115-116

774 51 2
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

1⃣1⃣5⃣ - 1⃣1⃣6⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a adidu'a Mommy na da Mommy nah)*


Alhaji Babba ya kira kannan sa ya fada masu duk abinda ya faru, nan Alhaji Karami ya hau fada dan daman shi yafi su fada yace
"Tinda haka suka bukata ya bata takardar ta."

Abba yace
"Ba za ai haka ba a kira Fauwaz din aji ya abin yake,"

Sahawarar Abba aka dauka nan Alhaji Babba ya kira shi, Yaa Fauwaz yana baccin rana kiran Alhaji Babba ya shiga dan haka yace ya zo nan ya tashi  Wanka yayi ya shirya sannan ya nufi gida.

A can babban falo ya samu Alhaji Babba da Alhaji Karami har da Abba sai abin ya bashi tsoro to lafiya. Zama yayi ya gaishe su. Alhaji Babba ne yai musu bayani abinda ke faruwa nan Alhaji Babba yace
"Babana ba dai dan ka auri yar uwar ka kake wulakanta ta ba."

Fauwaz mamaki ya kamashi shi me yakewa Billy yau wajen kwanan sa nawa rabon sa da ita ko ya ganta ido ne yake hada su in ba haka ba ko kallo wani lokacin bai mata.

"Wallahi Alhaji ba abinda ya hada mu in Billy ce nine ma nake hakuri da ita nan ya dan fada musu hakin da suke ci amman duk da haka Abba yace
"Kai ma babana har da laifin ka, ai bada dau da lallabe yanzu abinda zamuyi zamuje mu basu hakuri."

Alhaji Babba yace
"Hakan za ayi."

Alhaji Karami kuwa da ta tashi ne da ba inda za'a. Abba da Alhaji karami ne sukaje, amman sam Dad ya ki sauraron su yace shi takardar kawai yake bukata. In kuma ba haka ba koto ta raba su, wannan ya kara bata dan Alhaji Karami yace yanzu zai amso masa.

Suna zuwa suka samu Alhaji Babba da Yaa Fauwaz nan Alhaji karami yace
"Sam ba gidan mutunci bane kai Fauwaz ka sakar masa 'yar sa dan yace koto zai kai to menene abin zuwa koto? Dan haka ka sallame ta kawai."

Alhaji Babba yace
"Gaskiya kuwa ayi musu abinda suke so Allah ya kyauta."

Alhaji karami yace
"Saki uku zakai mata dan bana bukatar ko gaba mu kara hada zuri'a dasu."

Jikin Yaa Fauwaz a sabule ya rubuta mata saki uku, dan har yanzu yana jin son matar sa halin ta ne kadai baya so. Dan haka Abba ya dinga masa nasiha na ya dauki kaddarar sa haka Allah ya tsara masa daman.

Alhaji Karami da kan sa yaje ya kai wa mahaifin Billy yace
"Ba sai ka kai koto ba Allah ya kyauta."
Dad ya amsa yayi cikin gida.

Sai hayan magariba ya tafi can gidan sa. Yana shiga yai wanka ya fada kan gado wani bacci mai nauyi ya dauke shi.

Yasmeen kuwa tana gida kewar mijin ta duk ta ishe ta gidan ba dadi dan zama da sukai wannan karon ya kara musu shakuwa da son juna. Da kyar ta tashi ta gyara gidan tayi wanka sannan ta shiga kitchen ta rasa me zata dafa indomie ta dafa amman ta kasa ci sai ruwan tea kadai ta sha ta koma ta kwanta bayan tai masa text din safiya.

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now