*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_3⃣7⃣ - 3⃣8⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Hakika naji dadi da yadda naga kuna nema na a cikin kwana biyun da bana online, duk wanda ya neme ni ana fada min sannan ana nuna min, da wadan da sukai wa Mommy na (Pretty) magana duk na gani. Naji dadi kuma ina godiya Allah ya bar kauna. Wannan shafin nakune masoya wannan labarin _Ni da YaA FAUWAZ_ da wanda na sani da wanda ban sani ba dukka ina godiya wallahi.*
Sati biyu suka dauka suna cin amarcin su, iya hutawa yana samun damar hutawa a gun Billy amman sai yayi da gaske dan sam ita tace ba zai tsufar da ita a wuri ba dan tace yawan sex kan sa mace ta tsufa wanda sai dai ta yadda ayi romancing kadai, shi kuma Fauwaz sam baya gamsuwa da wannan dan yana da yawan feeling, in har ta bar shi sukai sex sai yayi da gaske da lallashi shima da kyar zata yadda.
A haka suka dibi sati biyu wanda a satin biyun nan ya kara karantar halaiyar Billy, wanda sam Billy bata iya girku ko kadan ba ko ruwan tea bata yi dafawa ba bare shara ita daga a dafa mata sai dai taci ta kwanta komai sai dai ai mata wanka kadai take yi da kanta hatta make up masu aikin ta maza su suke mata.
Zaune suke a falo tana sanye da dogon wando da riga yar karama ta kama jikin ta, kanta ta sha fakin sai tashin kamshi take. Yaa Fauwaz ne zaune a gefen ta sanye da three quarter duk farare waya yake da abokin sa.
Bell din dake daki ta danna nan da nan daya daga ciki masu mata aiki suka shigo, In akwai abinda Yaa Fawaz ya tsana bai wuce ya ga Billy ta kira wadan nan mazan ba dan ransa baci yake. Kallon wanda ya shigo tayi tace
"Peeta je ka kira min devid kace yazo ya gyara min kafata farce duk ya tarar min."Nan ya juya da sauri, bai jima ba sai ga Devid din nan rike da dan akwatin kayan gyaran kafar ta nan. Mikewa Yaa Fauwaz yayi yace
"Jeka!"Fuska ta bata tana kallon sa tace
"Yaje fa kace? Zaka gyara min ne?"
Ta tambaya dan indai ta kira masu aikin suyi mata abu yace suje shi yake mata. Kai ya gyada yace
"Jeka!"Devid ya fita yana mamakin mijin Hajiyar su, sam bai son hutu komai in zai mata sai yace aje shi zai yi. Baki ya tabe yace ko duk son ne ohoo.
"Oya come nd start ur job!"
Dan hararar ta yayi ta yi murmushi tace
"Eh mana ai ina jin kai zan dauka kana min aiki yanzu tinda kaine wankin under wear kaine gyara daki yau kuma kai zakai min gyaran kafa! Koma Allah yasa gyaran kafar ma ka iya.""To ban iya ba!"
Ya bata amsa yana komawa ya zauna.
"What?"
Ta fada tana shirin danna bell hadi da fadin
"Shine ka korar min shi?"
Da sauri ya ce
"Da wasa nake kar ki kira shi"Dauke hannun ta tayi daga kan abun tace
"Zo kai min to!"
Kusa da ita ya zauna yana kama hannun ta yace
"Baby na ina son ki gane ba wai aikin ne bana so ai miki ba amman bai kamata ace kina mace maza su zama masu miki hidima ba wannan sam bai dace ba, kar ku manta musulmai ne fa mu, tayaya za ai ace namiji ya taba jikin ki da sunan gyara fata bayan ba muharamin ki bane. Na yadda a samo mace tana miki ai akwai gidajen saloon da gyaran kafa mai zai hana kina zuwa suna miki."Wani kallon raini ta aika masa tace
"Bana son nasu, ba su iya komai ba, su tayiwa mutun sharing kayan su da wasu mutanen! Daman na lura wadan nan yan aikin nawa sun tsone maka ido, ka sani ba kai zaka na biyan su ba Dad da kansa zai biya su, in kaga basa nan sai dai in kai zaka duk abunda suke dan na fada maka tin ba yanzu ba bazan iya bauta ba kuma sai da ka amince dan haka ya rage naka!"
Yadda take maganar cikin zafi yasa yai shiru dan in ya biye mata zata iya kwabewa. Wannan yasa ya janyo ta jikin sa yana shafa ta a hankali cukin sanyin murya yace
"Ban san my Billy da fada ba, daga magana, banyi magana dan na bata miki rai ba. Ina kishin kine kuma zuciya ta bazata iya ganin wasu maza na dawainiyya da ke wajen taba miki jikin ki ba bayan nasan irin ni'imar dake jikin ki..."Katse shi tayi tana fadin
"Kar kasa zargi a zuciyar ka na fada maka tin ina gida su suke min komai acan ban basu kaina ba sai yanzu da nake dakai. Haba Fauwaz gaskiya bana son irin haka kenan ma baka....."Katse ta hima yayi yana fadin
"No ba haka nake nufi ba na yadda dake just ban son suna taban ke suna jin dumin jikin ki. Kisan yadda nake ji ko da taba ki nayi kuwa in har sukaji abinda nake ji ai bazan yafe ba. Yanxu dai ki yi hakuri akwai gun da akewa su Mommy gune mai kyau da tsafta zan na kai ki kuma ba za ana miki sharing da kayan koya ba. Ke zan ma dauki wacce zatana miki duk two week har gida a ware daki a zuba kayan gyaran kai da jikin is dat ok!"Ganin yadda yake lallabata yasa ta sauko, tace
"For now fa?"Murmushi yayi yace
"Kar ki damu zan miki ke in ina gari ma komai ni zan na miki kisan na iya gyaran gashi da jiki saboda princess."Nan ya fara wanke mata kafa sannan ya zauna yana yanke mata farce da kankare su. Da ya gama ta tsaya kallon yadda ya gyara mata kafar tai mata kyau dan duk gyaran da ake mata baya kai wa irin wannan. Nan ta kara jin son sa da tausayin sa. Tace
"Gaskiya Fauwaz yayi kyau. Ni kai zaka na min ma!"Dariyar jin dadi yayi yace
"Kar ki damu in dai ina gari baki da matsala."
Kissing nasa tayi. Suna zaune kokon ta yazo yace ya gama abinci nan ya mike ya dauke ta sukai Dining. serving nasu ya fara tana kallon sa a ranta tana fadin
"Shi baya gajiya dan yanzu ko dakin su na bacci ya hana ana gyarawa. shi zai gyara sanna ya wanke musu under wears din su da kayan bacci. Serving din abinci ma duk shi yake yi. Wanda ita tace baza ta iya ba. baki ta tabe a ranta tace
"Ai ban saka ba. Kai kaga zaka iya!"Nan ya zauna yana bata abincin a baki har ta koshi sannan shima ya fara ci.
Wata su daya da aure, ya fara shirin tafiya dan wani wasa da suke dashi a can kasar England. Abin mamaki sai ga Billy nacewa itama sai ta bishi. Da farko ya dauka wasa take sai da yaga tana hada kaya sannan yace,
"Wai da gaske kike?""Oh da da wasa nake. Ko laifi ne dan nabi miji na?"
kai ya girgiza ya kwantar da murya dan yasan halin ta yanzu zata ce dole sai ta bishin. In bai da gaske ba yasan bashi da yadda zai yi. Amman tayaya zata bishi bayan su ba zaman waje daya suke ba daga can sai can."Baby bai dace matar aure suna zuwa inda muke zuwa ba saboda gun is not safe!"
"What did you mean? Kana so kace da dan ina da aure ba za sake ba. Da nake binka bare yanzu? Kai baka san all what u men can do muma mata zamu iya.""Ba haka nake nufi ba. Yanzu ai tsaya kiji naga hutun ki ya kare na gun aiki shiyasa ma bana son ki bini dan kar kice na hana ki zuwa aikin ki. Nasan Dad ba zai ji dadi ba in kika ajiye aikin ki kina bina wasa kasashe in kin samu lokaci kya na zuwa kina min weekend ko?"
Tinawa da tayi da aikin ta yasa ta ce
"Shikenan amman zanyi missing wasan nan naku!""Don't worry I will do all my best insha Allah! And ga TV nan ko?"
"Yes! Bari naje na shirya zanje gida yanzu!"Ta shige dakin ta. Ajiyar zuciya ya sauke yana fadin
"Billy rigima kenan."Dakin sa ya shiga ya watsa ruwa ya shirya ya fito janye da trollyn sa dakin ta ya nufa bata nan dan haka ya koma falo nan ma bata nan. Wayar sa ya adauka ya fara kiran layin ta hr ta katse bata dauka ba. Kara kira yayi can ta kusan tsinkewa ta dauka tana fadin
"Ya akayi ne Fauwaz?""Na shirya zan tafi naga bakya daki ina kika shiga?"
"Oh sorry na fada maka zani gida ai na tafi!"Cike da mamaki yace
"Amman kinsan zanyi tafiya ya kamata ki tsaya muyi sallama ko?"
"Haba Baby ka fiya rigima sallama ko awaya ai mayi, ina missing din Mum and Dad dats why. Kaga bye safe journey."
Ta fada tana kashe wayar dai dai nan ta danna horn a bakin gate din gidan su.Wayar ya bi da kallo yana mamakin Billy ai dai ta tsaya suyi sallama lallai Billy akwai gyara yaso suyi sallama ya dan yi kissing swt lips dinta duk da ita bata fiya son kiss ba sai tace wai kazanta ne. A haka ya fita ran sa duk a bace.
Yasmeen kuwa bayan biki sai taji gidan duk ba dadi haka ta kare sauran hutun ta na sati biyu ta koma school inda yanzu saura shekara daya su gama karatun nasu. Dan rabi suna asibiti rabi suna makaranta. Sun hadu da Aisha aminiyyar ta a yanzu suka daura daga inda suka tsaya. Addu'a da rokan Allah da Mommy da ita ke yi ya rage mata damuwa dan har ga Allah tana mantawa dashi sai taga sakon kudi da yake turo mata ne take tunawa dashi.
*Hakika mai masoya shi ke da maganin bakin ciki (Inji barrister Sady) Ina alfahari daku masoya na a koda yaushe da wanda na sani da wanda ban sani ba. Allah ya bar kauna.*
YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.