chapter 15

486 48 7
                                    

Mihjana wayar ta kawai take dannawa, tana kuma duba agogo bata wani jima ba taji text ya shigo mata a tunanin ta ma insp ne sedai wannan bakon num ne ta sake turo masa message da shi ta buga tsakin bakin ciki.

  GASKIYA KIJ BURGE NI NASAN U ARE SHARP BUT BAN TABA TUNANIN BASIRARKI TA KAI HAKA BA SEDAI KASH KIN MAKARO ZAKI FADI A WANNAN KARON MIHJANA GET READY TO BE FAILED YOUR WELL WISHER!.

    Sanda suka koma cikin kotun tana cike da damuwa take sedai mihjana dakiyar zuciya gareta hakan be nuna a kan fuskar ta ba sema wani shu'umin murmushi da take yi wanda yafi kama da na takaici amma its kadai tasan ma'anar sa.

Kallon culprits din take dayan bayan daya tana sauke ajiyar zucuya na damuwa burin ta yanzu be wuce taga insp ya bullo ba, 

Tana hada ido da mamin maryam ta sakar mata murmushin nasara hakan nan ta ji ta maida mata martinin murmushin ta ce a ranta insha Allah gaskiya zata yi halinta zaku ji kunya a idan duniya maryam I'll ruin u, I'll expose u.

Alkali ne ya fito ya ce a cigaba da kara.

Barr.imran ya mike,

Barr:-ya me shari'a ya kamata kotu ta yi watsi da karairakin da barr take kawo mata tana wasa da hankali bayan bata da wani shaida a kan hakan kawai ta hada mana dan ta kubutar da mijinta daga kisan kan da ya aikata sedai kotun mu me adalci ce muna bukatar ayi mana adalci a kwato mana hakkin mu nagode.

Alkali:-barr ko zaki bayyana mana shedun ki?

Barr mih:-ta mike ya me shari'a bani da bayanin dazan bayar sabida shedun nawa har yanzu be karaso ba sedai a karo na uku ina bukatar wannan kotun me adalci data bamu karun kwanaki a dawo kotu saboda na nemo sheduna nagode.

Alkali:- ya numfasa ya gyara zaman sa ya bude bakinsa, a bisa rashin kwararan shedu da kotun da wadda ake kara ta kawo kotu tayi watsi da hujjojinta da ta kawo tunda bata bada shedun hakan ba dan kotu bata amfani da magana seda sheda saboda haka kotu ta yankwa dr abdulrazak hukuncin kisa ta hanyar rataya yana kokarin singnig ne aka ji wata murya ta dakatar dashi.

Ajiyar zuciya mihjana ta sauke.

Kowa ya juya baya inspector umar faruk ya bayyana kan shi na ambaliyar jini ya dafe gun da hanky.

Wani irin sanyin dadi ne ya zuyarci mihjana da azama ta mike ta na sakar masa murmushi sedai ta tausayawa yanayin da ta gan sa.

    Insp umar:- ya tsaya a cikin witness box ya tsaya ya mika gaisuwar sa hade da bada hakurin kin zuwa da wuri da yayi.

Mihjana:-ya me shari'a ga insp umar yazo da shedar dazata nuna muku maryam tana nan da ranta.

Insp:-haka ne mi lord bayan mun yi bincike me karfi muj gano cewa maryam da ake tunanin ta mutu tana nan da ranta sedai wadda aka samu gawarta ba kowa bace se zulaihat kuma muna da shedar hakan.

Alkali:-idan har kuna ds sheda ta ina?

Insp:-tana waje muna san kotu ta bamu damar da zamu bayyansr da shedar mu.

Alkali:-kotu ta baka dama.

Insp ya sauka daga kan witness box ya fita waje mintuna biyar suka dawo dashi tare da mata guda biyu, daya ta manyanta sedai ba sossai ba , se kuma wata fuskarta lulube da bakin mayafi.

Mihjana:-ta bukaci me lullube da bakin veil din ta hau kan witness box ta.

Mihjana:- hajiya maryam ko zaki iya budewa kotu fuskar ki ta gani ta tabbatar da zarginta a kan ki?

Maryam:-ta bude lulubinta sedai a maimakon fuskar maryam ta ainihi fuskar zulaihat ce ta bayyana a gaban kowa.

Cikin kaduwa mihjana ta zaro idanuwan ta da duk wani mahalukij dake wajan cike da mamaki da alajabi.

  Zulaihat suna na ba sunana maryam ba kuma bsn san tuuumar da ake min ba na jima a hannun dr.mukhtar da meenal suna azabtar da ni ta hanyoyi da dama a dalilin wasu sirrikan su da na sani yau ma da taimakon wannan bawan Allahn na kubuto sedai naji kina ce min maryam ni sunans zulaihat me aikin gidan su anty maryam ce ni.

Innalillahi wa inna illahir rajun kawai mihjana take fada tans kuma maimaitawa kanta ya kulle komai ya kwance mata ta shiga rudani da tashin hankali hakika tana cikin halin RASHIN SANI!!! Ya zats yi? Me mafita? Wannan kuma wane sabon kulli ne? Juyawa tayi ganin idanun kowa na kanta seda taji wani irin jiri na dibarta ta kasa ma wani katabus.

Dan dan dan masu karatu kallo ya koma sama!

Ko kun san me ke faruwa?

Ko kun gane mugun kullin?

Ko zaku iya warware mun wannsn abun?

Nikam er mutan panisau na gaza na afka cikin tafkin rashin sani.

Vote

RASHIN SANI!!!Where stories live. Discover now