2

4 0 0
                                    


Karfe 12:30 jirginsu ya sauka a babban airport Nnamdi azikwe international airport dake garin abuja
Bata sha wahala ba gurin daukar trollies din da ke baba yasa a ji da wannan

Fitowa tayi ta arrivals nan ta hango baba tsaye yana kalle kalle ko zai hango ta
Babana ta fada da karfi tare da karasawa inda suke da gudu
Rungume juna sukayi nan take ta saki kuka
Haba my darling kukan me kike
I missed you so much baba
Missed you more ba gashi kin dawo mun hadu ba
Zan haka mamanki na gida Tana jiranki oya mu tafi
Janye jikin ta tayi daga nashi suka karasa inda akayi parking motar su kirar Range Rover 2021 edition
Bude musu kofa driver yayi suka shige
Ko a motar ma kukan shagwaba ta cigaba dayi ita a dole sai an rarrashe ta haka kuwa akayi har suka karasa Gidansu dake Maitama Abuja
Baba na rarrashin ta sai da kyar tayi shiru
Ko da suka karasa wangale musu makeken gate akayi
Parking motar akayi driver ya fito ya bude musu kofa
Dai dai lokacin wata mata ta fito wadda bazata wuce shekara 45-50 ba fara ce sai dai ba cen ba kana ganinta zaka gane kamar ta da hafsah sanye da abaya black
Da gudu hafsah ta karasa tana fadin
Mamana
Rungume juna sukayi nan fa ta saki sabon kuka
Aa mene na kuka koma kinga mtls ta da ke abu kadan sai ki sa kuka indai kuka Zaki mun toh ki koma
Haba mama yahakuri
Ta fada Tana goge hawayen dake zuba
Mama ya aysha ta zo
Aa tana hanya dai
Dukansu shiga ciki sukayi zuwa babban parlor su da yasha royal chairs

Fitowa tayi ta arrivals nan ta hango baba tsaye yana kalle kalle ko zai hango ta Babana ta fada da karfi tare da karasawa inda suke da gudu Rungume juna sukayi nan take ta saki kuka Haba my darling kukan me kikeI missed you so much baba Missed you...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Nusaiba nusaiba fito da abinci ki tawo da ruwa
Cewar mama dake shirin zama
Ya karatu
Alhamdulillah baba amma karatu da wahala
Dama yanxu me yake da sauki ay babu
Fada mata dai kullum complain dinta kenan karatu da wahala toh ne yake da sauki a Wannan rayuwar ay sai godiyar Allah kawai
Yanxu dai ki tashi ki wanka ki zo ga abinci nan kafin nan aysha ta karaso
What about my bags
Sani zai kawo miki Su already ya tawo daga airport

Tashi tayi ta haura sama zuwa dakin ta
Ko da ta shiga a gyara ta kanshi kamar daxu ta fita
Wardrobe din ta ta bude ta ciro bubu da hula sannan ta shige toilet....

                            Shine Wace Hafsah?

Hafsah Ibrahim Dahiru Shine cikakken sunanta diya ga Ibrahim Dahiru shaharrarn dan siya koma Senator a garin Abuja sannan koma hamshakin me kudi
Yana da mata daya hajiya zulaiha da yara biyu Mata ta farko aysha me shekara 25 wadda ta ke auren da aure sai Hafsah me shekaru 23 da ta ke karatu a kasar turkey istanbul tana final year inda take karanatr history
Dukkansu mamansu suka dauko a kyau dayake asalin yar maiduguri ce wato shuwa-arab
Sun kasance farare sal kamar ka taba su jini ya fito ga hanci da koma manyan idanu sai doguwar fuska da gashi har gadon baya....
Wannan kenan a takaice.

Yana zaune a office dinsa ya dora kafa daya kan daya yana sipping tea a hankali
Sir yosuf is calling
Jin sunan da aka Kira yasa shi amsar wayar ba shiri
Hello sir jirginsu ya sauka yanxunan she will be at home in the next 30 minutes
Kashe wayar yayi ba tare da yace komai ba ya ajje gefe
Ya dade bai ji lbr da ya mishi dadi kamar Wannan ba
Haka koma ya dade bai ji fargaba da tsoro kamar yau ba
Get the cars ready
Ya fada batare da ya juya ba
Bai dade da fadar hakan ba ya tashi zuwa waje inda akayi parking mota guda biyu daya aka bude mishi ya shiga suka wuce
Basu tsaya ko Ina ba sai wani hamshakin gida dake unguwar asokoro
Ko da suka je gate a bude yake suka shiga
Gidan babba ne sosai don kafin kaga karshe shi sai dai a mota
Zagaye yake da flowers abun shaawa
Parking motar akayi ya bude yana shirin fitowa
Wata yarinya ta fito ta wata kofa yar kimanin shekara 9 ta tawo a guje tana fadin
Daddy oyoyo
Oyoyo my princess
daukar ta yayi cak suka shige cikin wani hadadden royal living room wato parlor
Kan kujera ya ajje ta shi ma ya zauna gefe
Daddy when are we visiting grandma I miss her so much
Kin ci abinci
Yes
Homework kin gama
No dady sai anjima
Ki gama homework ki shirya na kaiki
Daddy I love you so much
Ta fada hakan tare da mikewa a guje tare da shigewa wata kofa
Wayarshi dake gefe ya dauko tare da dialing wata numb da akayi saving kamar haka "Momma💕"
Ringing biyu aka dauka
Momma Ina wuni
Lfy Kalau ya Munira
Tana lfy yanxu ma take mun mgnr sai na kawo ta nace ta gama homework tukunnan sai mu zo if possible ma sai ta dan kwana biyu nan
Yanxu kuwa nake zan cen ku a raina toh Allah ya kawo ku lfy y aiki?
Alhamdulillah
Allah yayi jagora dafatan dai ka rage damuwar da kake sa kanka ya kamata kayi wa kanka fada Kai yanxu fa ba yaro bane bai kamata ka dinga damuwa akan wani abu da Baka tabbass a kanshi ba ka sa zuciyar ka salama indai Hafsah ce Allah ya Riga da ya dauke abar sa duk son da muke mata bazai kai wand Allah ya ke mata ba koma kuwa yana mata kyakyawan fata bai kamata ka zaba mata tawakkali ba Idan kayi hakan kuwa zaka zama butulu
Shiru yayi bai ce komai ba sai hawaye dake zuba a idonsa
In sha Allah momma sai mun zo
Yana fadin hakan ya kashe wayar tare da ajje wa gefe ya tashi zuwa sama.....

                     Shin wane wannan mutumin?

Abdoulfatah Lawal mangal kenan me shekaru 44
Da ga Lawal mangal da koma hajiya habiba
Shi kadai ne a gurin mahaifinsa da koma mahaifiyar sa
Ya kasance shaharren dan kasuwa me tarin dukiya da arziki ya koma gado hakanne daga gurin babanshi domin suna daya dagacikin manya masu kudi na Africa baki daya
Suna da company da suke producing Abubuwa kala kala a kasashe daban daban haka koma a gida Nigeria
Ya Kasance mutum me saukin kai me dadin mu'ammula da mutane
Yayi aure yana da shekaru 33 inda ya auri Hafsah diya ga Present President of Nigeria Isa bokari
Sunyi shekara biyu da aure kafin su Haiti yarinya mace da aka sa mata suna Habiba ake kiran ta da Munira sai dai koma Allah ne yin yadda yaso a gurin haihuwa habiba ta rasu ta koma ga Wanda yayi mu duka
Tun bayan faruwar hakan rayuwar Abdoulfatah ta canza baki daya dukkan wani farinciki a rayuwarsa ya goshe bashi da aiki sai kuka da kiran sunan Matar sa Hafsah
Ganin haka yasa Hajiya Habiba shiga cikin damuwa
Duk wani Abu da zasuyi ganin ya kwantar da hankalinshi ammma ya citura sai da su dangana ga wani babban malami dake garin Kano inda ake amso masa rubuta yake sha sai a hankali  rayuwarsa ta fara dawowa daidai duk ta bbu walwala ko annuri a tattare dashi haka rayuwa ta cigaba inda shi ya dage zai raini yarinyar domin a cewar sa ita kadai ce abunda zai gani ya tuna Matarsa wadda yaso da dukkan zuciyar sa... ya koma yi alkawarin bazai taba son wata ba balle ya ce zai aure ta
Sai dai koma abunda kake tsarawa daban da abunda qaddara ta rubuta daban
Bai taba tunanin son wata ko tunanin wata ba sai a ranar da ya hadu da Hafsah Ibrahim Dahiru
Bai taba tunanin zai so ta ba sai da yaji sunanta daya Matar shi amma duk da haka yayi yaki da zuciyar shi gurin cire ta a ranshi amma hakan duk a banza......

Wannan kenan a takaice......

Hafsah

Comments, like & share

Hafsah Where stories live. Discover now