*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_4⃣1⃣ - 4⃣2⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy da Mommy nah)*
Yana wajen a zaune sam ya kasa tashi sai tunane tunane yake har karfe daya tayi ya mike ya dauro alwala anan masallacin dake jikin gidan sa yai sallah. Bayan ya idar ya koma gida.
Karfe biyu dai dai ta shigo gidan sanye da dogon siket pencil duk ya kama jikin ta sai yar karamar riga da ta dame ta. Kanta ba dan kwalli sai wani dan karamin shara sharan mayafi da ta daura a kanta wanda iya kar sa kafada. Sai wani hill shoe da jakar ta rike a hannun ta. Tana tafe tana waya.
Yana zaune yana kallo da ba gane me ake a Tv yake ba ta shigo, dagowa yayi yana kallon ta shigar ta kara bata masa rai, ace matar aure ce wannan ai ba wanda zai yadda in ma an fada masa.
Tana ganin sa ta karasa wajen sa fuska a shagwabe tana fadin
"Honey na!"Bai kula ta ba dan yau ta kai shi bango. Dagowa tayi tana kallon sa tace
"Ya dai ko baka da lafiya ne?"Kai kawai ya girgiza mata tace
"To menene?"A hasale yace
"Au tambayata ma kike menene? Ace ki fita tin sassafe babu ko sallama. Bayan kinsan yau kusan kwana na talatin da biyar bana gari dole zan bukace ki, haba Billy!"Dan murmushi tayi dan ita sam bata wani ji damuwa dan ta fita ta barshi a gida ba.
"Goya ka zanyi mu tafi ne Fauwaz. Baga Peeta nan ba zai maka duk abinda kake bukata.""No billy ba komai ba, shin Peeta zai biya min bukatata ne? Ko kuwa zai zauna yai min hira?"
Dariya tayi tace
"Lallai wallahi Peeta ya iya bada labaran ban dariya a gida shi ke tayani hira. Kai ko da baka nan ma shi ke tayani hira sai mukai dayan dare yana ban labari kuma sam bana gajiya."Kai ya dafe da hannu dan ya gane sam billy ita bata dauki wadan nan abubuwan a ba dai dai ba. Shin ta ina zai bullowa Billy ne? Yana cikin tunanin Devid ya danno kai. Duk da a yadda suke bai ji kunyar komawa ba sai ma shigowa da yayi yace
"Maa an gama abinci yana dining akwai abinda kike bukata?"Fauwaz ta kalla tace
"Baby me kake bukata?"Wani kallo ya watsa mata sannan yace
"Nothing!"Kallon Devid tayi tace
"U can go!"
Ya fice. Kallon ta yake yana mamakin ta wai Peeta sai sukai karfe dayan dare yana bata labari bayan nan ma yasan zata iya fitowa daga ita sai sleeping dress. Wai shin ita me ta dauki wadan na yan aikin nata ne kawayen ta ko yan uwan ta da ta sake dasu har haka. Kuma bata damuwa su ganta a ko yaya ne? Yanzu ma kalli da shigar da ta fita ko a tsarin addinin musulunci hakan bai dace ba bare kuma ace matar aure har da igiyoyin uku akan ta.Sai ya tino Yasmeen da sam bata zama a hijab kuma kaya ta masu kyau da daraja. Bata saka kayan da zai dameta ko fito da surar ta.
"Baby!!!!"
Ta fada da karfi dan ta kira shu yafi sau uku bai ma san tana yi ba. Kallon ta yayi yace
"Ya akai?"
Kama hannun sa tayi sukai gun dining. Yau da kanta tai serving nasa dan taga alamar yau baya cikin mood din sa. Kasa cin abincin yai sai wasa yake da spoon din yana tunanin rayuwar sa da ta Billy.
Kallonsa tayitace
"Kai Baby yau akwai abinda ke damun ka. Shin menene matsalar ka?"Kallon ta yayi yana mai jin son ta amman bangare na zuciyar sa na fada masa sam Billy bata dace a so ta ba tinda bata san kanta ba bata san komai nata ba. Kishin ta yaji yana ratsa shi.
"kai min magana man please Baby what wrong with u?"Ajiyar zuciya yayi yace
"Baby wallahi ban son wadan nan yan aikin naki. Wallahi bai dace ba a al adance bare a addinan ce ke ba muharamar su bace da zaki na taraya dasu. Ko voice din ki ma bai dace su naji ba bare kallon wani bangare na jikin ki. Amman please kalli a yadda kika fita bayan nan ko a wane hali samar ki suke ba ruwan ki bare damuwa."Tin da ya fara magana take kallon sa wani irin kallo take masa, irin rainin nan sai da ya gama tace
"Ka gama Sheihk, daman ba tin yau ba ka tsani wadan nan masu min aikin in har kana so na koresu sai dai in kai zakana min komai dan na fada maka ni ban iya ba. Bafa kai kake biyan su ba bare kace kudin yai maka yawa ko something else.""Oh my god Billy please ki tsaya ki saurare ni mana. Ke bakya tsayawa ki fahimci abu kike fara fada. What I want u to understand is mu musulmai ne dole ne muna bin dokar Allah....."
"Allahu Akbar!!!"
Ta fada tana mai cigaba da magana,
"Kada ka manta tin a waje kan na amince maka na fada maka babu takura. Akan me zaka zo kana bata min rai kullum magana daya. Daman ku maza haka kuke sai kun auro mace ku zo kuna cewa baza tai kaza da kaza ba toni wallahi baka isa ba. Akan me, zaka tsaya kana ce min addini bai hallata ba kai komai yin sa kake a tsarin addinin. Kaga in bazaka iya ba ba dole amman ni da su Devid baka isa ka raba mu ba dan ni ba a yan aiki kawai na dauke su ba they are like my brothers."Maganganun sa ba karamin kona masa rai suke ba amman ya danne dan in har yai fushi yasan dukkan su ba zasu ji da dadi ba. Sonta ne kawai ke sa yake hakuri da duk abinda take masa amman da bata isa ko kallon banza tai masa ba. Mikewa tayi zata bar wajen da sauri ya kamo hannun ta yana fadin
"Haba Baby nida ba abinda kike nufi nake nufi ba. Kawai so nake masu miki hidima su koma mata!"Wani kallo ta aika masa tace
"Dan kana kallon su ko?"Cikin zafi yace,
"What did u mean? To nima kuwa sai wadan nan kedaran sun bar min gidana!"
Tsaki tayi sannan ta kalli gidan sannan ta mai dashi kan Fauwaz din tace
"Gidan ka din banza wanan gidan har shi kake takama da wani gidan ka. Ai wallahi fauwaz da ba dan darajar soyayya ba da ba abinda zanyi da wannan gidan. Ka san ni wace kasan daga inda nake, kasan hali na kasan ba wanda ya isa ya sauya min ra'ayi dan haka ka bini a sannu in ba haka ba dagani har kai ba zamu wanye lafiya ba."
Ta buga masa tsaki tayi dakin ta da sauri.Yadda zuciyar sa ke masa zafi da tafasa yasa, ya koma falo yana danne zuciyar sa. Billy ta bala'in bashi mamaki da tsoro. Shin haka zaman su zai kaya kenan. Yana zaune idon sa a lumshe yaji takun ta. Ta fito cikin riga da wando sai dan mayafi da ta daura akan ta, ko kallon inda yake batai ba ta fice daga dakin kan yai wani motsin sai jin tashin motar ta yayi. Ransa ya kuma baci shin da izinin wa ta fita. Ya jima a dakin yaga in ya cigaba da zama a gidan nan zuciyar sa zata iya fashewa dan haka ya fita ya shiga motar sa. Zageye garin ya farayi can ya yanke shawarar zuwa gidan Marzuk.
Waya yayi wa Marzuk din cewa gashi a compound din gidan shi nan ya fito tin daga kallo daya ya gane da akwai matsala. Dan haka yace su shiga ciki. Haka ya fito suka shiga. Anty binta ta fito tana gaisar da shi ciki ciki ya amsa tana fadin
"Ina Amarya mu ba muje ba itama bata zo ba.""Wallahi!"
Kadai ya fada ya gintse bakin sa. Shima Marzuk yana ta tsokanar sa. yana fadin
"Angon Billy hankali ya kwanta dai ko?"
Sai yaga ya mai shiru. Wannan yasa yace
"Yadai friend me yake faruwa ne?""Ni da Billy ne, wallahi friend tin da akai auren nan banda kwanciyyar hankali hakuri kawai nake da ita amman ita takasa ganewa yau ta mugun bata min rai!!"
Nan ya bashi labarin duk abinda ya faru. Marzuk akwai zuciya da saurin fushi ai nan ya hau fada sai kace shi akaiwa.
"Ai duk laifin kane, ya za ai tin farko baka ja mata birki ba. Wannan ba matar aure bace ai na fada maka tin farko ace mace ko gas bata iya kunnawa kana zaton a haka zaku kare rayuwar taku kenan. A haka zata haifa maka yara ta basu tarniyya. Gaskiya Fauwaz da sake, duk laifin kane. Ai sai da na fada maka ka samu macen kirki wacce tasan me take amman idon ka ya rufe ko da yake har yanzun ma idon ka a rufen yake. Ni dai shawarar da zan baka shine wallahi kada ka soma yadda da wannan shirmen dan ranar gobe kiyama har da kai a laifin yanzu gyaran tarbiyyar ta na hannun ka dan haka sai ka tsaya tsayin daka kaga ta gyaru."Bai koma gida ba sai bayan isha'i zaune ya same ta a falo daga ita sai wata shimi wacce tazo mata iyakar cinyar ta. Gashin kanta ta baza shi a gadon bayan ta. Yana shigowa ya daura idon sa a kanta take yaji tsigar jikin sa ya tashi. Nan da nan ya manta me ya kawo shi dan yadda ta tafi da hankali sa.
"Baby na!"
Ya fada yana zama a kusa da ita. Bata kalle shi ba dan ita har lokacin fushi take dashi. Dan bayan fitar ta ta hadu da wata kawar ta nan tagan ta itama rai abace take tambayar ta lafiya. Bata boye mata komai ba ta fada mata."Ai kinji matsalar auren kenan. Ace baka da kwanciyyar hankali. Sai da tin farko nace kada ki yadda kiyi aure, amman baki yadda ba kika jr kikai aure ai gashi nan zai raina ki da girman ki da aji ki kuma in har baki taka masa birki ba wallahi haka zai samu yai ta jan ki a kasa."
Nan ta gama zuge ta."Baby yunwa nake ji!"
"Ai kasan inda abincin yake ko?"
Bai ji dadin kalamar da ta fada ba amman ba yadda zai yi. Mikewa yayi ya nufi dining din inda ya tadda kala kalar abinci. Zubowa yayi ya zauna yaci sai da ya gama ya dawo falo.Tana nan inda ya barta dan haka ya zauna yana fadin
"Wai fushin kike har yanzu?""Kada nayi ne?"
Ta tambaya."Kiyi hakuri baby duk abinda kikaga ina yi sonki ne ya saka nake yi da kishin ki shike sani aikata abinda nake yi amman dan Allah kiyi hakuri. Da bana soki ba zan taba yin kishin ki."
Jikin sa ya janyo ta yana shafa gashin kan ga yana mata kalaman da zasu sata jin sanyi a zuciyar ta. Nan yai ta kalalame ta da kalaman sa har taji ta sake ta sauko dan itama ta sani Fauwaz daban yake a cikin mazaje dan ya iya soyayya duk da ita wani abun bata sake masa tai masa wai dan kar ya raina ta amman shi ba abinda baya mata.
Dagowa tayi tace
"Baby ka daina min irin wannan abin?"
"Am sorry bazan sake ba."
Yaja hancin ta.Nan suka lulla duniyar ma'aurata ya kara samun kan ta. Ta sauko har itama ta manta da komai.
Kwance suke tana kan sa sai shagwaba take masa,
"Baby na!!
Ya kira sunan ta. Amsawa tayi tana fadin
"Yane Honey!""Wallahi ina son ki, kuma ina kishin ki, tabbas in dai ina gannin yan aikin naki wata rana zaki gani na mutu dan zuciya ta bugawa zatai."
Yadda yake maganar cikin shagawaba da sanyin murya shi ya kashe mata jiki daman ga hannun sa yana wasa dashi a bayan ta."Yanzu me kake so?"
"Akan wadan nan yan aikin mana, zan fadawa Mommy ta samo miki yan mata suna miki aiki!"Shiru tayi bata ce komai ba. Yace
"Ba za a kori su Devid ba amman sai suna miki aikin waje, ni dai bana son suna kallan min ke wallahi. Please baby say something!""Baby but kasan nima ina son ka na kishin ka ko?"
"Really!"Dukan kirjin sa tayi yai Yar dariya yayi yace
"Ni da nake da ke wa zan kalla, duk matan duniya kamar maza nake ganin ke ke kadai ce mace a ido na ke kadai kike da abinda zan kalla. Me zanyi dasu. "Taji dadin yadda ya yabe ta dan haka itama sai tace
"Na amince amman gaskiya aka kawon wadan da basuyi min ba sai an canza!!Da sauri yace
"kada ki damu sai wadan da sukai miki."
Nan ta rumgume shi saboda yadda yake zura hannun sa a cikin kasan rigar dake jikin ta.Washe gari baya gidan bayan ta dawo daga aiki wajen karfe biyu sai ga Siyama da Kanwar ta yar shekara biyu nan da wani kanin su dan gidan Alhaji Karami mu'azam. A falo suka same ta nan suka gaishe ta suka ce kannen Fauwaz ne. Daga haka bata kara kula su ba sai kallo da take can bayan awa daya ta mike tace
"Bacci nake ji, zan je na kwanta ku gaida yan gidan!"
Tayi dakin ta abin yai matukar batawa Siyama rai dan daman batai niyyar zuwa ba Abba ya takura sai da taje. Tana komawa gida ta juyewa Mommy abinda Matar Yaa Fauwaz tai musu Mommy tace zai zo ya same tane.Ko da Yaa Fauwaz ya dawo ma ta manta da kannen sa sunzo bare har ta fada masa.
*Need more comment and vote*