Maraichi____
By_Nanatoou
Wattpad_@nanatoouPage_49
Muna tafiya, inna na rike dani dan jikina babu wani kwarin da zai iya dauka ta. Muna tafiya zuciyata na duka kamar ana daka sakwara. Fargaba cike a raina. Wani bene mukabi, kafin daga bisani muzo wani waje da rubutun ya saka zuciyata tsayawa. ICU, inda nake fatan ubangiji karya kuma kawoni, wajan da bazan iya mantawa da shi ba a cikin tarihin rayuwata. Me Sanah takeyi a ICU, shine tambayar da tazo min, amman kuma ina addu'ar Allah yasa hanyace zamu billa ta wajan. Addu'ata ta katse ne yayin da mukaja buri a kofar wani daki. Na daga kai na kalli inna, itama idanunta suna kaina. Amman sai taja hannuna yayin da muka karasa wajan wani transparent glass. Dakyar na iya daga idanuna, na kalli cikin wajan, yare da jan numfashi mai tsayi, dan bansan mai zanyi arba dashi ba.
Nai saurin dafa Inna, itama ta rikeni dakyau sakamakon jirin da ya debeni, bayan nayi ganin da bana fata. Kusan komai nawa sai daya kusan tsayawa, zafin da zuciyata keyimin ya kuma karuwa, naji ana sokamin mashi a zuciya ta.
Ba tare dana rasa kallo koda na kiftawar idoba, haka na kafe cikin dakin da idanuwa. Ina kallan yar uwata da take kwance sanye da rigan asibiti, ga tanan ko motsi batayi tamkar wata gawa. Ga oxygen nan a fuskarta, hannun ta sanye da drip, ga computers nan da suke nuna bugawar zuciyar ta. Na kasa dauke idanuna a kanta ba tare da na kifta koda sau daya bane.
Wannan situation din da suke gaba na shiya faru shekara daya da wani abin. Wannan shine yacca muke tsyuwa muna kallan mahaifiyar mu. Abinda kawai ya canza shine wancan karan Mummy ce a kwance akan gadon, yayin na nida Sanah muke tare muna kallan ta daga waje. Har yunzu ina tina yacca muke bakin cikin ganin mahaifiyarmu a wannan yanayin, yacca muma shiga damuwa, bama san mu rasa ta, amman kuma daga karshe sai data tafi ta barmu.
A yunzu kuma Sanahce a kwance tamkar matacciya, yayin da ni kuma nake tsaye a waje nake kallan ta, dauke da kunar zuciya da rashin madafa.
Ban san iya lokacin da muka dauka a haka a tsaye ba, nasan dai kawai naji Inna ta fara tafiya dani. Ban san a yanayin da nake ciki ba, amman dai nasan wannan da take tare da Inna, bani bace. Tunda bazan iya fadar mai zuciyata take ciki ba, ba kuma zan iya aikata komai ba, ko da muka bar wajan dakin, image daya ne kawai yake displaying a idona, shine Sanah da take kwance, sai kuma ta juye min ta koma min Mummy. Kwakwalwata ma, nasan cewa bata functioning a wannan gabar.
Ban san yacca muka karasa daki ba, amman na san dai Inna ta maidani ta kwantar, yayin dana cigaba da ganin wannan hoton dai.
I need to fight koma menene ya same ni a yunzu, amman kuma I'm already weak bazan iya ba. Lokaci guda kuma image din da ake raping Sanah a dawo min.
Yacca nake a kwancan, a haka nake sai kurawa ceiling ido da nayi kawai, sannan komai yana dawomin, amman kuma bana jin wani emotions. Abu daya nake ji shine weak and broken.
Ban san mai nayi ba, amman sai naji ana ta jijjigani, idonuwana suka sauka akan inna barira, da hawaye ke zubo mata daga idanuwa suka sauka a kuncin ta. Gashi dai kamar abu take cewa amman everything was mute, bana jin komai. Ina a haka naga an rufeni, mutane sun zagayeni, kafin daga bisani suhau dannamin kirji dakyar, daga haka kuma ban muka sanin abin dayake faruwa ba.
Sanda na kuma tashi kuwa, bana uhm, ban uhm'uhm. Kowa dai dai na bisa da idanuwa, amman ina jin yacca kirjina yake yi min zafi. Inna tana iyaka bakin kokarinta a kaina. Ina kallan yacca matan dakin zasuyi tayi min sannu, kowa yana bina da kallan tausayi, amman ni kuma sai dai kawai na bisu da ido, ina kallan bakin su.
Yawanci kuma daga kwancan da nake, sai dai na rufe idanuwa na, in tayin tunani, mai mukayi daya munanta haka a rayuwa. Haka zanta tunani zuciyata tanayi min kamar ta fashe.

KAMU SEDANG MEMBACA
MARAICHI
Fiksi UmumWe were gloomy after the death of our parents. All we need is even a bit of slightly light, but things fall apart. When things became dreadful, there's some hint of conceal deeds. The revelation goes with the end of our disastrous life. But how, whe...