*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_1⃣2⃣1⃣ - 1⃣2⃣2⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a adidu'a Mommy na da Mommy nah)*
Sai da tayi sati uku a gida lokacin ta warware kamar batai wani ciwo ba. sosai Mommy ke kula da ita haka nan Ummi sai kara gyara ta suke sai kace wata sabuwar amarya. Duk da ta dan rame amman tayi kyau.
Ummi ganin abun da Mommy kewa Yasmeen da zuciya daya yasa yanzu duk ta sake bata jin komai akn yadda Yasmeen ke agun ta dan ta gane facalar tata basu da matsala sun dauke ta kamar kanwa ga yadda ta rike mata yar yayar ta. Wannan yasa yanzu take kara ganin girman ta sosai.
Kullum suna waya da Yaa Fauwaz soyayya suke kamar sa yi me? Duk lokacin da zasuyi wasa tana zaune a gaban tv tana kallan duk motsin sa ko yaya ya fadi ko aka buge shi kamar ita aka yiwa. Kuma in sukai waya tai ta masa sannu tana kara masa kwarin gwiwa abinda yake saka shi kara bada himma dan ji yake kamar agaban Yasmeen yake buga kwallon yadda yake kokari, yasa in dai za ai ball in sunci to har dashi a wanda da suka ci. A lokacin taga Abbas shima a wasan.
Lokaci bikin Aisha ya yi za aje Gombe, ana ta shirye shirye dan Yasmeen so tayi ana sauran sati taje amman da ta fadawa Yaa Fauwaz ma da farko cewa yayi ba zata je ba kwata kwata. Amman da ta kwantar da murya da lallashi da lallaba sai gashin yace taje amman kwana biyar ya bata. Kamar tayi kuka amman tace ta gode.
Wannan yasa bata tashi tafiya ba sai ranar litinin acan akai musu lallai da gyaran kai. Sun je sunga tarba a dagon Aisha dan har da Ummi da Siyama da wasu yan uwan Mommy sukaje Mie Mie tace zasu zo daukar amarya.
Ranar laraba akai bridal shower alhamis akai kamu juma'a Mamin ta tayi yini, asabar akai daurin aure dinner aka ce sai an kawo amarya Kano za'a yi. Ranar asabar din suka dawo su da amare anan gida aka sauke ta dan sai lahadi akai dinner aka kika amarya gidan angon ta dake can rijiyar zaki. Gida yai kyau sosai aka taho a ka bar amarya da ango.
Duk da tana cikin bi hakan bai hanasu shan wayar su ba dan sai suyi awa suna waya Aisha tai tayi musu tsiya. Washe gari Yasmeen taje ta kara gyara mata inda ya dace ta gyata sannan ta taho.
Sati daya da biki Matar Yaa Ishaq ta haihu aka samu Baby Boy, ran suna Babyn yaci sunan Baba wato Ahmad ake kiran sa da Ammar, Yasmeen kuwa take ce masa mijin wai sunan Yaa Fauwaz.
Billy kam tin da suka rabu da Yaa Fauwaz ta kara kaimi gun Business din ta dan aikin ma ba sosai take zuwa ba sai yawo yau tana gari can gobe can, kuwa kawayen ta sunja hankalin ta, ta fara harkar kula mata wanda har ta waye a cikin sa.
Wannan world cup din da ake tana zauna tana kallo ranar da ake da yan Nigeria tana ganin Yaa Fauwaz sai da gaban ta ya fadi dan yadda ya kara kyau yai kiba ya dawo ainihin Fauwaz din sa dan da ka kalle shi baka ce yana da aure ba kamar saurayi take son sa ya dawo mata sabo taji ina ma taje taga wasan ido da ido sai dai ba zata iya ba.

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.