*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_9⃣1⃣ - 9⃣2⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*
*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*
A gida kuwa sai neman Yaa Fauwaz ake amman ba a samun sa a waya sai iyayen suka zata ko baya kasar ne amman sun san dai duk in da yake zai dawo kan bikin. Amman abin mamaki har ana gobe fara bikin yan mata ba shi ba alamar sa.
Sam Mommy bata damu ba dan tasan kilan cewa zai ba zai hallaci Bikin ba dan haka tace tafi nono fari.
Abba mahaifin Yasmeen shine ya tada hankalin sa dan yasan ko Fauwaz baya gari suna waya haka nan duk friday zai masa barka da juma'a amman sai yaga wajen sati biyu bai kira shi ba kuma ba text dan haka ya kira wayar sa bata shiga har gidan sa ya je aka ce masa baya nan matar gidan ma haka. Sai da ya koma gida ya kira Marzuk akan yaje.
A falon sa ya same shi ya shiga da girmamawa ya gaishe shi ya amsa yana fadin
"Marzuk ina Abokin ka ya shiga duk wayoyin sa a kashe na tura masa sako ta email duk ba respond hankali na ya kasa kwanciyya akan Fauwaz yana lafiya ka fada min in kasan wani abu."Kai yayi kasa dashi yace
"Kayi hakuri Abba naso na fada maka amman ya hanani dan yace bai son hankalin ku ya tashi, kuma ganin ina tsaye akan sa yasa ban sanar daku din ba amman nima ganin yadda jikin nasa yayi zafi jiya yasa na yanke shawarar zan zo na fada muku nasan ku iyayen sa ko da addu'a kuka taya sa zai samu sassauci. Amman kayi hakuri banki fada dan jin dadi na ba. Fauwaz yana kwance a asibiti wajen sati biyu."Kai Abba ya dinga girgizawa yana fadin
"Innalillahi wainna illahir rajiun. Assha! Amman baku kyauta ba. Yanzu yana asibtin?""Eh Abba!"
Kai ya jinjina yace
"Tashi muje naga jikin nasa. Daman tinda ake neman sa hankalin na ya kasa kwanciyya, ashe bai da lafiya, Allah ka bawa yaron nan lafiya tashi muje."Suka mike suka isa asibitin. Hankalin Abba bai kara tashi ba sai da yaga a halin da Yaa Fauwaz yake Abba sai da yai hawaye bayan ya bar wajen sa gun likita ya nufa.
File din sa Likitan ya bude yana fadawa Abba abinda yake damun sa bayan ya gana ya mikawa Abba File din dan ya kara gani. Sosai jikin amman yai sanyi ace yaro kamar Fauwaz shike da ciwon zuciya har haka, dan yanzu da yaje gun sa ramar da yayi ta tada masa hankali yana bacci amman daga gani ba bacci dadi yake ba.
Hawayen idon sa a goge yace,
"Allah ka tashi kafadun Fauwaz, Allah ka bashi kafiya "Likita ya kalla yace
"Yanzu ya ake ciki?"Ajiyar zuciya Likita ya sauke yace
"Hakikanin gaskiya ciwon zuciya ciwo ne mai babban matsala da hatsari, ba wai kamar zazzabi ba in baka da lafiya a baka magani da allurai shikenan kasha ka warke, shi wannan duk maganin da ake sha in har mutun bai da nustuwa kuma bai samu abinda yake so ba a banza dan za ai tashan maganin yanayin wani wajen. Dole asan menene matsalar da ta haifar masa da ciwon dan ta nan ne za a samar masa abun har ya samu kwanciyyar hankali daga nan kuma sai magani ya fara aiki. Ni na tambaye shi sam yaki ya fada min amman ban sani ba ko kai zai fada maka. Amman a gaskiya Fauwaz yana cikin critical condition da yana gab da rasa rayuwar sa.""Innalillahi wainna illahir rajiun!"
Haka Abba yake ta fadi dan hankalin sa yai mugun tashi. Ya fara tunanin me ya kawowa Fauwaz wannan mugun ciwon. Kai ya dafe yana tunani. Can ya kalli doctor yace,
"Bari yanzu zan je naga ya jikin nasa yake."Ya mike jiki a sabule ya nufi dakin yana kwance amman kamar bai da rai sai numfashi da yake yi kawai, ya rame sosai. Ido ya zuba masa yana mai zuvar da hawaye tausayin yaron ya kama shi. yana tsaye ya bude idon sa ganin Abba a kusa dashi yasa ya fara kokarin mikewa, da taimakon Abba ya zaunar dashi.
"Ina yini Abba?"Fauwaz ya fada yana dafe kirjin sa, dai dai shigowar Marzuk. Abba yace
"Sannu Baba na ya jikin?""Da sauki!"
Ya fada yana lumshe idon sa. Marzuk ya taho kusa dashi ya dafa shi yace
"Sannu!"Kai ya gyada masa. Sun jima a haka sannan Abba yace
"Fauwaz fada min me kake so?"Kai ya girgiza yace
"Abba ni ba abinda nake so!"Dan murmushi Abba yayi yace
"Fauwaz kenan baka dauken a matsayin uwa ba kenan ko? Ka fada min abinda kake so sai inda karfi na ya kare inda ina da hali Kaji."Ido ya lunshe yana tuna karamcin Abba agun sa wanda duk gidan nan yana daya daga cikin masu son sa da masa abinda suke so. Amman a da shi yaje ya tara da zancen auren sa kuma shi ya shige masa gaba. Sai ya tuna a gaban sa da aka kira shi akan soyayya suke da Yasmeen ya musa bai ji kunyar mahaifin ta ba. Sai a yanzu yaji kunyar mahaifin ta tayaya zai iya fada masa son Yasmeen yake a yanzu. Ba zai iya ba yasan Abba sai inda karfin sa ya kare. Bayan ita Yasmeen din tana son Abbas din nata. Tayaya zai sa ai mata dole. Rashin Yasmeen da yayi yasa yai hankali ya nutsu, kuma baya son kara shiga hakkin wani a yadda yake ganin yanzu mutuwa zai yi.
Tari ya hau yi yana dafe kirji, idon sa ya kawo ruwa. Nan Abba da Marzuk suka hau masa sannu, daga nan ya zame ya kwanta yana mai lunshe ido. Dole Abba yai masa shiru yana kwance bacci ya dauke shi. Kallon Marzuk Abba yayi yace
"Muje waje!"Dan baya son ya tada Fauwaz da ya samu yin bacci
*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+
Halima ta kasance kawar Billy ce amman ba so close ba dan Halima ita bata shigar banza da kule kulen samari abinda yasa Billy ke kula ta ma kenan. Gentle ce kyakyawa da ita. Tana da gata sosai dan babban ta jinin sarauta ne acan garin su.Duk wanda zai zauna da ita sai yasan AB wanda tin taba yarinya take masifar son sa shi kuma bai san ma tanyi ba duk shishige masan da yake sai dai yace Sister sa. Wanda ita kuma son aure take masa.
Tana da ji da kai da gayu wannan yasa duk suke dasawa da Billy a dan gaisa sai kuma in zaman lectures ya kamasu in a kusa suke su dan taba hira. Tin da suka gama ckul tai service taki aure wanda aka bata ita kawai AB take so wanda shi bai san tana yi ba. Sai kwasam taji an saka ranar auren sa abinda ya daga mata hankali. Acan garin su kawar ta ta kwantar mata da hankali shine ta taho Kano yanzu ta hadu da Abida har ta kai ta gun boa.
*Anty ce!!!*
YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.