9

2 1 0
                                    



Amma a ina ka taba ganina?
Murmushi yayi tare da cewa na dade da saninki sai dai Allah baiyi zaki ganni ba sai yau duk wannan ba shine abun tambaya ba idan akwai abunda baki gane ba game da abubuwan da na fada ki tambaya kai tsaye ina koma sauraron jin naki bayanin
... duk wani abu da ya kamata kasani alamomi sun nuna ka sani sai dai bansani ko akwai wani abun da kake da bukatar sani
Abubuwa biyu nake da bukatar sani a gurinki na farko kamar yadda na fada miki ni ba yaro bane ba koma wasa ko bata lokaci ne ya kawo ni gurinki ba ina so naji daga bakinki cewar ba dole aka miki da ki amince da wannan auren ba ina fatan ba dole aka miki ba
Shiru tayi kafin tace
Bbu wanda ya mun dole hasali ma an bani option sai dai koma bazan taba iya cewa baba na Aa ba ko da kuwa abunda yazo dashi baiyi mun ba na koma yi imanin cewar bazai taba zabar mun abunda zai zama cuta a gareni ba
Naji dadin jin hakan domin a yadda zamani ya lalace ba kuwa ne zai iya hakan ba hakan ya nuna mun irin tarbiyar da kike dashi, sai koma abu na biyo Kina da saurayi? Ko kina da wanda kike so??
Numfasawa tayi tana fadin banda saurayi bani koma da wanda nake so
Baki taba yin saurayi ko da sau daya ba a rayuwarki?
Nayi a school
Me ya rabaki dashi?
Mutuwa yayi kashe shi yayi, ta fadi hakan fuskarta cike da tsoro
lokaci guda yaji zuciyar shi ta tsananta bugawa
Ya kasheshi wa knn?
Sai a lokacin tayi realizing abunda ta furta
Uhmm bansani ba Nima haka naji lbr daga gurin yen uwanshi
Allah ya jikanshi ya mishi rahama
Ameen ya rahman
Shiru sukayi na wasu minutes kafin yace
Ina neman wata alfarma gurinki
Ina ji
Yaushe zaki koma school?
Nan da 1month
MashaAllah ina so ki yarda a daura aure a koma kawo lefe kafin ki koma Idan yaso kika dawo duk wani taro da ya kamata ayi sai ayi amma Idan har hakan baiyi miki toh bazan takura miki ba
Shiru tayi tana nazarin mgnr sa kafin tace
Allah yasa hakanne mafi alkhairi
Ameen Ameen
Kallon watch din dake hannunsa yayi ganin time ya saka shi tashi yana fadin
Zan tafi yanxu Munira na jirana bazatayi bacci ba sai na koma
Oky toh ka gaishe ta
Zata ji
Hanyar fita yayi tana biye dashi sai da suka zo dab da kofa tace
Yaushe zaa kawo ta gurina?
Wa knn?
Munira
Dan murmushi yayi yana fadin when are you free
Uhm gobe zan koma gida so probably jibi
In sha Allah if I'm free I'll bring her myself
Oky Allah ay kaimu
Sai da ya fita sannan ta koma zuwa dakin granny
Ya kukayi dashi?
Yanxu granny wai duk mgn da mukayi zan fada miki? Ta fada Tana dariya
Au tun yanxu an fara boye boye
Haba granny na isa na boye miki abu kawai dai ya bukaci da na yarda a daura auren kafin na koma school in na dawo yaso Idan akwai abinda ya kamata ayi sai ayi
MashaAllah naji dadin hakan kuwa sosai
Hira suka cigaba da yi na dan wani lokaci kafin ta tashi zuwa dakinta
Da isar ta ta tarar da wayar ta na ringing dauka tayi ganin sunan dake kan screen yasa gabanta faduwa
Kar dai yaji lbr aurena? tambayar da tayi wa kanta knn kallon wayar ta cigaba dayi har ta katse aka sake kira
Dagawa tayi batare da tace komai
Hello Sarauniya ta
Still shiru bata amsa ba
Yau koma ba mgn ko nayi lefi ne?
Kaga malam daga yau karka sake kirana domin kuwa a yanxu tamkar matar aure nake yen kwanaki ne suka rage na zama matar wanda nakeso koma na zaba dan haka ka daina batawa kanka lokaci
Dariya yayi sannan yace kika ce wanda kika zaba ko dai wanda aka zaba miki
Wannan koma bai shafe ka ba domin kuwa yayi mun ya koma kwanta mun a rai shi koma nake so nake koma fatan ya zama mijina danAllah dan annabi ka kyeleni me nayi ma ne? Wannan wane irin so ne cike da mugunta Idan har ka isa namiji ka fito na ganka sannan koma ka sani wlh tallahi Idan wani abu ya faru dashi har abada bazan yafe ma ba koma koma ka sani duk abunda ya faru da kai kayi kuka da kanka
Bata jira amsar sa ba ta kashe
Yanxu tuninta nine na kashe Mahish? Tambayar da yayiwa Kansa knn domin yasan ba shi ya kashe shi ba accident yayi abun koma yazo da karar kwana amma tunaninta nine na kashe shi?? ajiyar zuciya yayi lokaci guda koma ya saki murmushi
Ta fadi hakan ne saboda ta razana shi ko kuwa har zuciyar ta tana sonshi? ita kadai zata iya amsa haka sai dai koma yasan bashi da tabbacin samun amsa


Wahse gari misalin karfe 4 na yamma ta gama hada kayanta a cikin trolley da taxo dashi sannan ta yafa mayafin abaya da ta sa ta fito
Bata ga granny a parlor ba hakan ya saka ta shiga Dayan parlor nan ma bata nan
Fitowa tayi zuwa dan garamin garden din ta inda take shuke-shuke nan kuwa ta tarar da ita
Har kin fito
Eh granny mama na jirana
Toh Alllah ya kiyaye hanya ki gaishe su sai yaushe koma?
In sha Allah kafin na tafi zan dawo ay in sha Allah
Toh Allah ya tabbatar ki gaishe da mutan gidan sai nazo
Toh granny ta fada tare da rungume ta

Bakin motarta ta isa tare da bude backseat ta saka trolly sannan ta shiga gaba
Bude mata gate akayi ta fita a supermarket ta tsaya ta siyo ice cream tana sha tare da driving har ta isa gida....

Hafsah

Comments like & share





Hafsah hafsah hafsah

🫶🫶

Hafsah Where stories live. Discover now