8

3 1 0
                                    





Kamar ko yaushe misalin karfe 11 na safe ta tashi da ga bacci wayar ta da ke gefe ta sa hannu ta dauko
cin karo tayi da message from mr unknown da ya turo mata jiya da dare dan karamin tsaki tayi tare da ajje wayar gefe dai dai lokacin wani message din ya shigo ko bata duba ba tasan wane ya turo ta koma gama haddace dukkan kalamansa da texts dinsa
Tashi tayi zuwa toilet tai wanka ta fito sanye da towel
kan dressing table ta zauna sai da ta gama abunda take tsaf sannan ta tashi zuwa bakin wardrobe light color English abaya ta saka tare da saka hula kalar kayan
fitowa tayi tun daga stairs ta fara kiran Granny karaf kuwa ta amsa tana fadin hansatu kin tashi?
Yessss granny Kina Ina? Ina kitchen ki karaso
Bata ce komai ba ta karasa ta same ta
tarar da ita tayi tare da daya daga cikin masu aikinta suna preparing breakfast as usual
Karasawa tayi ta taya su......

Bayan sun gama breakfast ne ta tashi zuwa dakinta
mayafin Abaya ta saka tare da daukar keys din motar ta da jakarta ta fito
Sallama tayiwa granny sannan ta fito
bata tsaya ko Ina ba sai a gidan ya aysha dake Maitama, horn tayi gateman ya bude ta shiga parking tayi ta fito tare da shiga kofar da zata kai ta parlor
Koda ta shiga tarar da masu aiki tayi suna shara
Gaisheta sukayi ta amsa sannan ta hau stairs zuwa sama parlor dake farko ta shiga tare da zama
Numb ya aysha tayi dialing ring daya ta dauka
Ya aysha na karaso fa
Toh gani nan kina kasa?
Aa Ina parlor sama na farko kasan daga shara suke
Toh gani nan
Bata dade da ajje wayar ba ta shigo dauke da murmushi a fuskar ta
rungume juna sukayi kafin kowacce ta nemi guri ta zauna nan fa hira ta barke kamar wadanda sukayi shekaru basu hadu ba
Ni ko hafsah na tambaye ki
Ina ji
Toh wai kinsan shi wanda Baba yake shirin hadaki dashi? Kin gane shi?
Aa bansanshi ba balle nagane shi
Hafsah aure fa ba wasa bane baa taba samun kwanciyar hankali Idan har bbu soyayya tsakanin maaurata ina koma da tabbacin baba ya baki zabi domin ko me zai faru bazai taba miki dole ba
Yesss he did give me option amma ya aysha ta ya zan ce bana so? sanin kanki ne bbu wani abu da muka taba nema a duniya muka rasa duk girmansa haka koma duk kankantarsa bamu taba nema abu koda da kwayar zarra a gurin baba mun rasa ba duk wani farinciki yana bamu, da wane idon zan kalleshi nace abunda yazo dashi baiyi mun ba? I can't turn him down
Duk mgnr ki nagane ta na koma gane inda kika nufa ni kaina bazan iya hakan ba amma aure rayuwa ce da Idan ba kaf data ba bbu abunda zai raba ki da shi aure ba wai karatu bane da zakaje kayi na yen shekaru ka dawo gida daga ranar da aka daura miki aure toh fa kin koma karkashin wani shi yake da iko akan komai naki hafsah ina mai shawartarki da Idan kikaji wani abun a ranki bayan kun hadu ko kikaji baiyi miki ba ko kadan toh ki sanar da mama ko baba duk da nasan zakiji nauyin hakan amma ki sani wannan ne damar ki na karshe da Zaki iya canza raayinki Idan har hakan ya wuce toh kuwa duk abunda ya biyo baya dole ki hakura dashi
Numfasawa tayi kafin tace
In sha Allah hakan bazata faru ba
Allah yasa yanxu bari nake nasan yanxu zai fita sai na dawo
Ki gaishe shi


Sai dab da magribh ta bar gidan bata tsaya ko ina ba sai gidan granny
Sai yanxu zaki dawo kinsan na fada miki yau zai zo ku hadu kuga juna amma sai yanxu zaki shigo tukkunna ma ina kika je
Haba granny gidan ya aysha fa naje koma Ina ji kika je sai bayan isha zai zo
Toh uwar mgn tsayawa zakiyi kina bayani ko shigewa zaki tunda zaman jiranki zaiyi
Shigewa tayi bata ce komai ba
Wanka ta karayi ta fito wardrobe dinta ta bude ta fara neman wane kaya zata da
ta dade tsaye tana dube dube har wayarta ta fara karar kiran sallah Subhanallahi ta furta tare da ciro free doguwar riga ta lace

Hijab ta dauka tai sallah sannan ta cire ta karasa dressing mirror turare da fesa sannan ta shafa lipstick ta koma ta zauna Karfe 8:40 dai dai granny ta shigo tana fadin Yaxo yana parlor kasa ki tashi kije toh a haka zaki tafi bbu dankwali? wani s...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Hijab ta dauka tai sallah sannan ta cire ta karasa dressing mirror turare da fesa sannan ta shafa lipstick ta koma ta zauna
Karfe 8:40 dai dai granny ta shigo tana fadin
Yaxo yana parlor kasa ki tashi kije toh a haka zaki tafi bbu dankwali? wani sabon salo ne hakan
Dau rawa fa zanyi
ki sauri dai yana jiranki
Bata kara mgn ba ta fice daura danwalin tayi sanna ta yafa mayafi ta fito
tun daga stairs ta hangoshi sai dai ya juyar da fuskar sa gefe
Abdoulfatah kuwa tun daga nesa ya jiyo kanshin turaren ta sai dai bai dago ba domin bugun zuciyarshi kara tsananta yayi shi kanshi baisan dalilin hakan ba
Yana jin motsinta har ta nemi guri nesa dashi ta zauna tare da gaishe shi cikin sassanyar muryar ta
Amsawa yayi tare da dagowa
Kallonshi tayi da mamaki ganin mutumin da ta hadu dashi jiya a orphanage
kai  ne......
bata karasawa ba ya katse ta da cewar Eh nine
Lokacin guda muryar shi ta fara registering a kanta Jin muryar da ta sani sai dai koma bazata tantance a ina ba amma tabbass she's familiar with voice
Ko batayi mgn yasan me yake ran ta sai dai koma bazai fada mata shine Mr unknown shi kanshi bai San sai zuwa yaushe zai iya furta mata hakan ba
Shiru sukayi dukkansu kafin ta katse da cewar
Uhm akwai abunda kake so a kawo ma? Ta fada tare da shirin mikewa
Aa bana son komai lokacin kawai nake bukata
Komawa tayi ta zauna tana sauraran jin abun da zai fada
Bai sai na miki dogon bayani ba nasan an sanar dake ko ni waye da koma dalilin zuwa na gurin ki sai dai wasu bayanai da ni yakamata nayi miki su
Sunana Abdoulfatah Lawal shekara ta 48 ni cikkaken dan kasuwa ne ina koma kasuwanci a kasashe da daban daban na taba aure na auri matata me suna Hafsah ta koma rasu ne sanadiyar haihuwar yar mu Munira, tun bayan rasuwar ta ni nake rainon yarinya ta sai ummana da ke tayani Wanda a yanxu tana da shekara 9 tun bayan rasuwar matata ko da sau daya ban taba tunanin kara aure ba sai da naganki na koma ji sunanki daya da matata da na rasa hakan yasa na samu mahaifinki da mgnr domin ni ba yaro bane ba koma wasa ne ya kawo ni gurinki ba ina koma fatan Kingane bayani na Idan akwai wani abu da kike da bukatar sani ki fada ke ma koma Ina sauraran jin naki bayanin

Hafsah

Comments like & share

Hafsah Where stories live. Discover now