DR.SRY 03-04

7 0 0
                                    

♦️♥️♦️
           *DOCTOR SURAYYA*
                 ♥️♦️♥️

Na.Nasbat Gwandu.
(auntyn twins)

Page 03-04

✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶🖊
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶🖊,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶

Page 03-04

Bismillahir rahmanir rahim...

"Allah Mama ban samu keke napep da wuri bane kinsan yau Friday kuma koda aka tadamun an tada sallar Friday shiyassa"

Mama dan jim tayi sannan tace "toh masha Allah lallai anfara shiryuwa mutane da ana sallah amma ta sana'arsu suke, sun maidata gaba da komai Allah dai ya kara shiryawa"

"Ameen Mama shine baki jirani nazo na gyara kifin ba?, bara na dan watsa ruwa nayi sallah na fito amsa miki gyaran kifin"

Cikin jin dadi Mama tace "No yanzu jeki yi wanka da sallah kizo kici abinci, Aisha na nan zata soya na aikata makwabta yanzun zata dawo"

Zumbure baki tayi cikin shagwaba tace "Mama Allah Aisha bats iya komai ba kada ta lalata kifinnan don Allah kibari nayi!"

"Surayya banson shirme ai da koyo ake iyawa so kike ta tabbata bata iya ba? Kedai kije kikama aikin gabanki amma aiki kam badai wannan ba!"

Tashi tayi had da bugs kafa kasa alamun kuka,tana sambatu haka ta nufi daki Mama ko ta kanta batayi ba.

Tayi kusan 1hour a dakin sai da tayi taking shower sannan tayi sallah, ta fito ta tarar da Aisha na suyar kifi, cikin zolaya tace "aah autar mama aiki kawai ake? Mudai a mana mai dama idan anaso muci"

Aisha dariya tayi sannan cikin sakin fuska tace "anty Dr ina wuni? Ashe kindawo nake wahalar da kaina nasan idan kika mana zaifi dadi, ko na baki ki cigaba please"

Harara ta dankara mata cikin dan zafi tace "sannu a dole ga wahalalliya ta dawo ko!? Allah kinsan bana wasa dake ko? ki maida hankali ki karasa aikin ki, yarinya kamar ba macce ba sai dan banzan son jiki inda Mama bata maida hankali a kanki ba da ba mai rabata da ke!"

Bata bi ta kanta ba ta wuce kitchen zuwa dibar abinci taci.

Karkace baki tayi tareda sakin shagwababben kuka, Mama da fitowar ta kenan daga daki tace "lafiya auta waya taba minke ne?"

Shiru tayi sannan tace "Mama ba anty dr ce tace ba mai rabani dake wai don inada son jiki sosai!"

Fitowar Surayya daga kitchen ya maida hankalin su duka can, Mama ta jefeta da kallon rashin gaskiya nunata tayi tace "ke zo nan!"

Cikin inda inda tace "Mama nifa abinci zanci kuma ai ita tafara min rashin mutunci, wai bata san nadawo b da bazata wahalda kanta wurin suya ba, a dole ni ce wahalalla nadawo"

Mama kallon tuhuma tayima Aisha tace "auta aikin nawane wahala? Allah idan baki bar halinnan ba zamu saba"

Itadai Surayya ganin anbar chapter din ta yasa sum sum ta wuce daki da dan plate din ta,sai da ta dauko ruwa taci abinci dai dai cikinta sannna tasha ruwa ta tsaftace wurin tsaf, fita tayi tayi sharar gida tsaf sannan ta dawo daki da yake dutyn Auta ne abinci, duo da bataso haka ba Mama tace itama macece dole ta taahi tsaye ta koya mata.

Sallah tayi sannan ta dauko phones dinta huawei y6 da infinix smart 3 plus, kallon wayar tayi sam ta manta tasa ta flight mode haba shiyassa bataji ana damunta ba,messeges ne suka fara rututu wurin shigowa, ajiye wayar tayi ta dauki huawei ta hau online, kasancewar wayar special line ne a ciki duk tarkacen samarinta bamai number din itace wadda Baba ya siye mata, family and close friends ne kawai keda number, dubawa tayi taga fateema bata online, ajiye wayar tayi ta dauki infinix messages din sun mata yawa bazata iya karantasu ba, kuma da dama new number's ne, incoming call dinda ya shigo wayarta shi ya maida mata hankali ga wayar. 

New number ce ke yawo bisa screen din wayar batare da fargabar komai ba tayi receiving din call din, batace komai ba sannna kuma baa ce komai ba, dan siririn tsaki taja tare da hanging din call din, incoming call din the same new number ne yasake shigowa, batabi takan wayar ba saima tashi da tayi ta dauko school bag dinta, still wayar tata ringing tacigaba dayi, cikin jin haushi ta dauka.

"Hlo beautynah!"

Tanajin muryar tagane Suleiman ne Allah yabata baiwar rike muryar mutane, itama had mamaki take wataran cikin jin haushi tace "Oh daman kaine kake raina min hankali ko!?"

Suleiman dake zaune bisa machine dinsa ya yi murmushi tare da cewa cikin lallami "sorry Dr bansan kinyi receiving bane wallahi"

Cikin ko in kula tace "owkay kayi kanka yanzu bazan samu damar magana da kai ba, banda time sai dai zuwa gobe and please kada ka sake kirana" dif ta kashe wayar.

Suleiman inda sabo ya saba cikin rashin damuwa yace "kiyi abinki baby lokacin ki ne Allah ya mallaka min ke nima na rama".

School bag din ta bude ta dauki assignments din ta na  chemistry da biology da aka basu, da yake tanada textbooks da dictionary bata wani wahala ba ta kammala su.

Tayi mamakin ganin har ta kammala baa kirata Wanda hakan ya mata dadi, ganin hakan yasata dauko physics note din ta don ta duba, Alla yayi mata baseera sosia don ma bata maida hankali sosai ne, daukat book din keda wuya incoming call ya shigo wayart, Ahmad ne haka dai bata karanci kowa ba tazauna zaman waya, har Saleem da Samuel duk tayi waya da kowa,da kyar tayi wayar dasu don kowa ya kirata waiting call ya keji.

Bata bar wayar ba sai da taji ana kiran sallar magrin, bataji dadin rashin samun karatu ba amma ai zuwa anjima tayi, switch off din wayar tayi wadda ake damunta, tabar infinix kawai sanan ta nufi toilet, tayi alwalla sannan ta gabatar da sallar ta, nan ta zaunatana karatun alkur an har aka kira isha'i, tayi tayi azkhar sannan ta tashi ta ninke carpet din.

Side din Mama ta nufa ta gaida ta can ta taradda Aisha da Kabeer suna cin abinci, a a tare suka gaidata ta amsa bata ma bi ta Kansu ba ta biya kitchen ta dibi kifi kawai sannna ta koma side din ta, bata wani ci ssai ba.

10:08pm.

Karatu take sosai duk da kusan revising ne kawai take, kasan cewar next week zasu fara waec, takai kusan 12pm tana karatu ganin ta diba sosai yasata kwanciya don gobe Saturday ne.

Jin kawai tayi Mama na tadata wai anyi subh prayer, haka ta tashi bacci fal idanunta tayi sallah ta komai bacci, ba ita tashi daga bacci ba sai 8 kasancewar Mama bata bari baccin rana sosai,brush kawai tayi shara tayi ta share dakin tass tsakar gida kam mama ta share abinta, indomie da egg ta dafa taci sannan tafada toilet tayi taking shower, ta shirya kamar mai fita anguwa, side din Mama ta nuf batanan ba kowa side din Baba ta nufa ta tarar dasu parlour, gaidasu tayi cikin girmamawa, tare suka amsa Baba yace yar Baba anjima zan yi magana da ke da mamanki kinji, sai da gabanta ya fadi ta gyada masa kai tana rokon Allah yasa ba maganar abinda take tunani bane, jiki sanyaye ta bar dakin.

Sai da ta kammala girki zuwa 2 sannna ta buds wayarta ta kira Saleem.

Dedicated to mom ND dad

comment and share pls.

ANTYN TWINS😍

DOCTOR SURAYYA Where stories live. Discover now