*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_107- 108
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a adidu'a Mommy na da Mommy nah)*
Handle din kofar ya murda kamshin dakin ya doki hancin sa. Ido ya lumshe, fitilar dakin ya kunna ya hange ta can cikin bargo tana bacci, fitilar ya kashe ya nufi gadon ya kwanta ya janyo ta jikinsa ai kam sai ta kara shige masa. Hancin sa ya daura a wuyan ta yana shin shina kamshin jikin ta. Ya jima a haka ya kasa baccin saboda wani abu da yaji wana neman ya yafi karfin sa.
Can cikin dare ta farka taji ta jikin mutum zabura tayi tana mai kiran sunan Allah. Yaa Fauwaz ya tashi, yana fadin
"Menene?"Kai ta girgiza. Hannun ta ya jawo ya kwantar da kanta a kirjin sa. Take tsigar jikin su ta mike a lokaci daya. Sun jima basu koma baccin ma kowa na sauke numfashin sa a hankali sai daga baya baccin ya dauke su gaba dayan sa.
Sai asuba ya farka, yaji dadin baccin dan ya dade baiyi bacci irin na yau ba mai dadi. Ita ma ta farka amman ta kasa tashi. Saboda nauyin sa da take ji.
"Princess!""Na'am!"
Ta fada tana kara shigewa cikin jikin sa."Asuba tayi!"
"Toh!"
Ta fada tana janye jikin ta. Mikewa yayi ya shiga toilet yayi wanka ya alwala sannan ya fice.Yana fita ta mike ta shiga tai wanka ta dauro alwala sannan tazo ta saka hijab din ta dan tayi sallah. Bayan tai sallah ta hau gado ta kwanta can kuma ta mike ta fara aiki gyara gidan. Tana gamawa ta fada kitchen.
Dankali ta soya da kwai sannan ta tafasa ruwan tea da yaji kayan kamshi. Tayi masa farfesun kayan ciki ta jere a dining. Wanka ta shiga tayi tana fitowa ta turare jikin ta sannan ta shafe jikin ta da hadin da wacce tai mata gyara ta bata. Wata yar armless riga ta saka iyakar ta gwiwa ta kamata daga sama daga kugun ta ta baje ta saka skin tie ta kama gashin kanta ta kara wanka da turare. Kamshi ya dinga tashi a jikin ta. (wallahi duk talaucin da zakiyi kada ki yarda ki rasa turaren kaya kona jiki wato body spray da kuma humra. ki kasance mai yawan anfani da turanren wuta na gida ko kuma room freshener. Domin kamshi rahama ne. Kuma kada ki bari maigidan ki ya shaki wata iska daga gareki ba tare da ta fita da kamshi ba.)
Tana tsaye Yaa Fauwaz ya shigo, kallon ta ya tsaya yi, sanye yake da gajeren wando da jar riga sai kamshi yake yayi kyau dashi.
"Ina kwana?"
Ta fada tana durkusawa dago ta yayi yana fadin
"Kin tashi lafiya?"Kai ta gyada. Magana yai mata a kunne ta rufe fuska da hannun ta. Janta yayi sukai falo ya zauna a kujera ya daura ta akan cinyar sa. Nan yakara sata a cikin jin kunyar sa. Tace
"Yaya kazo muci abinci!""Kina jin yunwa!"
Ya mike ya kama hannun ta sukai dining. Tana bude fulas din kamshi ya cika wajen ido ya lumshe yana mai farin cikin yau gashi a gidan sa zai yi breakfast da abincin mai dadi ba tare da ya sha wuya wajen siya ko sawa ai masa ba an masa dan yaji dadi. A gaskiya Ya godewa Yasmeen kuma Allah yayi mata albarka.
YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.