part_II_10
Murtala Muhammad international airport Lagos.
Lumshe idanuwana nayi tare da ajjiyar zuciya bayan jirgin ya tsaya.
Na bude idanuwana a hankula kafin na maida akalar kallona zuwa window din ina kallan filin jirgin.
"Adda finally we have land...". Amjad ya fada. Jin maganar sa ya sanya na maida kallona kan shi. Yasa tsaye bakin shi yaki rufuwa.
Yasmeen har ta mike tsaye, idanuwansu duk akaina. Murmushi nayi musu kafin na soma kokarin cire seat belt din.
**** ***** *****
Bayan saukowar mu daga jirgin iskar garin ta bige ni. Na kuma gyara zama hand bag dinata. Yau gani cikin Nigeria.
Amjad sai dan guje gujen murna yake yi, Yasmeen ta bishi tana gaya mishi yayi a hankula kar ya fadi.
Wayata naji na vibrating hakan ya sanya ni soma kokarin bude jakata. Ko ban duba ba nasan bazai taba wuce David ba.
Hasashena kuwa ya tabbata, kafin na daga kiran ya katse, kawai sai na mayar jakata.
A kokarin yin hakan naji nayi karo da mutum. Nayi baya yayin da wayata ta bugu da kasa.
Nai saurin daga idanuwana ina duban wanda yai min wannan ta'asar yayin da idanuwana suka fada kam wani namiji da shima idanun shi suna kaina.
Na kalle shi na kalli wayata da take kasan,duk danaga shima kayan sa sun zube hakan bai dame ni ba face jin zafi a raina da nayi na rashin bani hakuri da yayi.
" you're blind". Na samu kaina da furta hakan.
"Excuse me".
Harara na watsa mishi, foolish man , na raya hakan a raina. Na durkufa na dauki wayata yayin da nai gaba ina jan dogon tsaki.
*****
Bayan mun isa gida tun a parking lot muka had'u da aunty Luba. Cike da farin ciki ta rungume ni tare da fadin, " masha Allah sannun ku da hanya... Daughter, sannu kun sha hanya".
"Yauwa Aunty". Na fada.
Ta sake ni tana maida hankalin ta kam Uncle tare da Amjad, " Big boy...." Ta fada cike da murna.
Amjad yaje ya rumgume kafafunta yana dariya.Shafa kanshi tayi tare da fadin, "masha Allah... Little ka girma da yawa...".
" mama... Ni yunzu ai big biy ne". Ya fada kamar yadda yake san ta dunga kiran shi.
Dariya mukayi, "Yasmeen sannun ku da hanya ku tawo mu shiga ciki....". Aunty luba ta fada. Tana maida hankalinta kan Uncle, " Abban yara sannu da zuwa".
Da yauwa ya amsa mata kafin muyi hanyar shiga cikin gidan. Aunty luba na rike da hannun Amjad.
A parlour muka yada zangon. Aunty Luba ta dube mu tare da fadin, "muje na kaiku daki tukunna sai kuzo muci abinci,". Ta fada tana yin hanyar waje, mu kuma muka bi bayan ta.
Sama muka hau sannan ta nufi dakin da mu. Ta bude ta shiga tana fadin, " Kubra ta fita na aiketa, tana ta jiran zuwan ku, yunzu zaku ga ta dawo, nasan she can't to meet you both".
Murmushi kawai nayi mata, ina tuna yarinyar da mukayi yarinta da ita. Yunzu nasan ta girma sosai.
Aunty luba ta gyara curtains din sannan ta kunna mana A.c din dakin. Dakin sai kamshin turaran wuta yake zubawa.
Ta juyo ta dube mu. "Ga toilet nan kuna gamawa ku sauko kuci abinci, kun ji". " to aunty".yasmeen ta amsa ta.
Ta sakar mana murmushi daya kawata mata fuska kafin ta zo ra raba ta gefe na ta wuce.

YOU ARE READING
MARAICHI
General FictionWe were gloomy after the death of our parents. All we need is even a bit of slightly light, but things fall apart. When things became dreadful, there's some hint of conceal deeds. The revelation goes with the end of our disastrous life. But how, whe...