page_35

79 12 3
                                    

____MARAICHI
BY_NANATOOU
WATTPAD_@nanatoou

Page_35


Ban san yacca zan ba. Nayi kokarin kwantarwa kaina hankali, ko dan na samu solution, na san abinda ya kamata nayi a dai dai wannan lokacin.

Na juya na dubi makarantar, na danyi nisa da ita. Dan yunzu nama kusan fita titi.

Sai kawai na juya na koma makarantar.
Da ragowan mutane har yunzu,na karasa wajan wani tsoho mai sayar da kayan kayan alawa a kura, yana dan nesa da makarantar. Na gaishe sa, Ya dubeni yare da fadin

"Yarinya mai za'a baki"

"Baba, dan Allah ya sunannan wurin..unguwar nan" Na samu na tambaye sa.

"Yarinya ai kundila kenan..." Yai magana yana cigaba dayin harkokin sa.

Nai shuru, ina maimaita sunan wajan a raina. Tabbas ina jin sunan gurin, ban kuma taba zuwa ba, amman kuma ai nasan, is far away daga gida. To ya za'ai na koma gida?, na kuma tambayan kaina.

Na samu waje nadan tsaya, tsoro na lullube ni, yunzu inna bata kuma fa, ko wani abu ya same ni, wani hali Sanah zata shiga?, nasan Hankalin ta zai matukar tashi. Yunzu tana can tana tsammanin dawowa ta.
Wannan tunanin yasani tashi a gurin gashi, yunzu anan kiraye kirayen sallar la'asar.
Na karasa titi, ina ta kallan yacca abin hawa suke kaiwa da komowa.A take wani tunani yazo min.
Na saka hannu a aljihun gaban rigata ina lalubar kudin da na adana a dazu, har yunzu sunanan. Hakan yasa na yanke final decision.

★★★★★

Tunda su kausar suka bar gida take jin wani farin ciki, gani take koba komai yar uwanta zata samu rayuwa mai kyau.

Ta juya ta koma daki. Ta zauna bakin gado tana duban Amjad da har yunzu bacci yakeyi. Ta saki murmushi tarw da fadin, "insha Allah, komi will be okay"

Kettle ta dauka taje kitchen suka gaisa da Inna Barira, sannan ta dafa ruwan zafi ta koma daki.

Tana hada ruwan a toilet, tazo ta dauki Amjad tayi masa wanka.

Bayan ta shirya sane, ta kaisa wajan Malam Sani, ita kuma ta tafi gyaran dakin Aunty Hajara.

Bayan azahar ta gama komi da zatayi, har abincin rana tayi. Ta kuma gyara wajansu, itama tayi wanka. Dokin dawowan Kausar kawai takeyi.

Ta amso Amjad suka zauna ata inda zasu dunga ganin shige da ficen da za'ayi ta wajan gate. Kawai tunanin irin tarban da zata bata takeyi, da yacca Kausar din zata cikata da surutu, akwai mutane da dama da take san taji ya suke. Tasan yau kam indai ba bacci Kausar tayi ba, ba zata samu sa'idar surutunta ba.

Ta saki murmushi tare da fadin, "My parrot". Haka taci gaba da zaman jiran tsammani har uku saura sannan taji an bude gate din da sauri ta mike tsaye tana kuma janyo Amjad tare da fadin

"Our sis is back" shi kuwa sai dariya, ganin yacca take masa murmushi.

In kaga yacca Sanah takeyi, zaka sha mamaki, kallo daya ya wadatar ya fassara maka yanayin jin dadin da zuciyan ta yake ciki. Kai ba zakace wannan Sanah din bace mai zama shuru waje daya, most of the times, zaka ganta a zaune, ka same ta, tabar duniyan mutane ta tafi na tunani, Sanah din da bata da wani kuzari ko laka a jikin ta. Amman kuma yunzu duk sabanin hakan ne tattare da ita.

Uwa ta janyo motar ya gama shigowa ciki take ji. Haka ta tsaya tana kallo har sukayi parking kafin Taga na ciki sun fara fitowa. Sameer yai cikin gida da gudu, Hafsa tana tafiya uwa zata balle, sai Baffa daya fito a mazaunin driver sai kuma Aunty Salima.

Sanah ta kuma wara idanuwan ta, tana tunanin ta inda Kausar zata billo, amman kuma babu ita babu dalilin ta.

Taji zuciyarta ya buga da karfi da sauri. Kaddai a makaranta suka barota, wani tunanin ya gaya mata. To in a makaranta suka barta menene dalilin su, nayin hakan, kamar Kausar maima ta sani a wajan gida.

MARAICHIWhere stories live. Discover now