rabu da junan su.

A daidai danger ta tsaya wayarta ta dau ruri num meenal ta gani ta dauka ta sa a handsfree.

Hello meenal
Hello mih
Uhm ina jinki
Kina ina ne?
Naje unguwa ne(ta fadi hakan ne saboda in tana case duk sirriksn ta bata fada)
Oh se naga kaman na ganki a airport rd?
Tayi dan jim se kuma tace airport rd kuma?
Eh
To bani bace baki ga daidai ba mezai kaini can.
Koda naji nima nayi msmaki amma kinsan a arean ne aka samu gawar maryam
Oh Allah sarki ina tuki ne zan kira ki anjima ina koma gida
Ok se anjima.

    A ranta kawai tunani take ksla kala haka ta koma gida tea kawai ta sha ta nufi dakin ta tana nazarin abubuwa da dsma.

    WASHE GARI!

     YAU NE ZA'A FARA CASE DIN WANNAN MATASHIN LIKITAN ABDUL_RAZAK WANDA YA KASHE BUDURWAR SA  BARRISTER MARYAM A HOTEL KO ME YASA ?

JARIDA TA BIYU KUMA TANA DSUKE DA SAKON:-

  BARR.MIHJANA CE TSKE KARE WANDA AKE TUHUMA DA LAIFIN KISAN YAU A BABBAN COURT.

SHIN ZATA BI GASKIYA TA SA A KAMA ABDOOL WANDA YA KASHE MARYAM KAWARTA, KO KUMA ZATA KUBUTAR DASHI A MATSAYIN SA NA MIJINTA.

haks aka dinga yawo da jaridar har tazo gunts murmusawa kawai tayi har ta karasa court.

Tun daga harabar en jarida ne cincirondo suna jiran isowarta aiko tana fitows tayi tozali dasu ta harde hannayen ta a jikin kirjinta, tana binsu da ksllo inda suka hasko mats camera da mic na magana wani dan jarida ya jefa mata tambaya.

Shin zski aiki da basirar ki ne wajan kare mijin ki bayab yayi kisan kai?

Idanuwan ta ta lumshe ta ce mihjina bata bayan karya zan yi komai ne dan gaskiya dan na bayyana me laifi na ainihi wanda yana yawo a gari freely wanda baya da laifi kuma a sake sa ita kuma wadda aka kashe a kwato mata yancinta.

Kina nufin dr.abdool bashi da hannu a kisan?

Tabbas

Am....

Ya isa no more questions ta nufi ciki cikin tako na isa da kasaita ba tada wani tsoro a tattare da ita.

Gaisawa suka yi da barr dake kare maryam (govt prosecutor)

  Mih ki shirya wannan karan zaki fadi a wannan case din.

Murmusawa tayi tace we shall see!

Judge ya shigo aka mike tsaye ya zauna sannan suka zauna, aka koro shari'ar.

Alkali ya bada umarni a fara mukkadamar sabida lokaci.

Govt prosecutor ya mike ya fadi sunan sa IMRAN IMAN Nine wanda nake kare wadda aka kashe.

Mihjins ma ta mike ta koro bayani a kanta ni nake kare wanda ake tuhuma.

Govt prosecutor:- ya mike ya dan mike ya nufi inda abdool yake ya soma masa tambayoyi, da farko ya sunan ka?

Culprit:-sunan abdool razak

Govt prosecutor:-me aikin ka?

Abdul:-ni likita ne!

Govt prosecutor:- kana ds aure?

Abdool:-eh ina da aure

Govt prosecutor:-me nene tsakanin ka da maryam?

Abdool:- uhm budurwa ta ce

Govt prosecutor:-good,kafin kai aure ko kuma bayn auren ka?

Abdool:-Uum kamin nayi aure

Govt prosecutor:-matar ka ta san da dangantakar ku?

Abdool:-kalloj mihjana yayi ganib bama su take kallo ba ya ce da kyar yana kinkina ah'ah.

Govt p:-ya juya point to be noted dr be sanar da matar sa cewa yana da budurwa ba, wannsn case din a bayyane yake abdool ya kashe maryam ne saboda karta tona masa asiri akan dangatakar ta da shi a gun matar ss me yuwa ta masa barazanar in be aureta ba zata fada ma matar sa shi yass ya kasheta ta hanya me muni,ya kirata a hotel ya dau advantage din kadaicin su ya daba mata wuka a wuyan ta wanda bata kuma shurawa ba a gun ta mutu sedai Allah ba azalimin bawan sa  bane  lokacin da yayi kisan staff din hotel din ta gab shi kuma tayi ihu aka zo aka gan sa tun kan ya gudu.

Abdool:- bani na kasheta ba

Alkali:-ya buga guduma alamun yyi shiru kotu zata baka damar yin bayani.

Mihjana:-ta mike ta ce objection mi lord wannan sam ba gaskiya bane hassashe ne na barr imran yake yi ba shi da hujar da ze yanke hukunci a kan wanda ake tuhuma kotu tana aiki ne da shedu da kuma zahiri ba hasasshe ba ngd.

Alkali:-barr imran a kula?

Govt prosecutor:- ya gyada kan sa, ina san kotu ta bani dama dan na kira shedata ta farko wadda ta ga dr abdool na kashe maryam.

Alkali:-kotu ta baka dama.

Muje zuwa!

Vote

Comment.

RASHIN SANI!!!Where stories live. Discover now