DR.SRY.09-10

8 1 0
                                    

♦️♥️♦️
           *DOCTOR SURAYYA*
                 ♥️♦️♥️

Na.Nasbat Gwandu.
(auntyn twins)

Follow me on wattpad @nasbatgwandu01

Page 09-10

✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶🖊
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶🖊,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶

DEDICATED TO YAR UBANAH😂😘 SURAYYAH OMG!!!  AM MADLY IN LOVE WITH THIS SOUL💕😘😍💓

09-10

Bismillahir rahmanir rahim...

"Haba better half baki fahimce mu bane amma ai tunda mu muka so wannan abin bakomai bane fah, please kiyi accepting din Saleem ni wallahi bana ra'ayin sa, idan kin lura ko dacewa ba muyi ba, behaviors dinmu sunsha bambam sosai da sosai don Allah kada kimin butulci ki watsa min k'asa a ido please!".

Ko kallon ta Fateema batayi ba sai ma k'okarin ninke prayer mat da take, sai da ta ajiye komai inda ya dace har hijab din sannan ta dawo wurin Surayya ta zauna, cikin rauni ta ce "Surayya don Allah na tambeki and kimin alk'awarin zaki bani answer dai-dai please!".

Surayya wadda zuwa yanzu ta cire hope d'in Teema zatayi accepting, ta kalli Teema wadda idanunta har sun zama red tsabar b'acin rai, a hankali ta ce "Allah yasa nasani idan nasani na miki alk'awarin zan baki answer dinki correct".

"Amma zama na dake kina zargin ina son Saleem ko?!".

Saurin kallon ta Surayya tayi fuskar ta d'auke da tsan-tsan mamaki ta ce "Wallahi wallahi wallah Fateema ban tab'a wannan tunanin ba balle har na zarge ki,  Fateema ni yanzu a matsayin y'ar uwata nake kallonki ba friend ba kinfi k'arfin friend a wurina!".

"Owk zan baki shawara a matsayi na na y'ar uwarki, Surayya me kika d'auki kanki ne? me kike son maida kanki ne? akan wani banzan buri naki kinaso ki bijerewa iyayenki Surayya? ina hankalin ki da natsuwar ki da tambiyar da aka baki? don Allah kada ki bari wannan dama taki ta kubce miki wallah Saleem namiji ne wanda ko wace mace zatayi kwad'ayin samu a matsayin mijinta, don Allah ki amince a muku engagement da Saleem!"

Surayya shiru tayi sannan ta aza hannun ta bisa laps din Fateema cikin raunin murya ta ce "Fateema ki yarda dani burina na gaba da komai a rayuwa ta, nima idan nasan yadda zan cire wannan buri nawa da nayi amma wallahi bazan iya ba, amma wallahi har yanzu ban tab'a jin son wani a raina ba, banson Saleem Fateema kuma kinfini dacewa dashi, ki k'ok'arta ki amince masa don Allah! "

Fateema kallon Surayya kawai take yanzu ta daina bata mamaki tsoro take bata ta ce "Saleem ke yake so Surayya ba Fateema ba!"

"Nasan Saleem na sona amma shi da kansa ya gayamin kema yana sonki, idan ma ni yakeso wallahi nasan daga Kin amince masa komai zai daidaita don Saleem d'an soyayya ne, kema hakan kinga taku tazo d'aya kenan! "

"Surayya bazan ci amanar ki ba ki sake tunani pls mubar maganar nan!"

Kamo hannayen ta Surayya tayi cikin alamar tausayi ta ce "Baki amana ta ba wallahi, ki tausaya wa Saleem yana buk'atarki a rayuwar sa pls!"

DOCTOR SURAYYA Kde žijí příběhy. Začni objevovat