Maraichi____
By_Nanatoou
Wattpad_@nanatoouPage_47
Rayuwata in aka kiramin yan uwana, to bani da wasu sama da su. Su din farin ciki nane. Feelings din su shine nawa. Sai na sasu a farkon komai sannan nake iya tunawa da kaina
Mun samu Sanah ta fita daga wannan depression state din data shiga sakamakon abinda Rashid yayi mata.
Ban taba ta da zancen ba, saboda har yau hakan nayi min ciwo a raina. Yayin da ta dayan bangaren kuma duk da jan kunnan da Aunty Hajara tayi mukayi watsi da hakan, ban kuma barin Sanah ta shiga gidan da zummar zuwa bangaren Rashid ba. Abu daya nayi da nake ganin hakam shine dai-dai. Nai mata karyar Inna Barira ce ke gyarawa. Ban san daga karshe in Aunth Hajara ta kuma sanin bama zuwa abinda zata yi ba. Amman kuma am ready to take the risk.
Inna Barira, komai zanyi a rayiwa sai na mata addu'ar gamawa da duniya lafiya. Bayan rasuwar iyayen mu, itace mace ta farko data fara tsaya mana, take tare damu, ta zaman mana wani bango da zamu jingina muji sassauci a zukatanmu, ko da kuwa tasan abinda akayi mana ko akasin hakan.
Na yadda da maganan da akecewa a rayuwa abubuwa biyune ke faruwa, kuma su suka hada duniyar tun farkonta kuma har zuea ranar da za'a nade ta. Kyakkyawa da mummuna, alkairi ko sharri. Wayannan su sukaya mu, sume suka fassara waye ma dan adam tare da rayuwar da mukeyi. Dole ya zama a cikin biyun nan ka dauki daya the good or the bad.
Kyakkyawa da Mummuna suke indicating din mutumin da yabi hanyar Allah mai dorewa tare kuma da wanda yabi ha yar shedan wacca zata kaisa ga hallaka.
Alokacin da zaka zabi dayan biyun nan, dole sai ka zamanto mutum mai nazari, ka zurfafa tunanin ka tare da kallan abubuwa ta bangare da dama.
A lokacin da ka dauki abu mai kyau, u have to be cautious, domin kuwa yana zuwane tae da kalubale masu dimbin yawa, na farko jama'ar da kake kewaye dasu. Duk wanda yace zaibi han yar ubangiji sai ya wahalta tare da fuskantar kalubale da bama, domin yayin da kace zaka zamanto mai gaskiya, a lokacin wasu zasu kalubalanceka ta bangarori da dama. Sai ka zamanto mai sadaukarwa a duk yanayin da kake ciki.
Hanyar shedan, ta zamanto mai matukar kayatarwa, tare da janyo ra'ayoyin mutane da dama koda ace bazasu tsinci komai a cikin taba, sukan bita daga karshe kuma wannan san zuciyar tasu yana kai sune da hallaka kafin su farga. Zalunci, danne hakkin na kasa dakai, zambo cikin aminci, ha'inci, karya , yaudara. Wayannan sun zamanto ba komai bane a cikin jama'a. Duk da sunsan cewa hakan ba dai dai bane, zasu aikatasa akan san zuciyar su, wanda daga karshe hakan bazai anfane su da komai ba, illa dana sani tare da cixan yatsa.
Shi yasa a komai anasan ka zamanto mai zurfin tunani, yayin daka yashi yanke hukunci karka yankeshi asan zuciyar ka, ya zamana cewa ka kallesa daga dukkanin bangarori kafin, sannan ka kalli daga karshe mai zai haifar maka kafin ka zabesa. Mu manta da san zuciyar mu, yayinda zamu saka Allah a komai namu, sai kkmai ya dunga zuwan mana cikin nasara da sahalewar ubangiji.
A koda yaushe wayannan maganganun suna yawan dawomin kwakwalwata ina jin tamkar a lokacin ake gaya minsu. Da nayi dogan nazari sai naga ba komai ke wahal damu ba face san zuciyar mu, to ya za'ayi mubar san zuciya, dan adam ya koma kan dai dai ne???
Amsar shine babu. Da ace akwai amsar Aunty Hajara zakaga cewa ba komai take tsinta a cikin cin mutincin da take mana ba, zata rungumemu ya'ya ta dubi maraichin mu, ta jamu a jiki. Amman kuma san zuciyarta mai yasa ta, sai ya bata sabanin hakan akan wani dalilinta, (na ban san sa ba) take ganin cewa samu a kunci shine ribarta da jin dadin ta. Meye to jin dadin ta dan mun zubar da hawaye, mai kuma zai rage ta dan ta sanya fara'a a fukokinmu tare da zukatan mu??, nan ma amsar shine babu.

YOU ARE READING
MARAICHI
General FictionWe were gloomy after the death of our parents. All we need is even a bit of slightly light, but things fall apart. When things became dreadful, there's some hint of conceal deeds. The revelation goes with the end of our disastrous life. But how, whe...