29-30

553 37 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

2⃣9⃣ - 3⃣0⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_



Tinda ya hango ta yaji nunfashin sa yana sarkewa bai kara shiga wani halin ba sai da kamshin ta ya doke shi. Ido ya lumshe sannan ya bude, akan ta.
"Masha Allah!"
Ya furta a hankali. Tayi masifar kyau wanda bai taba ganin wata tayi make up tai kyau haka ba. Dan haka sai yaji kishin suje can gun dan kada wasu su ta kallon ta ya rasa dalilin jin baya son ana kallon ta.

Yasmeen dake waya da su Aisha bata san yana kallon ta ba sai da ta gama sannan ta juyo suka hada ido. Murmushi ta sakar masa wanda ya kara bayyana kyan ta. Tace
"Big bro kayi kyau lallai na yadda yau ranar kace. Kaga kyan da kayi."

Dan murmushi yayi yace
"Ai kin fini kyau. Kin ganki kuwa? Ya salam gaskiya Princess kinyi kyau sosai anya kuwa zakije dinner nan?"
Fuska ta dan bata tace
"Akan me?"

"Kar ai ta kallon ki."
Dariya tayi tace
"Kai Yaa Fauwaz duk yan mata masu kyau da zaka gani, Gaskiya A'ah akan me?"
Ta turo baki. Shi kan sa yasan in yace ba zata ba bai mata adalci ba dan haka dole suka dauki hanya dan zasu su dauko Billy. Gefen titi ya parking ya dauki wayar.
"My Fauwaz ka zarce wajen kawai muma mun tafi!"
Billy ta fada.

Kai ya gyada kamar tana kallon sa sannan yace
"Ok gani nan!"
Ya juyar da kan motar zuwa titin da zai sada su da inda za ai. Har su Billy suka karasa basu je ba. Sai da taku san five minute sannan suka karasa.

Parking yayi ya zaro bandir din 1k ya mika mata. Amsa tayi tai godiya ta juya zata bude mota. yace
"Ba muyi pics ba!"
Juyowa tayi sai ganin flash tayi ya dauke ta. Kan ta kara wani yunkurin ya kuma daukar ta. Zatai magana ma haka dan haka sai ta tsaya yai tai mata har ya gaji sannan suka fito ya musu daya tare. Ba karamin kyau sukai ba.

Suna tsaye sai ga su Billy ita da kawayen ta. Kyau iya kar kyau Billy tayi kyau. Itama ta saka kalar kayan Fauwaz tana ganin Yasmeen ta saki murmushi ta janyo ta akai musu pics sannan Fauwaz sukayi. Gefe taja dan zasu shiga ganin ta tsaya a can gefe yasa ya matsa ya kamo hannun ta. Dole tana gefen sa suka shiga dan yan rakiyar ango da amarya.

Har sit suka karasa dasu Yaa Fauwaz da kyar ta samu ta kwace hannu ta tayi wajen su Aisha. Nan aka fara gabatar da biki kawayen amarya suna sha rawa. Ana zaune dan an fara serving mutane aka kira babbar kawar amarya dan ta bada tarihi amarya+ nan ta fito cikin iyayi tafara bayar wa, har ta gama sannan ta koma.

Yasmeen na zaune taji an kira suna ta tazo ta bada tarihin Yaa Fauwaz. Wata faduwar gaba taji. Da yake suna sit din gaba dan haka ta kalle shi. Shima ita yake kalla yai mata kur da ido. Kai ya gyada mata hadi da mata nuni da hannu alamar ta tashi taje. Jiki a sanyaye ta mike ta isa gun mc ta amshi spearker nan tayi sallama. Cikin harshen turanci kamar yadda kawar Billy tayi haka yasmeen tayi. Ta gabatar dashi da rayuwar sa a komai sannan ta bawa ango da amarya shawara ita kan ta tayi mamakin yadda ta iya wannan bayanan ai kam tana gamawa aka hau tafi kan ta farga sai jin ruwan kudi tayi akan ta tana dagowa taga Yaa fauwaz ne dan haka tai kasa da kai. Nan DJ ya saki kida,  nan vedio man da mai hoto suka hau haska su. Sai da ya karar da bandir biyu yan 1k sannan ta koma ta zauna kowa ta burge shi sosai. tana komawa Aisha tace
"Kinyi kokari sis ban zata zaki iya magana haka ba."
Murmushi tayi kawia.

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now