109-110

912 56 1
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

1⃣0⃣9⃣ - 1⃣1⃣0⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a adidu'a Mommy na da Mommy nah)*

Not edited


Ido ta bude tana kallon bayan sa tana jin tashin motar sa ta mike tayi kitchen. Nan ta hau aikin abinci. Tayi dambun shikafa da yaji kayan lambu, yai kyau, tayi potato ball tayi kunun aya da yaji madara da kwakwa sannan ta saka a firij.

Sai da ta gama ta dauraye abubuwan da ta bata ta kaje ta jera a dining sannan tashiga daki duk da ba datti yayi ba ta kara gyarawa ta kara saka turaren wuta. Wanda gidan baya rabuwa da kamshin sa.

Bandaki ta shiga tayi wanka ta dauro alwala dan ana kiran sallah la'asar ta fito ta shafa mai tai kwalliya ta hade jikin ta cikin kamshi, sannan ta saka wata doguwar riga mara nauyi ta kamata ta kwanta a jikin ta ja ce tai maka kyau ta karai mata haske, ta saka Hijab tai sallah.

Kitchen ta shiga ta tsiyayi hadin da Anty Binta ta aiko mata dashi, dan zakin sa ke sawa ta sha. tana kitchen din taji shigowar Yaa Fauwaz, sallama yayi a falo ta fito daga kitchen ta amsa ta taho cikin takun ta na kasaita da yanga tana wani lumshe ido, tace
"Yaya sannu da zuwa!"

Yaa Fauwaz tini yayi mutuwar tsaye, saboda tozali da yayi da hadaddiyar Babyn sa Yasmeen. Ya bude mata hannun sa a hankali ta tako zuwa wajen sa ta shige ya rufe hannun yana sauke ajiyar zuciya tare da sauke kan sa akan kafadar ta yana shakar kamshin turaren ta mai dadin kamshi.

Muje ka watsa ruwa zafi ko?"
Ta jashi sukai dakin sa shi dai binta yake kamar wani soko, a haka suka shiga dakin. Dakin wani kamshi na daban yake yi. Ido ya lumshe sanman ya bude, ta riga ta hada masa ruwan wanka dan haka tace
"Na hada maka ruwan!"

Ta fada tana yin waje juyowa yayi yana binta da kallo yadda kugun ta ke juyawa. Murmushi ya saki ya cire kayan sa ya shiga bandakin.

Shi kansa ruwan wankan nasa kamshin turare yake yana zubawa yana lumshe ido dan dadin ruwan yake ji mai dumi ga kamshi. Shi kansa bandakin kamshi yake na daban. Kwanciyya yayi cikin bahon yana tunanin rayuwar sa ta baya da ta yanzu, kullun yana mai kara godewa Alhaji da ya bashi Yasmeen abar son sa. Wai yau shine har da hada masa ruwan wanka mai kamshi gida a gyare yana kamshi ga abinci mai lafiya da gina jiki. Haka yai wankan cikin nishadi.

Yasmeen ta dawo dakin kayan da ya cire ta ninke sannan ta fito masa da wasu bayan ta feshe su da turare masu kamshi sannan ta ajiye masa a gefen gado ta koma falo.

Yaa Fauwaz ya fito ya goge jikin sa ya shafa mai sannan ya fesa turare, kayan da ta ajiye masa su ya saka sannan ya fito, a falo ya same ta ya karasa ya rankwafa yace
"Baby na sannu da gida!"

Murmushi kawai tayi tace
"Yaya yasu Mommy/"

Zama yayi ya daura kan sa a kafadar ta yace
"Tana lafiya tace agaishe ki,"

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now