DR. SRY. 01-02

34 1 0
                                    

♦️♥️♦️
           *DOCTOR SURAYYA*
                 ♥️♦️♥️

Na.Nasbat Gwandu.
(auntyn twins)

Page 01-02

✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶🖊
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶🖊,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶

Page 01-02

Bismillahir rahmanir rahim...

"Hmmmm!!!  nifa Surayya Allah mamaki kike bani wadda keda burin zama doctor amma sai dan banzan tara samari, nidai anawa tunanin is better ki kama kanki ki daina tara samarinnan please!" cewar Fateema suna zaune under tree da alama an tashi daga school ne suna jiran azo daukarsu.

Murmushi kawai Surayya tayi cikin rashin damuwa tace "firstly dai kafin nace komai inaso nayi correcting dinki mah name is *DOCTOR SURAYYA*  not Surayya please ki kiyaye kinji better half?, secondly kuma nagaya miki samarinnan bawanda na nema nace ina sonsa so basu dameni ba and daga na kammala ss3 dinnan duk sallamarsu zanyi cous karatun da nakeda burin yi bana wasa bane!.

"Tabbb lallai ke baki ma tsoron kijama kanki wani abu, idan kin cuci wani ya kyale wallah wani bazaki ji dadi ba please ni wannan kawai nakeso kibari Saleem da alamu da gaske yake, nifa Christian dinnna da kike tare dashi sam bai kwamta min ba please! "

"Lallai Fateema ni kowa bazan bari ba kinsan halin Abbanah yanzu haka dargar da muke dashi kenan, shi fa wai daga na kammala ssce aure zanyi ni kuma gaskiya bazan lamunci hakan ba so tun yanzu zan rabu da kowa idan ba miji ai dole a barni na sarara!"

"Please Dr Surayya kada ki tafka kuskuren da daga baya zaki dawo dana sani,  meye aciki idan kinyi aure kin cigaba da karatun ki kada ki ki cikawa Abba burinsa don Allah ki bari ayi duk yadda mahaifanki ke so"

"Fateema kenan ai ni bazan ce ban amince da burin su ko umarnin su ba, amma a kullum inaji a jikina da duk yadda sukaso aurar dani idan ban cika burina auren bazai yiwuwa ba,  haka kullum cikin rokon Allah nake akan duk yadda akaso aurar dani Allah ya  kawo wani dalili da zaa fasa auren har sai na cika burina!"

"Surayya da hankalinki kuwa? kada ki aikata abinda daga baya zaki dawo dana sani wallahi, kina ganin hakan da kika zabar ma kanki shine best solution ko?  Good nidai a kullum bazan daina baki shawara ba har sai ranar da nabar numfashi, sboda haka ni zan wuce bakin titi idan nasamu napep nawuce bye"

"owk bara na taso na rakaki" tafda tana mikewa itama tsaye wayar ta dauka tayi dialling din number Saleem.

"HI Saleem ka zo ka daukeni a skull kayi dropping dina gida yanzu idan kayi delay kuma bazaka tarar dani ba" dif ta kashe wayar tana murmushin da bangane nufinsa ba.

Fateema da ba yau ta saba ganin yadda Surayya ke nuna ma samarin ta izza ba,taso ta kyaleta tayi shiru amma kuma ta kasa tace "Dr Surayya kenan inama ace nice nakeda wanda yake so nah kamar Saleem da zakisha mamaki don sai na nuna masa kulawa sosai, kina wasa da damarki ne wallah better half! "

Surayya dake tafiya kamar bata son taka kasa ko kallonta batayi ba, sai da suka isa bakin titi har Fateema ta fidda ran samun answer dinta cikin ko in kula tace "Fateema zaki iya samun Saleem ko yanzu don ni ban taba jin soyayyar sa a raina ba wallahi ba,  so idan mun rabu zan basa shawarar ya nemeki Kin mafi dacewa dashi don behaviors dinku kusan daya,  so insha Allah har wanda yafi Saleem zaki samu"

Saurin kallon ta fateema tayi cikin mamaki tace "amma bakimin adalci ba idan kikayi tunanin ina son Saleem, Saleem naki ne kuma har gobe bazan daina baki shawarar da ta dace ba, ko Saleem ne kadai namiji bazan aure sa saboda dake ya dace ba dani ba!"

Keke napep ta tsaida tace mata "bye sai munyi waya "

"Bye"

Tsaye take bakin gate din makarantar time to time take jan tsaki duba wayarta tayi taga kusan 15mins da kiran Saleem bai zo ba, dialling din number din Samuel tayi shima cikin izza tace "Samuel ina school kazo kayi dropping dina gida yanzu am waiting for you kada kayi wasting din time dina! " dif ta kashe wayar ta, gama wayar ta keda wuya sai ga motar Saleem yayi parking gabanta yana mata horn, ko kallon motar batayi ba sai ma latsar wayar ta da ta cigaba dayi, ganin hakan yasa Saleem fitowa daga motar ya nufeta.

Tubarkallah Masha Allah shine abinda na furta lokacin da nayi tozali da kyakkyawar fuskar Saleem, kyakkyawa ne sosai fari tass sai dai shi ba dogo ne ba don tsawon su zaiyi daya da Surayya, cikin kulawa yace "please Dr Sury am terribly sorry koda kika kirani ina office aiki yamin yawa sai da na nemi Suleiman kafin na baro office din am sorry please forgive me!" ya ida cikin sigar tausayi da lallashi.

"owk" kawai ta furta amma fuskar ta ba alamar dariya.

Cikin lallami yace "idan kinyi hakuri doctor please smile smile please "

Murmushi tayi sannan cikin sauri tace "let's go please Mama na jirana a gida "

Da kansa ya bude mata gambu ta shiga sannan ya koma yafara driving.

"Masha Allah yanzu kinga saura few month's mu kammala ssce dinmu, sai mu fara neman wace skull zamu cigaba don mu cika burin mu ko!? "

Surayya murmushin yake tayi ta rasa wani irin so Saleem yake mata a hankali tace "uhm kasan burina yana gaba da komai a rayuwa ta idan har ina raye insha Allah zan cika wannan favourite buri nawa "

"amma Dr ya kamata ko engagement ne muyi idan mun kammala ssce ni zan jiraki zuwa ko yaushe amma please ki bari a manaa engage"

Nan da nan duk annurin da ke bisa fuskar ta ya bace cikin fushi tace "idan har dagaske Kana sonah van aminta asan da wanna maganar ba gidan mu!"

Baiyi mamaki ba don da duk ya dauko maganar wataran sai suyi sati suna fada cikin damuwa yace "but why!?"

"bazan lamunci duk abinda zai min katanga da cika burina ba!" incoming call ne yashigo wayarta dai dai Sun iso inda yasaba ajiye ta, a hankali ta furta "thanks You"tare da receiving Samuel baiji me ta ce ba amma tabbas kunnen sa Sun jiyo masa Samuel.

Aza kansa yayi bisa steering motor runtse idanun sa yayi zuciyar sa na masa azabar radadi,  sosai yake kishin Surayya amma ita bata maida receiving calls din bf dinta gabansa a bakin komai ba, duk yadda yaso rabuwa da ita yakasa sabida son ta da yake,  yanzu haka babansa ya tasasa gaba maganar aure ya rasa yadda zaiyi wadda yakeso kula samari ne kawai aikin ta, bude idanunsa yayi wadanda suka zama red color sai da ma ya tsoratani a hankali cikin tausayin kansa yace "Ya Allah! Idan Surayya ba rabona bace Allah ka fidda min sonta dake azabatar dani! " a 360 yabar shiyar.

Har ta isa gida waya take da Samuel suna ta Case din yaje makaranta batanan, ganin maganar bazata kareba yasata hanging din call din missed calls din Ahmad da bashar tagani tsaki taja tasa wayar flight mode sannan tayi sallama cikin gida.

Mama dake zaune tana gyaran kifi ta amsa da "waalaikissa salam yar albarka meya tsaidaki yau hala? "

Cikin kwarewa da karya tace................................

Toh fa labarin *DOCTOR SURAYYA* YANZU AKA FARA YA KUKA GANI FAN'S IDAN NAGA COMMENTS ZAN CIGABA IDAN BABU ZAN AJIYE RUBUTUN KO BANZA TYPING DAN BANZAN WAHALA NE DASHI.

ANTYN TWINS 😍😘

DOCTOR SURAYYA Where stories live. Discover now