7

1 0 0
                                    



"Zabi ya rage naki hafsah kin fi kowa sanin bazan taba miki dole ba koda kuwa akan raywar ki ne sai dai ni me Baki shawara ne domin kuwa a rayuwa baka samun dama sau biyu dama daya ce yake zuwa ma a rayuwa Idan har kana da rabo sai kayi amfani da ita Idan koma baka da rabo toh shkn ta wuce ka duk karfin ka duk kudin ka, haka koma dukkan abun da zai biyo baya toh kasan wanda ka samu ne ina mai baki shawara a matsayi na na mahaifin ki me  son cigaban ki , Idan har kika amince zan fi kowa farinciki sai dai Idan har hakan zai cutar dake toh kuwa zai zamar mun babban bakinci ki a rayuwa "
Baba ya karasa fadin haka yana maida kallon sa kan hafsah dake kasa
"Ni kaina zan yi farinciki da amincewar ki sai dai koma bazan so a miki abunda bakye so ba, Wannan rayuwar ki ce aure rayuwa ce da bbu wanda yake son barin ta Idan har yayi ta sai mutuwa, dukkan mu nan bbu wanda zai zauna miki da mutuminnan ke Zaki zauna dashi haka koma ke Zaki rayuwa dashi, karki yarda da wannan saboda mu domin kuwa rayuwar ki ce karki yarda da wannan saboda farincikin mu ke koma ki rusa naki, aure rayuwa ce ne dogon zango ne cike da kalubale karki yarda da wannan saboda wani dalili ba don ya kwanta miki ba Idan har kinji ko da kadan bakya sonsa ko baiyi miki ba ki fada Ina miki alqawarin cewar an bar mgnr nan ko da wasa bazaa sake tayar da ita ba"
Granny ta fada ita ma kallon ta na kan hafsah

Taji abunda dukkansu suka fada sai dai bata da zabi bata da farincikin da ya wuce naso a rayuwa bata taba neman abu ta rasa daga gurinsu ba, Taya zata ce musu Aa?  da wane ido zata kalle su ta ce Aa?
Ajiyar numfashi tayi kafin tace
"Baba na yarda zabinka shine nawa"
Dukkansu kallon ta suke kafin yace
"Aa hafsah karki yarda da wannan saboda ina so hakan sam bazai mun dadi ba kina bukatar lokaci kiyi tunani?"
Girgiza kai tayi tana fadin
"har cikin zuciyata naji yayi mun ni kaina shaida ce kan halayansa masu kyau duk da bansanshi ba sai dai nakan ji sunanshi gurin mutane, ina koma fatan hakan ya zama alkhairi a garemu baki daya "
"Alhamdulillah Alhamdulillah naji dadin jin wannan zance kwarai Allah ya miki albarka "
"Ameen Ameen"  tana fadin haka ta tashi tare da barin gurin
Ko da ta isa dakinta zama tayi tana tunanin kala kala lokaci guda hawaye suka fara anbaliya a fuskar ta
Yanxu shkn duk dreams din da take dashi ya rushe? Zata auri wanda bata sani ba? zata auri wanda ba soyayya tsakaninsu?
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai take maimaitawa a zuciyar ta gaba daya
Jin mutum na shirin shigowa dakinta tayi saurin goge hawayen dake fuskar ta tare da gyara zaman ta
Granny ce ta shigo tare da rufe kofar dakin
Hafsah! Hafsah! Hafsah! Sau nawa na kira ki?
Uku
Kina son aurennan
Dagowa tayi ta kalle ta kafin ta gyada Kai alamar Eh
Hafsah knn bani na haife ki ba amma tabbass nasan halinki fiye da kowa tun Kina cikin zani nake rike da ke har girma yazo miki ki sani aure ba abun wasa bane aure yafi a yi wasa dashi rayuwa ce cike da kalubale kala kala kowacce mace da nata mtlsr bbu rayuwa ce me cike da abubuawa iri daban daban sai wanda kika sani ba wai Ina fada miki haka bane saboda na tsorotar dake sai dai Ina fada miki a matsayin a na me son cigaban ki, aure rayuwa ce me dadi wadda ake Gina ta cike da soyayya da kaunar juna rayuwa ce me dadi ta samun yanci rayuwa ce da kowacce mace ke fatan samu har ma mazan duk da kalubalen dake cikinta hakan bai hana ta zama rayuwa me dadi da kwanciyar hankali ba sai dai hakan zai faru ne Idan har kikayi da cen miji shi ma koma yayi da cen mata Ina koma kyautata zaton wannan mutumin yana da duk wani qualities da mace zata bukata gurin namiji amma duk da hakan bazaa samu kwanciyar hankali da fahimtar juna ba Idan har ke baki sonshi kin aure shi ne saboda mu ko mahaifinki, ki sani fa wannan ne chance dinki na gyara rayuwarki wannan ne kadai chance dinki na gyara rayuwarki na gaba domin kuwa yanxu ta wuce toh shkn baki da wata dama na fadar raayinki duk yadda zamu so ki dashi Idan har bai kwanta miki ba ko Kina da wani daban da kike so toh fa mu kanmu abun bazai mana dadi ba asking you for the last time do you like him?
Shiru tayi da wasu minutes before tace
Granny ke da kanki kin yabe shi kin koma yarda da nagartarshi haka ma baba duk da bansanshi ba amma na kanki kyawawan ayyukansa Ina koma kyautat zaton nan ba dadewa zan so shi kamar yadda ya furta yana so na
Tabbass naji dadin Jin hakan daga gare ki Allah ya miki albarka ni yanxu zan fita gobe babanki yace zai turo shi ko gaisa hakan yayi miki yazo din?
Girgiza kai tayi alamar eh

..............................................

Haka mukayi dashi ya koma ce gobe na tura ka gidan hajiyarsu tana cen kaje ku gaisa
Dadi kamar ya kashe shi ya rasa me zaiyi bai taba tunanin zata yarda da amince mishi ba amma tayi hakan sai dai baisan dalinlinta ba kashe shi baba yayi da cewar
Amma ka tabbata ka fada mata ko kai wane sannan koma ka sanar da ita mgnr Munira
In sha Allah
Toh zaka iya tafiya
Baba a dawo lafiya
Allah yasa ka gaishe da Munira
Zata ji
Fita yau ranshi fal rabonshi da yaji irin wannan farinciki ya manta burinshi na shekaru ya kusa cika sai dai fargabar shi daya ya fada mata shine wanda ta dade tana nema? ko kowa ya yi shiru? gaba daya kanshi ya kulle

Hafsah

Comments like & share

Hafsah Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum