DR.SRY 05-06

7 0 0
                                    

♦️♥️♦️
           *DOCTOR SURAYYA*
                 ♥️♦️♥️

Na.Nasbat Gwandu.
(auntyn twins)

Follow me on wattpad @nasbatgwandu01

Page 05-06

✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶🖊
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶🖊,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶

DEDICATED TO GOLDEN PEN WRITERS BANDA KAMARKU.

Page 05-06

*READER'S SO SORRY WALLAHI WAYANA YA FADI SOSAI TA FASHE KEYBOARDS DINA SUNA BANI MATSALA SOSAI ZAKU DINGA JINA TIME TO TIME KAFIN A GYARA*

Bismillahir rahmanir rahim...

"Assalamu alaiki Mrs Saleem!".

A hankali ta ce "wa'alaikas salam".

Gyara kwanciyarsa yayi bisa bed  tare da cewa "kintashi lafiya Doctor? ya su mama da Aisha?".

yatsine fuskar ta tayi sannan cikin son tak'aita maganar tasa ta ce "komai alhmdllh daman so nake kazo ka kaini gidan su Fateema, zan shirya zuwa 3pm".

Daman ko bai fada ba yasan ba,a banza ta nemesa ba cikin dan damuwa ya ce "ba matsala insha Allah daga nazo zan kiraki sai na kaiki".

"owk sai kazo bye" bata jira amsawar sa ba tayi hanging call din.

Wullar da wayar yayi gefe zuciyar sa na tafasa da abinda Surayya ta masa, duk da tasaba amma shikam kullum abin k'ara b'ata masa rai yake, yakamata ace yasaba da irin wannan amma sam yakasa sabawa, a hankali cikin tausayin kansa ya ce "sai yaushe ne Surayya zata soni kamar yadda nake masifar sonta, anya zuciya ta kinmin adalci kuwa?!".

Cikin sanyin jiki ya tashi yayi taking shower din sa, ya shiryawar sa tsaf cikin shaddar sa white colour daman white shine favourite colour dinsa, sosai yayi kyau wrist watch dinsa ya dauka sannan ya tsaya ya kalli kansa a mirrow, ya rasa menene ya rasa da Surayya ke wulakanta sa tana masa yadda ta ga dama, bai bari wannan tunanin yayi tasiri a zuciyar sa ya dauki car keys dinsa, bai zarce ko 'inaba sai gidansu.

Parking yayi a parking space gidan tubarkalla dai dai gwargwardo, gaisawa yayi da gateman sannan ya nufi cikin gidan da sallama dauke a bakin sa, Umma dake zaune tana zubawa Abba koko a kofi ta amsa, shima Abby amsawa yayi yana dan tamk'e fuskar sa.

Zama yayi saman center carpet din parlourn tare da dan russuna wa cikin girmamawa ya ce " Abba Umma ina kwanan ku dafan nasame ku lafiya? "

A tare suka amsa da "lafiya qlw"

Umma kallon sa tayi tana murmushi ta ce "Babana na zuba maka koko da kosai ko? "

Gyada mata kai kawai yayi tare da kawar da kansa saboda hararar da Abba ya banka masa,  cikin dan zafi Abba ya ce "ai Kulu ki maida hankali kina ciyar da wannan tuzurun wadda yanzu yakamata ace ya ajiye miki yan jikoki! "

Sadda kansa yayi cikin muryar tausayi ya ce "Abba ka kara hakuri dani Insha Allah very soon komai zai wuce "

Umma ma tana miko masa kokon da kosan ta ce cikin lallashi "Abban Muhammad insha Allah indai aurene very soon zamuyi shi mu huta da gori "

DOCTOR SURAYYA Where stories live. Discover now