part_II_17

50 6 3
                                    

'Aboki...'' na furta sunan sa cikin nutsuwa. Murmushi ya sakar min kafin ya amsa da fadin, ''Yes dear friend ya akayi...''.
Na ɗan ɓata fuska kafin nace, ''kaƙi zuwa na ganka, session din ma har yau baka zo ma, it's been a week''.

Murmushi yayi kyan shi na fulanin usul yana baiyana, ''calm down, na gaya miki uzurina amman this week zan shigo Abuja insha Allah''.

Na gyaɗa kaina tare da fadin, ''Allah ya yadda''.

''no more complain yunzu'' yai maganar cikin sigar tambaya. Gyaɗa kaina nayi ina kuma sakin murmushi, ''eh.. mana tunda zaka zo shikenan''

''Ya jikin naki, bakya samun matsala da bacci?"".

Gyara rikon wayar nayi, ina ganin yadda ya nutsu yana jiran amsa ta. Murmushi nayi mishi tare da fadin, ''Komai ya dawo daidai friend, ina bacci sosai, even today i over slept sai da gari yayi haske fa nayi sallah, wannan maganin daren yana sani bacci sosai zan dena shan shi...'' na gaya mishi ra'ayi na game da maganin.

Girgiza min kanshi yayi, ''A'ah Kausar karki soma, hakan abu mai kyaune ai bacci will always help you relax, pressure din da ƙwaƙwalwa ta dauka duk zai sauka..''.

Na gyaɗa kaina cike da fahimta, ''okay...''.

''mafarki fa, kinyi...?" Ya tambaye ni, duk da baiyi specifying wani kalar mafarki ba, amman kuma nasan yana san yasan ko in har yunzu ina samun waƴannan mafarkan da suke firgitani

Girgiza kaina nayi, kafin na soma faɗin ''Friend relax, any sign of trauma barina yake yi, yawanci baccin da nake yi yunzu ma is dreamless, bana wani mafarki, kuma daman kaga addu'o'in da kace na dunga yi duk ina yi, kuma yunzu bana tunani da yawa''. Na faɗa masa iyakacin gaskiyata.

''keep it up, nasan zaki iya hakan''. Ya faɗa cike da ƙara min ƙwarin gwiwa. Gyaɗa mishi kaina nayi, ''Yasmeen is truly happy yunzu, for the past days tare muke kwana dasu, muna hira sosai, friend and... and...''sai na kakare wajan abinda zan gaya mishi, nayi ƙasa da idanuwana na dena kallan wayan, ina jin zuciyata tana duka da ɗan ƙarfi.

''Kausar...''. Ya kira sunana, hakan ya sanyani na ɗaga kan nawa na kalli wayar. Hankalin shi kwacokwan suna kaina ne. Ya gyaɗa min kan shi cike da san ƙarfafa min gwiwa tare da assuring din cewa komai zaiyi daidai.

Na jinjina kaina, ''friend... Komai zai dawo daidai...?" Na jefa masa tambayar dake addabar ruhina.

Cike da assurance yace, ''in sha Allah Kausar, you're improving and i'm so proud of you, you could always be yourself''.

''thank you'' na samu bakina da firta hakan.

''ok, ya kamata na tafi yunzu akwai patients da zanyi attending, hope that's fine''.

Gyaɗa kaina nayi sannan mukayi sallama nayi disconnecting vedio call ɗin.

Ajjiyar zuciya nayi tare da ajjiye wayar a gefe.

Miƙewa nayi tare da sanya takalma na na nufi kitchen inda na baro su Aunty Luba.

A kitchen din kuwa gaba ki dayan su they were occupied suna kaiwa da komowa kowanne a cikin du da aikin da yake yi.

Na kara cikin kitchen din, Aunty Luba nima ta haɗa ni da abinda zan taimaka musu dayi.

Girke girke yunzu suna daya daga cikin abinda yake dauke min hankalina sannan kuma ya zama daya daga cikin hobbies ɗina a yunzun. Haka ya sanya Aunty Luba take koya min abubuwa da dama.

Yau har  baking nayi da safe da kaina amman Aunty Luba tana guiding dina daga gefe, nayi cupcake din da dan dama saboda zamuje mu dubo ƙawar Aunty Luba bata ji daɗi ba.

Sai can bayan sallar azahar muka kammala yin komai.  Dakina na tafi naje na soma yin sallah kafin na daga bisani na koma downstairs muci abinci. Bayan mun gama cin abincin kuwa, kwanciyata nayi tare da ɗora kaina akan cinyar Aunty Luba, Kubra ƴar tsokana kuwa bata fasa halin ta ba, ta hau tsokana ta wai ita ta rasa gane waye auta tsakanina da Amjad, ni kuwa dariya kawai nayi mata. Aunty Luba ce me iƙirarin nice yar auta kuma kar wanda ya takura mun.

MARAICHIWhere stories live. Discover now