page_37

65 11 0
                                    

MARAICHI____
BY_NANATOOU

PG_37


Dariya tayi kafin tace, "shi wannan daga baya kenan.." Sai ta kuma gyara zaman ta tare da fadin, "kin san wani abu, nifa yunzu komai zan iya akan burina, kuma ga matakin cimma nasara na fara hangowa, sharadi shi kuwa wannan ba matsala bane, kawata.."

Maryama tai mrmushi,"shi yasa kullum kike dada burgeni, ba wasa"
Ta karashe maganan suna tafawa, sannan ta cigaba da fadin," tafiyar zata dauke mu, kamar sati daya kafin mu dawo, na gama shirya mana komai, a ganina mu tafi gobe mu zuba sammako, amman ban sani ba in hakan yayi miki?" Maryama ta tambaye ta.

"Kinjiki da wani magana, ai da zafi zafi, ake bugun karfe, sanyar mai zamuyi kuma,  ke mafa babau wasa..."

Maryama ta danyi yar dariya

"To, na sani ko hubbin naki bazai barki, ki wuce gobaba, kin san ku masu mazajan nan"

"Shi har yama soma..." Cewar Aunty hajara.

★★★

Ko dana koma daki, ban iya zama kona kwanta ba. So na dauki littafina, na fice daga dakin.

Bakin famfo na samu kaina da zama,  kasancewar wajan da inuwa. Littafin ma dana bude sai na kasa fahimtar duk abinda yake cikin sa.

Tunanunnuka suka cunkushe a kwakwalwata, amman kuma kace na tsayar da abu daya kwakkwara dake cikin zuciyata nima ban dani ba. Kawai dai bana jin dadin komai, zuciyata kuma tana min zafi.  Zan iya cewa, tun dana fara zuwa makaranta sai yunzu na kuma tsintar wannan yanayin tare dani.

Na jima a wajan, dan har sai da nayi bacci a wurin, dana tashi kuma, kran la'asar ne ya tada ni.

Wannan ranar haka na gama ta, koda Sanah ta sani a gaba da tambaya, sai ido kawai na iya tsura mata, ina ganin yacca gaba daya ta canza, sai naji na kuma damuwa sosai.

Washe gari babu makaranta, hakan ya saka tin asuba ban iya komawa bacci ba. Na tashi na soma abinda ya dace ace nayi. So nake Sanah ta samu hutu, dukda cewa bansan takameme meke faruwa da ita ba. Amman dai nasan tana bukatar hutu.

Lokacin da gari ya danyi haske na gama gyaran compound nayi duk abinda ya dace a wajan.

Na koma dakin mu, na samu Sanah har lokacin bacci take yi. Haka daman nake so. Dan haka, na samu a silale na kuma ficewa a dakin.

Ta kofar baya na kitchen, na shiga cikin gidan. Na samu na fara gyaran daya kamata nayi. Nai shara da goge goge. Bacin na gama a lokacin gari ya gama wayewa, the next thing daya rage shine hada breakfast kafin gyaran dakunan gidan.
Na tsaya tsakiyan kitchen din ina tunanin meye abinda ya kamata nayi nan gama, ban ma san ta ina zance zan soma girki ba. Ina a haka kofa ta bude, Sanah ta shigo. Sai taja ta tsaya tana min kallon, mai kike anan?

Murmushi na sakar mata, naje tare da rungume ta, sai kuma na dago ina bata fuska nace, "bafa yunzu ya kamata ki tashiba, yau kamata yayi kiyi bacci isasshe and i'll do the work, "

Sanah ta bani wani kallo irin "really, are u serious?", na kuma bata fuska.

"Nifa, Allah ya gani bansan wannan kallo, sai kina daukata irin that little pampered baby," nai maganan uwa zanyi kuka.

Sai naga ta saki murmushi tare da fadin , "exactly, that's what u're" ta karashe da yar dariyar ta.

"Ai shikenan.." Na fada da frowned face dina.

Sanah tai murmushi tana jawoni, "u act mature now, daddy's girl, is now a big girl, she knows right and wrong...and uhmmmm" sai ta dakata, na dubeta irin cigaba inajin ki. Jamin cheeks dina tayi, tare da dariya tana fadin.

MARAICHIWhere stories live. Discover now