_____MARAICHI
BY_NANATOOU
WATTPAD_@nanatoouAssalamu'alai'kum... I'll like to use this opportunity to show my gratitude towards my fans/readers,family and friends,for showering your love towards me...Few words are not enough for me to say thank you and i love u all.i really appreciated the love,thank u all for the birthday wishes.....
Pg_14
Baccin da na kwana biyu banyi irin shiba shi nayi,sanah kuwa bacci yau baiga idan taba,akan dadduma ta karashe daren nata,sai bayan tayi sallar asubane,ta tashi kausar tayi salla itama,amman ganin taqi tashi sai kawai ta itama ta kwanta,daga haka bacci yai gaba da ita.
Kukan da Amjad yake ne ya tasheni daga bacci,na yamutsa fuskata,kafin na fara kokarin bude idanuwana, haske na gani,sai kuma jikina da yakemin ciwo ta ko ina..jin kukan amjad na kuma tashi yasa na karasa ware idanuwana,ina yamutsa fuska jin jikina ba dai daiba,ta koina jikin ciwo yake min.na juya ingama a ina nake...na ganni a kwance a kasa akan bargo na kuma duba gefe na babu kowa awajan,to meya kawoni nan gurin,ina ne nan din. na karewa dakin kallo..anan ne kuma na tuna ashe jiya mun canza muhalli,an kawomu wani akurki a matsayin dakin mu...kukan amjad ya kuma katsemin tinanin nawa..ta waje kukan ashe yake shigowa..nai sauri na mike..na nufi hanyar fita.
Sanah ce,take ta jijjigashi tana rarrashinsa yayi shuru,itama bacci bai dade da daukar taba,kukan amjad din ya tashe ta,kuma tun dazu take kokarin ganin yayi shuru amman yaki yayi, tasan yunwa yakeji..kuma da taje main house din taga basu bude ba,ita kuwa bazata iya buga musu ba..tanata tunanin yacca zatayi mishi ta tasa...
A lokacin ne, ni kuma na fito daga dakin,sai bata rai nakeyi..na dubi sanah "mai ya same shine??'' Maganata ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi yi. Uwa zatai kuka ta dubeni " he's hungry" "to baki bashi abinci bane" sanah ta girgiza kanta "basu bude gidanba tukunna, kuma bana san tashin su" na bata fuska..ina san ince wani abu,amman kawai sai na share...na juya cikin dakin...idona ya sauka akan cake da juice din jiya nai saurin dauka na kuma fita.."mi koshi a bashi wannan allah yasa yaci"...sanah ta dibeni ganin abunda zan bashi "an zaici kuwa kausar..kin san fa kawai custard yake sha " "kika sani yunzu zai iyacin wannan din kafin anjima mu gayawa baffa a siyo masa custard din " na karashe maganar ina zama a kan dakalin wajan...sanah ma ta zauna,na karbi amjad din ina masa wakar cry cry baby...juice din ma fara bude wa na fara bashi a hankula,allah ya taimakeni kuwa ya karba ya fara sha..kusan a tare muka sauke ajjiyar zuciya nida ita..dan koni danace sai sha din,banda tabbas din hakan,shi yasa na dunga addu'a a zuciyata.
Ganin ya dan sha da auki,sai na ajjiye juice din na gutsirar masa cake din da kadan kadan na dunga bashi..yana karba ina hada masa da juice din sai da yadan ci da yawa sannan na kyaleshi.
Na bawa sanah shi, ni kuwa na mike na shige dakin,toilet na shiga,nayo alwala,nazo nayi sallah..na nan nade kayan shinfidar da mukayi,sannan na kuma fita waje.har yunzu jikina ciwo yake min...natashi nakoma wajan wajansu sanah din..har yunzu suna nan ainda na barsu..sai na zauna kusa da ita...amjad ya dawo jikin,anan dai ya dunga wasansa...yaso ya sauka ma na hanasa ina fadin "kul..ba'a wasa a kasan nan gurin kaji ko?" Ya kuwa zuba min ido kamar yasan me nake fada mishi nai murmushi ina karajin soyayyar yaran a raina nace "kai little dinnan ko...." Sanah ta mike tana fadin "let me shower" na gyada mata kai kurum.Bayan ta fito ta shiryane,nake cewa nima zanyi,ta dubeni "ki bari sai anjima" bata fuska nayi "my body is aching,in nayi zan danji dama damaa" bata kalleni ba ta kuma cewa "ni dai na gaya miki,ba yunzu zakiyi wankan ba,kinji ko?" Kai da kaji yacca tai maganar kasan commanding dina tayi,bazan iya musa mataba,haka na tsinci kaina da obeying abinda tace din, na samu na zauna,idanuna a kasa, yunzu she's like a mother to me..saboda haka nayi ma kaina alkawarin yi mata biyayya a kowani hali,tunda for sure,duk abinda zatayi is fot our own good,nasan sanah ciki da bai dinta...ban bukatar wani karin bayani a halayyarta.

ESTÁS LEYENDO
MARAICHI
Ficción GeneralWe were gloomy after the death of our parents. All we need is even a bit of slightly light, but things fall apart. When things became dreadful, there's some hint of conceal deeds. The revelation goes with the end of our disastrous life. But how, whe...