page_05

120 12 0
                                    


____MARAICHI.
BY_NANATOOU
WATTPAD_@nanatoou

Pg_05

     Wannan haihuwa..kuwa ta farantawa kowa rai..acikin dangi..Alh Abubakar yana can baisan ..abinda ke gubana ba..hankalinsa dai, duk yana akan ya tafi tsangaya..kasancewar yasan ya bar yagana..haihuwa ko yau ko gobe.. Dukda yana shayin,kattime..haka ya tun kare ta da maganar yanasan yaje don ya gaida iyayen nashi... Nan take kuwa, ta fara masifar,ita bata yardaba, daga haihuwarta zai dauki kafa yabarta da wahalar yayansa,dan haka ya bari sai an kwana biyu.. Badan ranshi yaso ya hakura da zuwan,sai bayan wata sannan ya kuma tada zancan..batasan zuwansa amman wannan, karan sai tace ya shirya,itama tanasan zuwa itama..Da ace adane sai yafi kowa farin Cikin zataje gaida iyayensa, amma yunzu sai ya zamana akasin hakan yakeji...zuciyar sa..cike da zulumin..yacca zata kaya musu in ta samu labarin yayi aure..matar ma harda ciki...koda yake yunzu zuciyarsa tafi karkata akan ta haife cikin..shi yasa yaketa daikin zaije..kodan yaga gudan jinin sa.. Ahaka dai suka nufi tsangaya....sun sami tarba mai kyau...sai haba haba akeyi dasu. Jikokin gidan sunata shiga domin gaidasu..amma dakyar kattime take amsawa...sunasan su dauki dantama...amman haka suka haqura.daman bata tawo da yaranba tabarsu a gidan aminiyarta tabawa. Ita dai baba furera...tana daga jefe a kishingide..tana kallan ikon allah..can kuma sai ta dan murmusa.. Bayan sun gama hutawa.. yamma nayi, kattime tace itafa ba kwana zatayiba tafiya zasuyi yau... Goggo Abu ta gyara zaman ta tare da fadin.."au kice komawa zakuyi..gashi kodan baku bari kun gani..ba"sai kuma tadan daga murya wajan fadin "uwata...karbo babban mutun kice da mamansa ta leko akwai baki zasu gaisa".. Tunda kattime taji ance 'da'taji gabanta ya fadi amman haka ta daure bata nuna komai ba..yayin da shi Abubakar kuwa...wata murna da farin cikiara misaltuwa,tare da tsananin fargaba,sukai masa dirar mikiya...wato dai hasashensa ya zamo gaskiya kenan...ya sami tsatso ta yagana...matar da yayiwa akabi da yar aljanna...waya kaisa farin ciki a wannan lokacin...ya wannan tunanin sai ga yarinyar da aka aika ta shiga runfar..goggo Abu ta karbi jariri,wanda ya doshi watanni kusan biyu ba kwanaki...da fara'arta ta amsheshi tana masa kirari " mai gidan,da ba cefane "tun kan ta mikawa..Abubakar shi, ya yunkuro,yakarbesa,cikin tsantsar soyayyar yaron. Fara'a taki boyuwa a fuskar Abubakar, ya rungume Muhammad a kirjin sa...sannan ya dubi..goggo abu yana fadin..yunzu fisabilillahi,goggo ai haihuwar,a rasa wanda zai gayamin..an kyauta kenan..murmushi daya kasa boyuwa a fuskar goggo da baba ganin yacca ya nuna soyayyar dan murarayan...yasa cikin dariya goggo abu tace "wazai gaya maka..babu dan sako..yunzu ai gashi ka gansa ai" "me aka sa masa goggo" yai saurin tambayarta "Babban sunane,ko baka gansa ba da surfar manyaba" ta kashe maganar cike da zolaya.....Abubakar zaiyi magana sallamar yagana..ta katsesu..tana sanye da atamfa tayi lullubi sosai..tanan durkusa dan nesa dasu..ta fara gaishe shi..tare dayi masa anzo lfy...goggo abuce tace mata ga uwar gidanta...kattime daman da tun sanda taga fuskar yaron tare da tsantsar murnar da Abubakar yakeyi...wanda zata iya rantsewar,ko sanda tai haihuwar fari me wannan daukin ba,hakan yasa tai mutuwar zaune...kar dai ace Abubakar ya munafuncetane yaci amanar ta..in kuwa hakane wallahi zatai musu tijara...ta nunawa kowa iyakarsa ..dan sun samuma tana daga musu kafa...kafin ta gama far fadowa da wannan al'ajabin ta kuma tozali da yagana..taga yacca mijinta da tafi so yake bin wata da kallo me cike da tsantsar so da ma'anoni da dama...kamar dirar mikiya kuma taji abunda goggo Abu take fada "uwar gidanta..???" Chab wallahi bazai sabuba...bata tsaya tunanin komai da ko shayin wani...ta mulmulo ashar ta zabga musu a wajan,kallo sai ya koma kanta, kan suce lafiya...ta dire danta a gefe...ta mike cike ta bala'i..ta fara fadin.."ni za'a ha'inta a munafunta...wallahi ba'isa...baman na san ba kaunata kukeyiba na zaman muku ciwon idone ba yacca zakuyi dani shiyasa....amman saboda tsohon annamimanci..sai da aka nemo wata kodaddiya aka hadata da mijina to wallahi da sake"ta juya wajan Abubakar "kai kuma tsohon munafiki...me surfar munafikan farko..Allah ya toni asirinka...daman amanata,kakeci,yaudai karshe tika tika tik..to wallahi baka isaba, daga kai har masu doraka a hanya...saboda annamimanci..shine kake cemin ka tafi kudu saro kaya bini bini ko??ashe nan kake zuwa kana cin amanata..an shanye ka sai yadda sukayi da kai..... " nan kuwa yaji ransa ya baci ya taka mata burki amman taki bari..goggo Abu tace ya kyaleta..haka Abubakar dai bace komaiba, ya sunkuyar da kansa ya kasa cewa komai...haka ta ci gaba da tijarar ta ba wanda yace mata kala...sai shigowar Alhaji umar ne ya tsawatar mata...cewa tanajin shakkarsa sai tayi shuru tana huci uwa wata zakanya..yayin da yagana ta takure a gefe ..tanajin matikar tsoran matar...alh umar yace maza su tattar su tafi.....jiki asabule suka wuce ...yayin da yagana kuma goggo abu ta dunga karfafa mata gwiwa tace kartaji komai insha allahu..komai zai daidaita.
Abubakar kam..ba irin tijarar da kattime batayi masa ba..sai ya zanto ya fita a harkarta...tunda yasan yasan yayi aure sai ya jishi saakayau, babu fargaba ko tararrabin yacca zai sanar mata.. Daga karshene da yaga abun nata ba arziki...saiya fita a harkarta,kwata kwata,sannan ya dau alwashin koya mata hankali..hakan yasa ko kallanta bayayi bare ya kulata...ta karaci haukanta...bayan kwana biyu kuma da kanta jikinta yai sanyi ganin yacca ya canza mata kartaje aikinta yayi kasa taje tai abunda zai sanadin auranta...wannan tunanin yasa ta sauke kanta kasa ta basa hakuri amman ya ki sakar mata fuska...sai da aka shefe wasu lokuta kan su dai daita kansu.sai ya zama duk friday da weekend yana can tsangaya..hakan yanayiwa kattime ciwo..amman bayacca ta iya...gashi...aikin take yi abin yaki ci...
Acan vangaren kuwa yagana taci gaba da rayiwarta da danta cikin aminci...bata da wata matsala..ban kowa so yake nuna mata..ta bangare mijintama bata da wata matsala. Shekarun Muhammad uku allah yayiwa alh umar rasuwa...tsoho mai ran karfe...wannan zuri'a sunyi rashi sosai...amman haka suka dauki dangana suka izawa zukatansu.
Bayan wani lokaci kuma Allah ya kuma yiwa baba furera rasuwa itama...wannan rashin yayiwa mutane da dama ciwo a ciki kuwa harda yagana dan tayi babban rashin rasa yayar mahaifinta da tayi..kuma sirikarta mahaifiyar mijin ta sannan matar da ta tsaya mata a matsayin uwa..take share mata hawayenta...tayi kuka sosai...shima Muhammad alokacin sai daya dan matse dan shekarunsa shida...gidan ya zamana sai yayye iyaye sun kare sai goggo Abu, data rage...bayan rasuwar baba furera ne kuma komai yasoma tabarbarewa...domin in alh abubakar ya zoma sai yaita fadanda babu gaira babu dalili..gashi sai ya shafe wata shida baizoba...bai damu da komai nasuba ...yan uwansa da suke tarene suke taimaka mata....
   Muhammad ya gama primary dinsa ..ya zamana saura secondary..hakan ya saka yagana kokar tawa..ya tafi..kuma gashi daman free education ne.ana haka itama Baba abu rai yayi halinsa..haka dai sukaci gaba da rayuwarsu... Rana tsaka kuma saiga Alh Abubakar, wai zai tafi da ita..vatai gardamaba..tabishi...komawa cikin kano da zama kuma rayuwa tare da mace daba digon imani a zuciyarta'kattime' yasa rayuwa tayiwa yagana tsauri..ita takema kattime komai..tare da hidimar yayanta duk da dai a lokacin ta aurar da matan saura daya agabanta, sai mazanta guda biyu kuma...kattime mulki take zubawa san ranta..ko abinci sai in taso take bawa yagana..hakan yasa ya gana dagewa wangan neman abinda zata rufawa kanta asiri...tai surfe tai wankau..wannan takinne kuma ta lura tana da shigar ciki...gashi mai wahalarwane...ranar da kattime tasan da cikin sai datayi kamar zata rufe yagana da duka, amman taqiyin hakan,tafison tai mata kisan mimmike..hakan yasa ta nika ayyukan da take bawa yagana...baiwar Allah kuwa haka take daurewa tayi...har cikinta ya tsufa ..lokacin..Muhammad yazo hutu yana jss3.yana tausaya wa mahaifiyarsa hakan yasa yake san ya girma kodan ya dauketa daga wannan uqubar da take ciki...dawowarsa da kwana biyi ta haihu..ta haifi yarta mace...kamarsu daya...Muhammad yaita murna..da alh Abubakar yaji shima sai da yayi murna,da kansa yai mata huduba da fa'iza..ya kuma yanka nata rago daya...haka rayiwa taci gaba da tafiya..yau zuma gobe madaci...har allah ya saka..muhammad ya kare karatun secondary dinsa...a lokacin yana da shekaru goma sha takwas...ya kuma ci gaba da karatunsa a.. Bayero university dake nan cikin garin kano...a shekarar ne kuma allah ya karbi ran alh umar...ba tare dayi cuta ko wani abuba...kwanciyar bacci yayi aka tashi kuma rai yayi halinsa..alokacin, shekara daya kenan da haihuwar da kattime takumayi kenan akasa jaririn abubakar.
A raban gado kuwa san rai aka nuna da san zuciya kattime da ya'yanta sukayi handama da babakere a komai...gashi daman shi Muhammad ba abun daya sani game da dukiyar mahaifin nasa,sai dai yasan cewa yana da matukar arziqi...wasu yan kudade aka basu sannan suka basu lokacin tashi daga gidan..acewar su zasu siyar suma...Ran Muhammad ya baci amman ba damar magana, dan yaagana ta hana shi...sarkokinta na..bashi dadaddu tace ya siyar sannan suka siyi gida a goron dutse da kudin..suka hada inasu yanasu haka bar musu nan din.
   Yunzu rayuwa tai musu dadi domin..ba wata takura..fa'izama ta sake abunta ba kamar acan da bata da ikon fita tsakar gidaba...sauran kudin kuma Muhammad ya samu wani aminin alh Abubakar...shiya taimaka masa ya dunga nuna masa kasuwanci..yakuma ci gaba da karatun sa yayin da aminin mahaifinsa din ya dinga juya masa kudin yacca ya kamata...yayinda su ishaq suketa shagalinsu da dukiya san ransu..bayan kare karatun Muhammad ne..yaje yayi bautar kasa..sai kuma ya dawo ya tsindima harkar kasuwancin sosai...yana da burin inganta rayuwar kanwar tasa tilo da kuma ta mahaifiyarsu..dan taga rayuwa..Ubangiji ya basa nasibi a akasuwancin...riba ta ko ina shigowa takeyi..daga nan kuma sai yayi gidan gona .a gefe kuma yana kasuwancinsa a kwari..ga kuma kayan kitchen da yake siyarwa ...nan danan sai albarka ta shiga cikin abun nasu rayuwarsu a yinzu sai hamdala...
Bayan shekaru biyar..ya tafi cairo karo karatunsa na matakin masters...can ne kuma yar buzaye ta tafi da imaninsa.....
   Khadija matashiyar budurwace mai shekaru goma sha tara..a lokacin...yar asalin garin afadez ce acan jahoriyar Niger... Yar babban gidace..ta kuma kasance autace ita...yan uwanta suna matikar ji da ita...karatu ya kawota cairo..inda take hada degree dinta akan physiology... Haduwarta da Muhammad ya kawowa ko wannensu sauyi a rayuwarsa ...sun kulla alaka mai kyau da tsafta a tsakaninsu,har Muhammad ya hada masters dinsa..alokacin ya zamana sauran yan watanni itama ta kare nata karatun..yai mata alkawarin zaije agadez...bayan dawo warsa kuwa be samu matsala da yagana ba tai masa fatan alkhairi...faiza sai murna itama takeyi.. Koda Muhammad yaje agadez sun karbeahi hannu bibbiyu..ya kuma yaba da dattakonsu..hannan suka tsaida maganar zai turo magabatansa.. Yana dawowa Nigeria, bayyi kasa a gwiwaba ya tun kare yan uwan mahaifansa da sukayi saura...suma sunyi murna dan ya kamata yayi auran tunda har yakai shekaru talatin...koda sukaje agadez sun sami tarba mekyau hakan yasa suka kuma aminta da tarbiyar matarda zai auro..nan suka abubuwan da al'ada ta tanadar sannan aka tsai da lokacin biki wata biyu masu zuwa...bayan su dawo akaafara,shirye shiryen biki..yayin da Muhammad ya dukufa ganin ya gama hada laife ankai...yar allah yasa aka kai cikin nasara
Bangaren kattime kuwa...da farko rayiwa tayi musu dadi yayin da sukeyin yacca sukaga dama..gashi ishaq ya isa aure amman yaki yayi...kuma bata isa ta gaya musu ai jiba ..ita a wajantama ai ba komai..suka gyara gida...ko.ai na tafiyan musu dai dai..ga yayanta mata a gidan miji sai mazan ukune a gabanta...ta wani fannin kuma tana kishi da nasarar Muhammad sosai dan duk yacca suke ciki suba da saniya akan komai...yaso lalata rayuwar Muhammad din..amman allah bai bata ikoba...sai abinma ya kusan komawa kan yayanta..dan alokacin saida atika ta dawo gida da saki biyu..yayin da yusha'u kuwa ya dunga shaye shaye na fitar hankali...wanda saidaya taba masa kwakwalwa..takai yana ganin likita....ishaq kuwa gashinanne yana dan taba kasuwancin...sai rashin albarka.
   Wata biyu sukazo suka wuce...akasha biki...aka kawo amarya gidanta.anan goron dutse,wanda asalin wanda suka siyane shine yinzu Muhammad ya siyi filin kusa dasu ya kuma kere gidan.
   Zaman khadija da yagana..abin sha'awa domin sanyine ya hadu da sanyi..suna zama cikin girmama juna...ga kuma fa'iza fa ta zama koda yaushe tana wurin khadija.shakuwa ta shiga tsakaninsu mayiqa..shekarunta sha biyar tana ss1.
Yagana..mace mai zuciyar musulmai...duk abinda kattime tai mata..tamaidashi ba komaiba...tasa Muhammad yana yi mata abu tamkar uwarsa..tun ransa bayaso .sai ta tuna masa girman sada zumunci..da kuma yafiya..hakan yasa ya dunga hidimta musu kan jiki kan karfi...ya dauki nauyin karatun Abubakar....ya jawo ishaq zuwa kasuwa...sannan ya fitar da yusha'u waje dan a duba kwakwalwarsa. Yan uwansa mata kuma yana binsu har gidajan su ya musu ihsani ya kuma kyautatawa ya'yansa ..duk da wannan abun, yagana da zuri'arta babu taba birge su kattimeba...kullum cikin tsine musu sukeyi....suna cewa su suke bin bokaye da malaamai dan su lalata mata rayuwar zuri'a.
Bayan auro khadija, sai suka dauki hassadar su da karan tsana suka dora akanta...
  Shekara daya shekara biyu...shiru khadija..bata haihuba hakan yasaka..baba kattime ta fara takuwa mata da fadin kyale kyalen banza ce ,sai kyau babu amfani..yacca suka takura mata in sunzo gidan, ko insun hadu a wajan wani taron na dangi..ya saka ya fara tunanin kodai da gasken bazata haihuba.suka dangana da likita...yace lafiya lau..a daya bangaren kuma fa'iza ta kare karatun secondary dinta...tana da niyar ci gaba da karatu..yayin da Muhammad kuma..yaketayi mata shirye shiryen zuwa turkey..acan yakesan tayi karatun nata.cikin yardar allah komai ya kammala..ta tafi..sai fatan Allah yabada sa'a..acanne kuma allah ya hada da bilal..half cast ne...mahaifinshi turkiye mahaifiyar sa Lebanese...a makarantar yake sai dai..shi a shekarar karshe yake..yana gama karatu fa'iza ta sanarda khadija yayin da ita kuwa ta sanar da mijin nata...yaso yaki amince wa ganin nisan da za'a samu atsakaninsu gata ita kadaice yar uwarsa...khadija ta jajirce ta nuna masa mahimmancin amincewar sa kodan in ganta rayuwar fa'izar dan ta kwallafa ranta akan bilal din.ya abince kuwa ba'a jimaba kuwa akayi hidimar aure aka gama.amarya ta tare a turkey ta kuma ci gaba da karatunta...wannan abu ya kuma yiwasu kattime zafi........

#COMMENT
#VOTE
#FOLLOW
#SHARE

MARAICHIWhere stories live. Discover now