DR. SRY 13-14

9 1 0
                                    

♦️♥️♦️
           *DOCTOR SURAYYA*
                 ♥️♦️♥️

Na.Nasbat Gwandu.
(auntyn twins)

Follow me on wattpad @nasbatgwandu01

Page 13-14

✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶🖊
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶🖊,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶

DEDICATED TO HAFSAT KAOJE LOVELY GWAGGO.

PAGE 13-14

Bismillahir rahmanir rahim...

Tafiya suke kowannen su rike da papers alamun questions paper's ne a hannunsu da calculator cikin gajiya Fateema ta ce "Allah mathematics dinnan tayi wuya ba kamar waec ba kinsan waec uncle Usman ya taimaka na sosai, kuma luckily baa turo mana external invigilator ba sai da muka kusan kammalawa sannan yazo!".

Kamar da dutse take magana saurin kallon Surayya tayi wadda da alamu hankalin ta baya kanta tafiya kawai take, sake kallon ta tayi ta na tausaya rayuwarta ganin duk tabi ta rame kamar ba Dr Surayya ba, cikin damuwa ta dafi kafadarta Jan hannun ta tayi suka samu under tre suka zauna cikin rauni ta ce " Surayya wai sai yaushe zaki daina wahalar da kanki ne!?, engagement ne anriga anyi kusan 2weeks kenan har ma anfara maganar fixing din date din aure tunda saura mana 3weeks muyi graduating, don Allah ki daina sa ma ranki abinda kikasan ba fashi, kinga yadda kika zama kuwa!?".

Surayya kallon ta tayi hawaye fal idanunta cikin damuwa da rauni ta ce " Fateema Suleiman nefa aka mana engagement dashi, bana sonsa ko cikin boyfriend's dina shine Wanda nafi tsana sam bama shiri!'.

Girgiza mata kai tayi alamun kada tabari hawayem ta su zuba, riko hannun ta tayi a hankali ta ce "Surayya nasan da haka amma aishi yana sonki, ki barwa Allah zabi ki dage da addu'a wata bata auren mijin wata kamar yadda wani auren matar wani, kedai ki bar komai ki dage da adduar idan aurenku alkhairi ne Allah nuna mana rana!".

Cikin jin takaicin kalaman Fateema ta ce cikin zafi " Haba Fateema kamar wadda batasona ni wallahi inaji a jikina mijina baya kusa har yanzu Allah bai hadani dashi ba, kuma Suleiman ni nasan insha Allah Allah zai kawo abinda zai dakatar da wannan auren, don ba damuwa kawai nakeba kullum dare da rana cikin rokon Allah nike, akan kada wannan auren yayi kuma inaji ajikina bazaiyi ba!".

Fateema shuru tayi tana kallon kawarta wato mai hali bai canza halinsa, a hankali ta ce " Kada kiyi kuskure kidai nemi Allah  zaba mana mafi alkhairi zaifi!".

Surayya kokarin kauda maganar tayi ta ce " Hmmm Allah mai iko wai sauranmu 3weeks wallahi na matsu mugama da matsalr ssce!".

"Ai saura kiris wanda yayi kusan 6years ai 3weeks bazasu gagara ba Allah dai ya nuna mana lokaci".

" Ameen ameen yakamta mu tafi ko?".

"Gaskiya kam mun zauna sai surutu muke" tafada suna mikewa suna daukar papers da calculators dinsu, tafe suke gwanin shaawa har suka isa titi suka tari napep, sai da aka fara dropping din Fateema gida sannan Surayya ta wuce.

Da sallamar ta ta shiga cikin gidansu Mama dake sharar tsakar gida ta amsa mata cikin fara"a, gaidata tayi cikin sauri ta amshi tsintsiyar cikin rashin jin dadi ta ce "Haba mama kedai bakida lafiya meya hadaki da shara dakin bari nadawo ai sai na yi ko!?"

Murmushi Maman tayi cikin jindadin kulawar da Surayya ke nuna mata ta ce "Allah miki albarka yar nan amma ai naji dama sosai, keda kika dawo da gajiyar exams ai sai ki huta, ya exams?".

Shagwabe fuska tayi ta ce " Exams alhamdullillahi Mama don Allah ki bar sharar bari na sauya kaya nazo na ida don Allah!".

Duk yadda mamar taso haka ta turje barmata tayi har cikin ranata ta na samata albarka da mata adduo.

Sai da ta kammala share gidan tasss sannan ta nufi kitchen ta tarar anyi girki, ranta ba dadi ta wuce dakin batason mama nawahlada kanta sabida hawan jinin ta bai dade da tashi ba batada lafiya.

Zaune take bisa bed din ta rike da Q&A na chemistry tana nazari kasancewar yau Thursday ba suda exam sai Monday, shigowar Aisha da gudu yasata maida  hankalin ta wurinta cikin zafi ta ce "Ke zonan!".

Zuru zuru da idanu Aisha ta fara cikin tsoro ta ce " Don Allah anty Dr forgive me wallahi Kabeer ne ya biyoni kuma aikoni akayi!".

Kara tamke fuskarna tayi ta ce "Bakiji menace? ba zonan!".

Kamar tayi kuka haka ta isa wurinta kama mata kunne tayi sai da ta saki karar azaba, ta ce " Wannan ne last time da saki shigomin daki ba sallama, so nawa ina warning dinki amma bakiji idan kika sake sai na zaneki wallahi, stupid girl kawai oya fita kiyi sallama sannan ki sake shigowa".

Sum sum ficewa tayi ta na matsar kwallan karya, sallama tayi sannan ta shiga ta ce "Anty wai ana miki sallama a waje Mama tace nazo na fada miki".

Hararar ta kawai tayi da gudu tabar dakin bambami Surayya ta fara ta na cewa " Mutum sai dan karen naci kamar maye, akansa na kashe wayana yanzu kuma ya biyoni har gida meyasa wasu maza basada zucuya, kullum cikin nuna mana baa sonka ake amma kaki kabari nayi rayuwata!".tana mita haka tasa hijab din ta tasan yanzu mama zata sallamo mata da kanta.

Zaune ta tarar dashi bisa machine dinsa sallama ta masa don tasan darajar sallama,amsawa yayi yana kallon ta yana murmushi cikin damuwa ya ce "Haba yazaki kashemin waya bayan kinsan dole nayi missing din ki shiyassa ma na biyoki!".

Kallon sa tayi daga sama har kasa cikin jin takaicin sa ta ce " Sannu ubana bana bukatar jin voice dinka sam kuma banyi farincikin ganin ka ba, wai Suleiman meyasa bazaka gane irin tsanar da nake maka ba!".

Ko kadan kalamanta basuyi tasiri akansa ba ya saba tun ransa na baci yanzu har ya daina cikin ko in kula ya ce " Hmmm nidai bazan janye ba kuma insha Allah ke rabona ce ke matatace! Ina sonki Surayya bazan iya rayuwa babu ke ba, zan jira har zuwa ranarda zaki fahimci ni masoyinki ne na asali ki soni".

"Allah Ubangiji yamun dubun tsari nafison Allah ya dauki raina da naga wannan ranar!". wani uban tsaki ta buga sannan ta wuce yana kiranta ko kallonsa ba tayi ba.

Jan Babur dinsa yayi yana jin ba dadi.

Comment
Vote
nd share.

ANTYN TWINS😘

DOCTOR SURAYYA Where stories live. Discover now