*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_7⃣5⃣ - 7⃣6⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*
Kwana yayi bai runtsa ba tin daga lokacin kuma ya rasa me ke masa dadi da wani ciwon kai ne ya taso shi a gaba. Bayan nan sai yaji numfashin sa na fita sama sama, sam ko motsa jikin da yake zuwa ya ajiye shi, gawani faduwar gaba da yake ji sannan baya son cin abinci kwata kwata ga damuwa ya rasa ta ina zai fara. Kullum zai kira ta suyi hira amman ya kasa tarar ta da zancen.
Kwance yake yaji numfashin sa na fita da kyar wannan yasa ya mike zaune, yana dafe kirjin sa. Ido ya lumshe fuskar ta ke masa gizo wannan yasa ya dauki waya ya fara neman layin ta. Tana cikin yan uwan ta suna ta hira wadda yawancin ta akan Yaa Fauwaz take basu labarin sa. Siyama bata nan da bama ta fara ba. Wayar ta tai kara tace
"Kunga dan halak!!!"Ta dauka tare da fadin
"Assalamu Alaikum Yaya na ya kake ya England?""Wa'alaikumsalam!"
Ya amsa muryar sa na fita a hankali. Wata zabura tayi ta gyara zama tana fadin
"Lafiya kuwa ya naji muryar ka haka? Ko baka da lafiya ne?"Duk ta rude, yasan ko ba soyayyar sa a zuciyar Yasmeen tausayin sa zai rinjaye ta ta amshi soyayyar sa. Dan haka ya dai dai ta murya tace
"Ke Princess daga bacci fa na tashi."Ajiyar zuciya ta sauke tana fadin
"To ya kaka?""Lafiya lou. Yaushe zaki dawo daga maidugurin ne?"
"Nan da sati biyu.""Ok ina son in kun dawo na zo ne!"
"Ok I will let u know in zamu dawi yasu Anty Yagana kice ina gaishe fa kuma ina nan zuwa nima.""Ok zan fada mata."
Sukai sallama. Asibi yar gidan Anty Yagana da ta girmewa Yasmeen ta kalle ya yace
"Ooo ashe yar gida za ayi?""Name fa?"
"Ke da Yaa Fauwaz man ashe soyauya kuke."Dariya tayi tace
"Me kika gani? Ni ba wata soyayya tsakani da Yaa Fauwaz!"Dariya Asabe tayi yace
"Yasmeen kenan duk wanda yaga yadda kuke ke da Yaa Fauwaz sai yasan akwai wani abu a boye tsakanin ku. Bayan nan sai dai bamu zauna ba baki da labari sai nashi ko saurayin ki daya baki taba bamu labarin sa ba wannan ya nuna min shi din ne dai saurayin. Kinsan shi dai mata basu zauna ba amman da sun zauna zaki ji suna zancen mazajen su ko samarin su. To ke da wannan ya bada na saurayin sa ke sai ki bada na Yaa Fauwaz. No wonder wallahi ki rike abinki dan Yaa Fauwaz ba abun yadawa bane ya hadu ta ko ina."Shiru kawai Yasmeen tayi dan ta rasa mema zata ce dan ita kam ta shiga uku kowa sai ya gane tana son Yaa Fauwaz. Dariya yan dakin suka dauka suna fadin
"Feel free sis menene a ciki to?"Hawaye ne ya taru a idon ta wannan yasa ta mike ta bar dakin da sauri. Ba wanda ya lura sai asabe dan haka ba tare da kowa ya lura ba itama ta mike ta bi bayanta.
YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.