MARAICHI___
BY_NANATOOU
WATTPAD_@nanatoouPg_42
Yau da sassafe na tashi, bayan na shiga bandaki nayi uzurirrikana na fito, na kalli yacca Sanah take bacci ita da Amjad. Na salallaba na fita daga dakin. Ina matukar dan iskan dafen dake kadawa a waje. Na sami waje na zauna, tunani nake amman bama zan iyacewa ga abinda baje tunani taka meme ba. Na jima a wajan kafin naga na tashi na koma ciki. Shigata ba jijawa sai ga Inna Barira ta zo. Tun kan mu gaisa na ganta a gigice, yacca gaba daya tayi ne nasan cewa da matsala, amman kuma maiya faru ban sani ba. Kafin ma na tambaye ta, ta hau tashin Sanah daga baccin da take yi. Bata bari Sanah ma ta gama watsakewa ba ta fara ce mata ta taso. Na dubeta cike da san jin mai ya faru na fara tambayar ta lafiya kuwa?.
Tai shuru cike da jimami, yayin da Sanah ke kokarin mai da hankalin ta kanmu. Ta samu ta dan mutsittsika idanuwanta tare da fadin, "Inna wani abunne ya faru?"
"Allah ne yaima Sameer rasuwa da asubah" mukaji ta fada, maganan ya riskemu tkar saukar aradu. Ni da nayi niyar zama na kame a yacca nake, yayin da Sanah ta mike zumbur tare da dafe kirjin ta. We were very shocked. Maganan tayi matukar dukanmu. Ni a wajena ma ji nake nice kunnuwana basu jiye min zancan da kyau ba. Zuciyata ta fara bugawa da karfi, mutuwa? Kuma sameer. Anya kuwa hakane. Duk muka zubama inna Barira idanuwa cike da waduwar gaba muna neman kara tabbatarwa da abinda yaima kunnuwanmu dirar mikiya. Ina wannan sheken ne inna kuma fadin, "Yayi rashin lafiya, kafin gari ya waye a asibiti ya rasu. Ga gawar can ma an kawota..." Tai maganan cike da sanyin jiki, maganan na fita da dacin dake ranta da mutuwar.
"Innalillahi wa'inna ilaihir'rajiun" muka hada baki wajan fada nida Sanah. Yayin da araina naci gaba da ambatarta.
Na samu na zame na zauna ina tunano fuskar yaron. Yacca yake sakin mirmushi, da yacca zai bata rai wani lokacin.
It has been a Month, dawowar mi wannan gidan. Kuma a two weeks din da suka gabata, ina yawan ganin sa.
Na tuna rabo na da shi fa three days kenan, na fara tuna abinda suka gabjata a cikin ranan.
Yamma ne, ni da Amjad muna waje muna wasan mu. Kusan guje guje ne wai zai kamani da tafiyar sa ta yan yaye. Sai dariya nake masa ganin yacca sai yazo dab dani saina zille masa nayi wani gurin kuma. Sanah na daga gefe da kur'ani tana karatu amman a cikin ta ba'a fili ba. Tunda yunzu in dai bata wani abin to koda yaushe cikin karanta kur'ani take.
A raina ina raya dama ta taso taxo muyi. Muna a haka naga ana leko mu. Hakan ya saka na dakata dan na tabbatar da hakan. Sai kuwa naga an kuma lekowa din. Amman anyi saurin janyewa. Amjad ne ya kama kayana yana dariyar ya kamani. Nai dariya nima ina fadin, "ganin dama nayi ka kamani yaro". Daga haka na dauke sa, nayi hanya naga waye a wajan yake leko mu. 7 xuwa na tarar da Sameer a tsugunne a wajan. Na tsaya a kansa ina kallan sa shima yana kallo na. Ban taba ganin sa a wajejen nan ba, ya wanci sai dai na gansa a compound yana wasa da machine dinsa ko bicycle. " ko maiya kawo sa nan ?" Na tambayi kaina. Sai kuma na kwabi kaina, ina ruwana da zaman sa anan din. Daman sanin bansan wake lekamu ba ya saka na zo na gani, dana san shine ma bazan zo ba.
Na juya zan tafi kenan muryar sa ta dakatar dani, "Zan iya bin ku?" Ya tambaye ni. Na juya na kalle sa. Yai wani tsuru tsuru da shi. Sai kawai na gyada masa kaina.
Nai gaba ina juyo sa yana biyo ni. Na karasa kan shinfidar da nayi mana muka zauna. Sai gashi shima ya cire takalmin sa ya samu guri ya zauna. Ya saka hannu a aljihun wandan sa duka biyun ya ciro chocolate guda biyu, ya mikowa Amjad. Kamar jira little yakeyi ya saurin sauka a jikina ya amsa. Sameer yai murmushi sannan ya dube ni tare da fadin, "Kullum ina san na dunga wasa tare da shi" ban amsa sa ba sai kallan sa kawai da nayi. Sai kuma yace, "shi basa da kayan wasa ni kuwa ina dasu da yawa a cikin gida, baki gani ba, katan dakine da kayan wasa na a ciki,". Yanxun ma ban amsasa ba. Dan banma san to, me sanxe masa ba. Ina ruwana da kayan wasan nasa. Sai kuma naji ba dadi a raina. So yake mu dunga wasa, ko kuma ince yana san mu saba amman kuna ni ban ma san yacca zan dunga yi masa ba. Muryar sa ta kuma katse ni, " kinaji , na dauke sa muje daki na muyi wssa tare da shiii" yq kaeashe cike da san na amince , "Allah ya kiyaye, uwarka ta karyamin dan uwa dan ba karamin aikin ta bane" na fadi hakan a raina. Amman a zahiri sai na dube sa tare da girgiza kaina kawai alamun a'ah.

YOU ARE READING
MARAICHI
General FictionWe were gloomy after the death of our parents. All we need is even a bit of slightly light, but things fall apart. When things became dreadful, there's some hint of conceal deeds. The revelation goes with the end of our disastrous life. But how, whe...