chapter 20

959 67 4
                                    


END

Anyi biki na gani na fada tamkar dai auran fari cikin garin kano ta zauna kusa da iyayen ta umar na mata irin mugun son nan kulawa kam ba a magana yana bata taimako sossai wajan aikin ta yana karfaffa mata gwiwa sossai har mamaki yake bata wani zubin ganin yadda ta zama komai nasa duk da aikin sa be sa sun nesanta da juna ba.

Ga mihjana dai ana da juna biyu dan wata hudu abunda ta dade tana so a wancan lokacin a gidan abdool Allah beyi ba ashe tana sa rabo da wani mijin ne bashi ba kuma hakan ya mata dadi da bata haihu da abdool ba.

Seta ajiye aikin na wani dan lokaci kamin ta haihu dama prvt office ne da ita.

Cikin shekara uku ta sambado yara uku maza biyu mace daya
Mazan ne first born din ta twins Muhammad kabir da muhammad sageer ita kuma macen maryam (ahalam)

Ya kamata fa ki sambado mana wasu twins din ko

Uhm Allah ya kawo masu albarka ai abun so ne su din ..naji shiru ne har yau babu wata ajiyar ne?

Hah ai se nan da wata shekarar hutawa muke

Yayi dariya baki isa ba gimbiya yau zami yi wasa kuma zan ci kwallo a raga so ki shirya ahalam na bukatar kswa ita ma

Taya shi dariyar tayi ita ma tace eh man tunda nike haifo su nake wahala ta

Au kin .manta tare muke yin laulayin da nakudar?

Uh gaskiya ne ban manta ba na tuna lokacin da kika haifo maryam ko slippers babu a kafata

Ta tuntsire da dariya wallahi ranan ka ban tausayi rigar baccin na fa ka sa ashe kedai bari matas kin wahala ne ni kuma na rude.

Ya rungoma i love you mih so much

Ta lafe ita ma a jikimsa love you more.

Asuba ta gari

Nagode da bin novel din da kuka yi masoysna

Ina mika muku godiyata ta kasancewa dani a cikinwnnan litaffin me suna RASHIN SANI!

KUSKUREN DA KE CIKI ALLAH YA YAFE ABUBUWAN AMFANA KUMA A CIKI ALLAH YA AMFANA.

INA SON KU IRIN SOSSSI DIN NAN

MU HADU A LITTAFI NA GABA KUKAN SO.

RASHIN SANI!!!Where stories live. Discover now