DR. SRY 11-12

9 1 0
                                    

♦️♥️♦️
           *DOCTOR SURAYYA*
                 ♥️♦️♥️

Na.Nasbat Gwandu.
(auntyn twins)

Follow me on wattpad @nasbatgwandu01

Page 11-12

✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶🖊
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶🖊,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶

DEDICATED TO SWEETEST LOVE FAIZA.

PAGE 11-12

Bismillahir rahmanir rahim...

Saurin kallon sa tayi luckily suka had'a ido dashi ya kashe mata ido, kawar da kanta tayi tare da kallon Surayya cikin sanyin jiki ta ce "Ko zaki bi Saleem mu ajiye ki tunda bakijin dadi!? ".

Jan hannun ta tayi sannan ta ce "Rufamin asiri kada na shiga tsakanin romeo da Juliet nidai ga ma napep nan zamuyi waya".

Gyada mata kai kawai Fateema tayi ta samu napep ta shiga sannan ta fara tafiya kamar batason taka k'asa, tana ma Surayya jimamin rashin Saleem kwana d'aya d'innan da sukayi yadda yake nuna mata kamar ya had'iye ta tsabar so da kulawa, da wannan tunanin ta isa bakin motar bude gambu tayi ta shiga ita wata irin kunyar sa takeji sosai.

"Tabbb lallai ashe inada aiki Babylove wannan kunya haka, nidai Allah tana kwafsa min don Allah a daina!".

Ganin ya fara driving yasa a hankali ta ce "Good afternoon!".

Murmushi yayi ya kalleta sannan ya ce "Afternoon ya studies? hope bai wanda ya takura ma wife dina today!?".

"Alhamdulillahi nd meyasa kana aikin ka kazo daukana ai da kabari zan shiga napep mana tunda ita ta kawoni".

Kallonta yayi yana murmuahi ya ce "Gaskiya ni idan da zaki bani dama har kawoki ma zan dinga yi, Allah ina kishinki sosai yanzu haka ina office hankali na duk na kanki Allah ".

"No kada abin ya maka yawa niko daukana da zan dauke maka".

"Him nidai nasan komi ne indai akan ki ne bazan wahala ba".

Parking yayi bakin gidansu ya ce "Har mun iso amma kam munyi sauri wallah kamar kada mu iso!".

"Thanks alot sai munyi waya! " tafada tana bude gambu tana fita daga motar.

"Nikam banason thanks dinki I love u kawai nakeso kicemin!".

Saurin kulle gambun motar tayi da dan gudu tayi cikin gida tana dariya k'asa k'asa.

Dariya shima yayi cikin jindadi ya ce "Yah Allah ka mallakamin wannan yarinyar!",  kwana d'aya dinda sukayi jinsa yake kamar sun shekara tare.


Zaune take bisa carpet tana karatun al-qur'an ta kammala sallahr zuhr prayer kenan, ta kusan 30minutes tana karatun sannan ta kammala karatun addu'a tayi sosai daga ganinta tana cikin damuwa, addua tayi Allah yasa kada tayi aure yanzu sosai takai kukanta ga ubangiji, ninke carpet din tayi sannan ta dauki wayar ta dake ta faman ringing *SAMUEL* ne keta faman damunta, cilla wayar tayi bisa bed tana tunanin lokacin daukar mataki akan dukkan samarinta yayi.

Fita tayi ta nufi kitchen shinkafi da wake da k'wai da k'wai ta tarar, sosai taji dadi kusan shine favourite abincin ta plate ta samu ta d'iba da kwai da kwai, ta zuba tanka sosai da mai a hankali ta baro kitchen din tasan idan Mama ta ganta sai ta mata fadan cin yaji, sai da ta ajiye abincin ta koma ta dauko ruwa, jin vibration din wayarta yasata daukowa tana jan tsaki, sosai ranta ya b'aci receiving tayi tana cewa cikin tsiwa "Yau kam dole ayi ta k'are!".

Samuel da ke zaune gaban Mommyn sa daman itace keson gaisawa da ita, cikin dan zafi ya ce "Haba Sureey tun d'azu nake kira Momma nah keson ku gaisa mana!".

Cikin jin takaicin sa ta ce "Oh shiyassa kake damuna kamar bashi kake bina, toh ban buk'atar magana da ita kuma please kadaina takuramin wallahi bana sonka!".

Runtse idanun sa yayi tashi yayi yabar parlourn cikin mamaki ya ce "Surayya kada kimin haka kimin wulakanci don kinga ina sonki Allah komai zai iya faruwa dani! ".

"Nidai kaga bawon Allah don Allah nagaji wannan ma last waya ce nake dakai inada wanda nakeso, kuma idan ba rashin hankali irin naki mezan da arne!? ".

Sosai kalmar ta masa zafi cikin b'acin rai ya ce "Ni zaki zaga wallahi u must pay akan abinda kikamin!".

Tsaki taja tare da hanging din call din, abincin ta bata wani ci sosia ba tamafi cin k'wai da k'wai, ruwa tasha ta kwashe plates ta dawo wayarta ta dauko incoming call ne ya shigo Suleiman ta gani, shima d'auka tayi ta gaya masa magana son ranta ta kashe wayar, sim din gabadaya ta dauka ta kare ta ajiye wayar b SIM.

Toilet ta nufa tayi wanka ganin 3:47 yasata saurin shiryawa, sallah tayi ta fita zuwa aza dinner.

Hankalin ta kwance haka ta kammala tuwon shinkafa da miyar alayyahu sai kusan 7 sannan ta kammala tuwon ta, da miya jin ana kiran sallar magrib yasata komawa d'aki ta gabatar da sallar ta, assignment din da aka basu ta dauko ta duba bata wani wahala ba dukda maths ne,  sallar ishai tayi sannan ta ida assignment  din, ninke carpet tayi ta nufi side din Mama.

Ta tarar su Aisha da Kabeer na cin abinci duk gaidata sukayi ta amsa sannan ta nufi bedroom gaida Mama, ta tarar da ita tana ninke carpet din sallah gaidata tayi ta amsa cikin sakin fuska, tashi tayi da niyyar barin dakin Mama ta ce "Surayya zauna muyi wata magana dake".

Bata kawo komai a ranta ba ta zaune gefen gado,  itaama Mama zama tayi cikin damuwa ta ce "Kinada labarin wani yaro yazo gun babanki akan cewa yana sonki, kuma ya amince bincike kawai zaiyi zuwa 2months ayi engagement sai aure! ".

Saurin kallon Maman ta tayi idanun ta suka fara zubar k'wallah, cikin crying voice ta ce "Mama ni ce za'a yiwa baiko da wanda bansani ba? ".

Jikin Mama sosia yayi sanyi a hankali ta ce "Yanzu maganar da nake miki na masa magana yace nan da one week idan kin fidda wanda kikeso zai janye, shiyasa na sanar da ke SUrayya nasan kinada burin zama Doctor kada ki bari wannan burin naki ya wahaldake ki cutar da kanki,  idan kika fidda wanda kikeso insha Allah zai amince miki kiyi karatun ki dakin mijinki, aure ba shine zai miki katanga da cika burin ki ba!".

Kuka take rerawa a hankali cikin tausayin kanta ta ce "Allah Mama yanzu banda zab'i duk yadda Baba yayi ba laifi! ".

"No kidai yi tunani kuma don Allah kukan na meye? kada kisama zuciyar ki tunani Surayya Babanki bazai miki abinda zai cutar da ke ba, tashi kije ki kwanta sai da safe! ".

Sum sum ta tashi tabar dakin tayi kuka kamar mi sannan daga baya wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita.

Sosai tabi ta rame duk ta k'are wanda hakan ya dami mama da Fateema, tamabayr duniya an mata tace bakomai duk da damuwar hakan bai hanata karatun waec ba don suara 1 Week a fara,  duk da bawani gane karatun take ba saboda damuwa.

*BAYAN WATA BIYU*
.

Comment
Vote
nd share.

ANTYN TWINS😘

DOCTOR SURAYYA Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ