DR. SRY 07-08

8 1 0
                                    

♦️♥️♦️
           *DOCTOR SURAYYA*
                 ♥️♦️♥️

Na.Nasbat Gwandu.
(auntyn twins)

Follow me on wattpad @nasbatgwandu01

Page 07-08

✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶🖊
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶🖊,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶

DEDICATED TO OMAR FAROUK.
ND ABAKAR SADEEK.

07-08

Bismillahir rahmanir rahim...

Mamaki ne k'arara ya bayyana bisa fuskar Saleem, ransa ya b'aci sosai amma dole yayi accepting d'in wannan offer idan har yanason fitar da ita daga rayuwar sa, tunda ya gano cewa sam ba d'igon sonsa a cikin zuciyar ta.

Surayya ganin shirun yayi yawane yasata cewa "Owk ba damuwa zan baka time amma wallahi Fateema batada matsala sam kuna kun dace, idan ka shirya amsar offer ta zaka iya gaya min".

Murmushin k'arfin hali yayi cikin son k'ara ma kansa k'arfin guiwa ya ce "No bana buk'atar wani time nayi accepting din offer dinki!".

Murmushi sosai ya bayyana bisa fuskar Surayya cikin tsananin farin ciki ta ce "Wowww thanks alot and ni nasan zakaji dad'in wannan abin Insha Allah! ".

Murmushi yayi ya ce "Naga alama ai don Fateema inda da ita nafara had'uwa da bazan nemeki ba!".

Maganar ta doke ta sosai cikin b'acin rai ta ce "Mekake nufi kalmar nan taka Saleem! ".

Y'ar dariya yayi daman ya fad'a ne don taji haushi cikin ko in kula ya ce "Laaa kada fa ki maida maganar tawa wani abu, ba abinda Saleem ke nufi nidai ina buk'atar ganin princess dina kafin na wuce, please a taimaka min a sallamomin ita".

Maganar tasa haushi ta bata fuska a dan had'e ta ce "Owkay!".

Fita daga molar tayi har yanzu tana juya maganar cikin brain dinta, k'ok'arin ture wannan tunanin tayi sannan ta nufi cikin gidan, ta tarar dasu parlour sun baje ana fira da sallamar ta ta shiga d'akin, su duka biyu suka amsa cikin farin ciki Humaira ta ce "Lale marhaba Allah dai ya k'addari zan ganki gidana!"

Dariya tayi ta ce "yau dai gani na huta da bambami ko? "

Humaira ta ce "Lallai kam zauna mana ko? "

"Ai bak'uwa nike ba idan natashi zama zaman nake " ta kalli Fateema dake latsar waya ta ce "Uhm Better half Saleem na nemanki and please promise me duk abinda ya ce zaki amince"

Kallon bangane ba ta mata cikin mamaki ta ce "Doctor kinsani a duhu yaya zakice namiki alk'awarin abinda bansani ba? no nikam a'a nd kiran mi Saleem kemin?"

'Bata fuska Surayya tayi cikin jin haushi maganar ta ta ce "kinsan dai bazan cutar da ke ba ko?  please kimin wannan alfarmar kuma fa yana jiranki yanzu! "

Tashi tayi tana yafa veil dinta ta ce "Allah yasa zan iya miki wannan alfarmar " tafada tana fita.

Surayya ganin ta futa ta zauna ta kalli Humaira ta ce "Amarya bakya laifi ananan anata amarci ko! ?".

"Bara dai nakawo miki ruwa kada na cikaki da surutu?".

Nufar motar tayi bata kawo komai a ranta ba, knocking din glass din motar tayi sauke glass din yayi murmushi shinfid'e bisa kyakyawar fuskar sa, a hankali ta ce "Ance kana nemana! ".

"Hakane kam amma Malama Fateema kimin uzuri ki shigo motar mana, important magana ce please".

Cikin mamaki ta ce "Owk ".

Bud'e mata gambun yayi ta shiga ta zauna ta rufe.

Watsa mata idanunsa yayi yana kallon ta yana fatan Allah yasa ta amince masa, don gaskiya yarinyar ba laifi barakallah Masha Allah Surayya fari da k'iba kawai zata nuna mata.

Takura tayi da kallon da yake mata kuma baice komai ba cikin takura tace "Ina sauraron ka!"

Gyara muryarsa yayi sannan a hankali ya ce "Fateema!Fateema!!Fateema!!!".

"Na'am"

"Nasan kinsan yadda nakeson friend d'inki amma tana wulak'antani tana min yadda taga dama right?"

"Hakane amma ka k'ara hak'uri da ita pls soon komai zai wuce "

Murmushi yayi ya ce "Wannan babu ita yanzu tsakani da ita,  bcoz  komai namu ya banbanta Fateema yakamata ace inada iyalina yanzu , so bazan iya jiran k'awarki ba shiyassa nakawo kaina gareki kuma ina fatan ki sharemin hawaye na, kada kimin yadda Surayya tamin".

Da sauri ta kallesa zuciyar ta na bugawa da sauri - sauri cikin kid'imewa ta ce "Ban fahimceka ba!? ".

"I mean ina sonki Fateema please ki taimaki wannan bawon Allahn kada ki tuna cewa ni saurayin best friend d'inki ce, ko kuma kin yaudare ta No ita da kanta ta hada wannan abun kuma banga matsalar hakan ba tunda bata sona!!!".

Watsa masa idanun ta cikin mamaki ta ce "Amma wallahi kun bani mamaki Saleem to insha Allah koda maza sun k'are bazan auri wanda nake fatan yazama mijin Surayya ba, har ina farin cikin ta sameka nasan zaka canzata sosai Saleem amma wallahi nayi mamaki, kama bar furta min kalmar so don inajin kamar naci amanar friendship ne pls! ".

Baiyi mamaki ba daman yasan za'ayi haka cikin marairaicewa ya ce "Fateema da zakimin adalci kinsan nasa Surayya amma tagayamin bata sona, kuma nifa namiji nakai lokacin da nake bukatar mace a rayuwa ta, burin Surayya har how many year's kike tunani zatayi? zan baki time kiyi tunani amma nida ina sonki kuma bazan daina sonki ba sai idan kema Kim wulakantani! ".

Shuru tayi tama rasa abin ce masa sai can ta ce "Surayya cewa kawai take sai ta cika burin ta amma gidansu bazaa bari ba zanyi magana da ita!" ta fada tana kokarin bude motar ta fita.

Ganin hakan yasa Saleem saurin sa motar lock cikin muryar tausayi ya ce "Yanzu ba Surayya nakeso ba Teema nakeso, don haka kada ma ki wahalda kanki don ni Saleem Muhammad Abdallah nabar Surayya Insha Allah! ".

"Ka budemin mota na fita! "

"Owk Ma'am adai tuna da Saleem pls saboda kece rayuwar sa a yanzu "

Kulle kunnuwanta tayi cikin dan daga murya ta ce "ka budemin kofa nafi ta! "

B'ude kofar yayi ta fita cikin fushi tayi cikin gidan.

Iskar bakinsa ya furzar cikin damuwa ya ce "Ya Allah!!! kasa wannan yarinyar ta amince min nidai wallahi ta min! " tada motar yayi yabar unguwar.

Tana shiga gidan bata kalli kowansu ba ta dauki handbag dinta, Humaira ganin mood dinta ta ce "Aah Fateema ina zuwa? lafiya? ".

"Zan wuce gida wataran nadawo!".

Surayya na mata magana amma ko ta kanta bata bi ba, ganin hakan yasata ajiye drink's dinda take sha, sallama tama Humaira cikin sauri tabi bayan Fateema, har ta samu keke napep bakin gidan koda ta fito, do sauri ta isa itama tashiga.

Cikin damuwa tace "Fateema please try to........... ".

Shhhhhhh Fateema ta katseta "bana bukatar jin komai thanks for everything".

Bata sake cewa komai ba har suka isa gidansu Fateema.

Sai da ta gaida Umma sannan tabi bayna Fateema ta tarar da ita ta fito daga alwalla kenan, itama alwalla tayi suka yi sallah.

Cikin damuwa Surayya ta dubs Fateema ta ce......

Comment.
Vote.
nd share.

ANTYN TWINS 😘

DOCTOR SURAYYA Where stories live. Discover now