page_63

128 22 8
                                    

Pg_63

Bansan ya akayi ba dai, yacca ya Umar ya tafi, sai ya barni tsaye a wajan tare da wani irin feeling a zuciya ta. Sosai nake jin karayar zuciya a tattare Dani. Sannan wani guilty conscience ya rufe ni.

Nasan ba laifin sa bane, Amman me ya saka muka tsaurara Abin. Wata zuciyar ta bani Amsa cewa saboda uwar sa ne.

Nai saurin toshe duk wata kafa da zata kuma sakani in zargi kaina a halin da take ciki, na karfafawa kaina gwiwa tare da binsa da addu'a. Nasan hakan ne alheri a tattare da su.

Banyi aune ba sai ga Yasmeen tazo, tana tafiya dakyar ta dubeni tare da fadin, "kin wahalar Dani wallahi, sai neman ki akeyi".

Na kalle ta tare da gyada kaina nayi gaba, ta biyoni muka nufi gida.

A sitting room din baba muka tarar da su. Sanah tana zaune a kasa lullube cikin laffaya, ko alamun fuskarta ba'a gani.

Baba Kuma sai nasiha take yi Mata.
Nan dai bayan ya gama, su maman Hamza suka kamata, tare da Mata guda biyu da suka zo tafiya da ita suka fita.

Na tsaya a wajan a raina ina raya cewa yunzu shikenan da gaske mun rabu yau ba zamu kwana tare ba.

Yasmeen ta fisgo hannuna mu kayi hanyar waje tana fadin, "ke wallahi kina da matsala kina tsaye  anan wajan sai an tafi an barmu dan ba tsayamu zasuyi ba".

Muna fita muka fada wata mota daya daga cikin ukun da suke waje a lokacin. Bayan mu wasu Mata biyu suka shigo wayanda kawayen maman Hamza ne daga Nan dai drivern mitan yaha muka tafi.

Tafiya sosai akayi, wacca bahaushe take kiranta uwa ta yada shege. Kawai baza idanuwa nayi Ina bin titi da kallo, Dan Yar sai da mukayi hanyar fita daga kaduna, acan wani sabuwar unguwa Mai dai dai Kun mutane suke, Nan mukayi. Sannan motar mu ta kutsa cikin wani gida da gate dinsa take a wangale.

Muna fita suka soma sakar guda, hi Jake ayyiriyiriyiriririiiiiiiiiiiiiii, ta ko Ina.

Muna tsaye aka fito da Sanah daga mota, sannan sukayi cikin gidan, kawayen maman Hamza suna ta yaba mata.

Sai da suka gama shigewa cikin gidan sannan na soma bin compound din da kallo wandafitilu suka haske ta ko Ina. Ba karya daman Khamees ko Banga idansa ba nasan Dan karyane Mai San nuna shi takai wajan ko Kuma ya wuce, tunda tun farkon haduwar mu dashi har zuwa wannan lokacin Wasa yake da kudi.

Yasmeen ta Kuma tsaki tana Jan hannuna mukayi cikin gidan. Bamu tsaya ako Ina ba sai da muka dangana har Daman bene cikin wani daki inda nan muka tarar da aka sarin mutane.

Sanah zaune a gefe gado har yunzu a lullube fuskarta yake.

Wata Mata dafa cikin matan da sukaje dauko ta, ita ke Mata nasiha a yunzu. Bata ja da nisa ba, suka muke tare da fatan Allah ya bada zaman lafiya suka fice.

Sai da suka gama tafiya sannan maman Hamza ta soma Bata nasihan Wai Allah ya kawo Sanah gidan arziki ta saki jiki taci arziki tabar arziki a mazaunin sa.

Ita da kawayen ta kowa na fadin Albarkacin bakinsa bayan wasu mintuna Kuma maman Hamza ta Mike tare da fadin, to dare yariga yayi, mu bara mu wuce, Allah bada zaman lafiya.

Ta dakata ta dubeni nida Yasmeen mun arabe a gefe sannan tace Mana muyi sallama da Sanah mu fito mu wuce.

Naji zuciyata ta doka da karfi,da gsake. Dai tafiya zamuyi mu barta ita daya.

Suka fice suka barmu mu daya a wajan. Ahankula na karasa na zauna kusa da ita tare da kwantar da jikina a barin jikin ta. Nan naji alamun sheshekarta, tana kuka. Zuciyata ta Kuma raunana.

Na saka hannuna na kamo hannunta na rike shi Gam, Ina jin a Raina bana san na rabu da wannan halittar, ita din wata barice ta rayuwata.

Yasmeen ta dafa kafada ta, yayin dana lumshe idanuwana Ina Kuna jin Ina ma dai Ina ma. Amman aikin gama ya riga daya gama.

MARAICHIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora