DR. SRY 15-16

6 1 0
                                    

♦️♥️♦️
           *DOCTOR SURAYYA*
                 ♥️♦️♥️

Na.Nasbat Gwandu.
(auntyn twins)

Follow me on wattpad @nasbatgwandu01

Page 15-16

✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶🖊
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶🖊,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶

Surayya (Y'ar uwa), Faeza(besty), Najaatu (Najeesh), Inaya(Yar Sanyi😂), Aisha (Ummi tafarki).
Bazan taba mantawa daku ba da soyayyarku a gareni inayinku Over wallahi.

PAGE 15-16
Bismillahir rahmanir rahim.

Tana kammala wayar ta ajiye ta bisa bed, murmushi ne kawai ya kufce mata tana tunanin inda da ne ta isa ta ajiye waya har yanzu ba'a fara damunta ba,  cikin rashin damuwa ta ce:

"Haba ina dalili a zauna zaman damunka wallahi rayuwa haka tafi komai dadi ba takura".

(Nidai na kalleta na ce "Atoh kanki akeji dai yanzu daman tarkacen samarinnan ganewa ne kawai bakuyi amma ba wani fa'ida sai ma rashin kwanciyar hankali".)

Tashi tayi ganin zaman dakin ba abinda zatayi bayan tunani,  wayarta ta dauka ta dubi time 5:12 tagani hijab dinta ta dauka ta bar dakin, ta tarar da Aisha da Kabeer suna wasa tsakar gida ko kallonsu batayi ba ta nufi dakin Mamanta, gyaran wardrobe ta tarar tanayi cikin damuwa ta ce "Mama sannu da aiki ya jikinki? ".

Kallonta Mamar tayi ta ce "Jiki alhamdulillah y'ar albarka, ina zuwa haka naganki da hijab? ".

"Mama naso naje wurin Zainab ne amma nafasa ki kawai na ida miki gyaran, indama aikawa kikayi aka kirani namiki bakifa da lafiya don Allah kidinga hutawa! ".

"Is owk Surayya am feeling better daman kinsan ciwon namu time to time, so yanzu normal nakejin kaina and ki wuce wurin ziyarar ki please idan akan wannan aikin me saura kadan na karasa ".

"Owk Mamanah Allah kara sauki bara nayi sauri na dawo ".

"Uhm ki gaidamin da Zainab din kinji tunda yanzu itama tafara zama irinki tabar kawomin ziyara".

"Tau zataji insha Allah sai na dawo".

Tafiya take a hankali kamar mai tausayin kasa kasancewar gidan ba nisa layinsu ma daya, bata dade ba ta iso gidan da sallama ta shiga gidan, ta tarar da Zainab har tasa hijab  tana batun sa takalmin ta har ta kulle dakinta.

Cikin mamaki Zainab ta ce "Wa'alaikis salam lale marhabin shin dagaske Surayya ce nake gani ko kuma gizo idanuna kemin? ".

Dariya tayi ta ce "A'ah fita zakiyi ne kuma gashi kinyi bakuwa sai a budemun daki ko?"

"Abu dole daki ai nakune daman wurin Mama naso zuwa na gaidata nasan nayi laifi wallah,tun ba yau ba naketa niyyar zuwa wallahi lafiyar ce yanzu sai a hankali yau ciwo gobe lafiya ".

Da sallama ta shiga dakin fes dashi tsaf tana yaba tsaftar Zainab "Allah sarki kodai mun samu karuwa ne haka ba labari? ".

Murmushi Zainab tayi ta ce "Ke dai nayi mutumenki sob'o ki tashi ki dauko kisha nasan bakida labari shiyasa ziyarar ma an manta dani tunda nabar yin mutumenki".

DOCTOR SURAYYA Donde viven las historias. Descúbrelo ahora