DR. SRY. 23-24

18 0 0
                                    

♦️♥️♦️
           DOCTOR SURAYYA
                 ♥️♦️♥️

Na.Nasbat Gwandu.
(auntyn twins)

Follow me on wattpad @nasbatgwandu01

Page 23-24

✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶🖊
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶ ✍ ,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶ 🖊 ,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.

INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?

NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna LIKE a shafin mu na Facebook. 👇

https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu.

DEDICATED TO MOM AND DAD 😍 ♥.

        Page 23-24.

*OMAR FAROUK SPECIALIST HOSPITAL*

hospital d'in daga ganin ta babbar hospital ce, tana da tsari sosai da sosai daman tanada file a hospital d'in bata wani jimaba aka duba ta,  medicines kawai aka mata prescribing, basu wani dad'e ba suka wuce amenity duba Naseer, sun tarar da jikin sa da sauk'i sosai sun jima ba sosai sannan suka tafi.

Zaune take tana shan fura mai sanyi wadda Mama ta dama mata don tasha magani,  tasan halin Surayya da batasham magani sai da koko ko fura, ba laifi ta d'an sha furar sannan tasha medicines d'in, sai da ta gyara wurin sannan ta samu ta d'an kwanta tunani fal ranta.

Maganar Mama da Suleiman ne ke dawo mata, da duk ta tuna da magaanar wani irin bak'in ciki da b'acin rai ke lullub'eta, zuciyar ta har zafi take mata,  a hankali hawaye suka fara silalowa gefem kumatun ta,  sa hannun ta tayi ta share hawayen, so take ta manta da maganar don ta samar wa kanta salama, amma hakan ya faskara, tana wannan tunanin incoming call ya shigo wayar ta,  better half ne ke yawo bisa screen d'in wayar, a hankali ta yi receiving din call d'in tare da sallama.

Fateema dake kwance bisa bed din ta jin muryar Surayya sai da hankalin ta ya tashi, saboda tayi low sosai saurin tashi xaune tayi cikin damuwa ta ce "Besty meke damunki please naji voice dinki very low kamar wadda tayi kuka!?"

Lumshe idanun ta Surayya tayi a hankali ta ce "Nothing fa kada ki tada hankalin ki mura kawai ke damuna,  dats oll kuma daga bacci natashi! ".

Sauke ajiyar zuciya tayi sannan ta ce "Wai thank God!!!  Betterhalf yakamata ki shigo yau kince zaki shigo amma shiru,  tunda mukayi maganar akwai magana ki shigo please! ".

"No Fateema kidai shigo banjin zan samu damar fita ko'ina yau please! ".

"Hmmm haba Doctor kindai san nafad'a miki mama tace bazata sake bari na fita idan ba dole ba, shine kuma zaki ce nazo bazaki zo ba?  Bayan kinsan anfara preparations din aurena! ".

Shiru tayi tasan batada gaskiya amma cikin lallashi ta ce "So sorry betterhalf insha Allah idan nasami dama zan shigo ".

"Nasan dai Mama bazata hana miki zuwa ba don haka, please kizo kafin asr prayer hakan nakeso! "

Dafe kanta tayi ta gaji da argument d'in da suke, hakan yasa cikin gajiya "Owk insha Allah idan nasamu yadda nake so xanzo, amma ban miki alk'awari ba! ".

"Owk nidai am waiting for u sai kinzo"

"Owkay bye "

"Bye"

Hanging din call d'in tayi  ta kwanta tana dafe kanta a hankali can k'asan mak'oshin ta ta furta "Ya Allah!!! ".

Incoming call d'in Suleiman ne ya shigo wayar ta, tsaki taja kamar yana gabanta tare da galla ma wayar harara, rejecting d'in call d'in tayi ta sakashi a black list,tana kammala haka incoming call d'in Zaainab ya shigo wayarta, answering tayi tare da sallama tundaga voice d'in Zainab tagane ba lafiya ba,  cikin damuwa ta ce "Am on my way! ".

Hijab d'in ta kawai ta zura sai wayarta da ta d'auka a hanzarce tabar d'akin, wurin Mama ta nufa ta tarar da ita tana yanke ma su Kabeer farce, cikin girmamawa ta ce "Mama sannu da aiki Zainab na nemana zanje na dubo lafiya! ".

Cikin kulawa Mamar ta kalleta ta ce "Keda bakyada lafiya ina zaki iya zuwa kuma? Kibari na aika Aysha muji lafiya".

"No Mama naji dama kibarni naje daga jin voice d'inta akwai matsala wallahi".

"Tau ba matsala Allah yasa lafiya muji alkhairi, ki hanzarta ki dawo dai ".

"Owkay insha Allah sai na dawo " tafad'a tana barin gidan.

Da d'an saurin ta ta isa gidan sallama take amma ba ansa,  hakan yasa kaitsaye ta nufi cikin d'akin ta tarar da Zainab kwance lullube da blanket, cikin sauri ta nufi inda take sosai jikinta yayi zafi,  cikin damuwa ta ce "Sannu Zainab meke damunki nd ina Taheer dabai kaiki hospital ba!".

Rik'o hannun ta tayi cikin zafin ciwo ta ce "Surayya malaria ce daman tunda nasamu cikin nan yazomim haka".

"Ina Taheer tou!?".

"Baisan banda lafiya ba banason tada masa hankali shima bawata isassar lafiyar garesa ba, so please am hungry ki sama mun abunda zanci!".

"Owkay ba matsala me zaki iya ci dimple namiki, zakici indomi? ".

"No kidai samamin koko daga nan nasha magana".

"Owkay insha Allah! ".

Haka ta dama mata kunu tasha ta taimaka mata ta had'a mata ruwan wanka tayi, sai do ta share mata gidan tasss duk da baida ma datti, Jallof rice mai sauk'i ta aza mata sai da tayi sallar zuhr sannan ta ida,  Bata ci ba ta ce ma Zainab zata tafi Allah sauwaka, godiya Zainab tamata Sosai sannan ta wuce.

Sauri take kada ta had'u da Taheer tasan lokacin dawowar sa kenan, fitowar ta kenan motarsa ta Parker, kallon da dai ta tsana yau ma shine yake binta dashi bata ma kallesa ba balle tayi ta kansa a hankali ta ce "Ahir d'inka da kallon matar wani wanin ma mai rabo! ".

Sai da tayi sallahr Asr taci abinci taso zuwa gidansu Fateema, Mama tace taa huta tabari har gobe.

*SALEEM*

Kwance yake idanunsa a lumshe yayi hugging d'in pillow, earpiece ne sanye a ears d'insa da alamu wyaa yake sai wani blushing yake,  cikin tsananin kulawa ya ce "Babyna saura k'iris fa! "

Fateema dake zaune bisa stool ta mirror, murmushi kawai tayi ta ce "Ina Ummanah tana lafiya!? ".

Lumshe idanunsa yayi yanajin dad'in yadda take yawan tambayar lafiyar parents d'insa, ya ce "Lafiya qlw alhmddlh, and kuma nidai ina son naganki tunda yanzu ganinki sai an yanka ticket".

Dariya tayi mai sauti ta ce 'Ganina kam sai bayan 3weeks, lokacin munzama thesame! ".

B'ata fuska yayi kamar wani k'aramun yaro cikin voice d'in tausayi ya ce "Nop Teemanah sai idan so kike akai amarya ba ango ciwon missing din beauty face din princess din sa ya kasheshi,  kuma ko yanzu ai muzama abu d'aya ".

Murmushi tayi jin Umma na kiranta yasa a hankalo ta ce "Will talk later Umma na nemana! ".

"Owkay swthrt take care bye ".

Toilet yafada yayi taking shower...............

Comment
Share
Vote

Antyn twins 😍

DOCTOR SURAYYA Where stories live. Discover now