6

1 1 0
                                    



Kwance yake kan makeken gadonsa yana ta juye juye ya rasa me ke mu shi dadi
ciwon mara ya saka shi a gaba, tun mutuwar Hafsah yake fama da wannan ciwo ya koma yi wa kansa alqawarin bazai taba aika ta zina da yer kowa ba saboda shi ma ya haifa yasan ciwon ya'ya'
danne kasan cikin yayai da yake mishi zafi kamar gurin zai fashe runtse ido yayi yana furta dukkan adduar da tazo bakinshi
ya dade a haka kafin ciwon ya lafa mishi
tashi yayi yana tafiya da kyer har ya karasa fridge madara ya dauko da ruwa da koma maganinshi
komawa yayi ya zauna ya sha maganin ya kora da madara
yayi a kalla 20 minutes a zaune kafin ciwon ya daina
Kallon time yayi 3:30 na dare
Alwala yayi ya tada sallah, sai da yayi a kalla raka'a 8 yana yi yana sallame wa kafin ya zauna
addua ya fara yana neman Allah ay shige mishi gaba kan mgnr auren sa da hafsah yau sati daya kenan da yi wa baba mgnr amma har yanxu bai ji yace komai ba duk da hakan ba mtsl bane amma yasan Idan har taki amincewa da mgnr sa toh tabbass zai shiga cikin yana yin da bazai misaltu ba
ya dade yana adduar Allah ya kawo mishi ma fita

..................................................

Karfe 12 tashi daga bacci, sakkowa tayi zuwa toilet brush ta fara kana tai wanka ta fito house wears ta saka ta fito parlor
Tarar da granny tayi tana tsintar gyada kamar yadda ta saba
Good morning granny
Morning jikalle kin tashi lafiya?
Lafiya lau Alhamdulillah
Yanxu kuwa muke mgn da babanku yace mun zai zo Anjima akwai mgnr da kuyi
Ni koma? Allah yasa ba lefi nayi ba
Kinyi wani abunne
Aa
Toh koma tunda baki komai ha ay sai mu jiran shi
Toh akwai abinci I'm starving
Ki duba kitchen akwai tea sai dai kisa a dafa miki wani abun in kina so
Hanyar kitchen din tayi batare da tace komai ba

...........................................................

Nayi matukar jin dadi da wannan zance yaushe yazo ma da mgnr?
Jiya yazo har office ya same ni karki ga yadda yake murna
MashaAllahu ashe dai zan ga bikin hafsah Ina doran duniya
Abun dadin ma shine mutum ne me hankalin gsky ga girmama magana dashi
Ay wannan kowa ma yayi mishi shaidar hakan na koma ji dadi da shi ya furta yana son ta da bakinshi tun rasuwar tshohuwar matarshi bai kara cewa yana son wata ko zai kara aure ba nasan yanxu haka cen sun fi mu farinciki jin wannan abu
Naga alamun haka sai dai wani hanzari ba gudu ba hafsah na da saurayi ko wani wanda takeso?
Anya kuwa alhaji kasan halin ya'r taka ko mgnr aure aka mata yanxu fuskar ta zata sauya ita a dole ba yanxu zatayi aure ba gashi shekaru na kara gaba 24 zatayi fah ay ni kar ma ka biye mata wai sai an bi zabin ta domin bazata yarda ba
Ay kuwa kinsan duk yadda naso ta d aurennan idan ta bude baki tace bata so to fa mgn ta kare bazan ma ta auren dole ba sai dai zan bata shawara don ba lallai ta kara samun mutumin kirki kamar shi
ni ma bazan so a mata auren dole ba sai dai karka nuna mata kana bin bayan ta nasan halin ta sarai
na rasa me ke damunta iya gwargwado dai kyau tana dashi na koma tabbata ita ke korar samari ba son ta ne baayi ba
dariya yayi kafin yace duk kyanta ta kai ki? Ya kara sa fada tare da kanne ido daya
Oh ni bazaka girma ba kai
tana fadin haka ta tashi shi ma ya bi bayan ta

...........................,...,................

Bayan ta gama break fast ta koma dakin ta
shiryawa tayi cikin shigar atampa riga da skirt

Daurin tayi ta yafa dan karamin mayafin ta tare da dauko jaka ta fito Granny ni na tafi Ina zuwa koma Yau ne fa zanje orphanage Oh haka ne na ma manta toh Allah ya kiyaye hanya amma karki dade na fada miki babanku zai zo Anjima Toh in sha Allahu s...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Daurin tayi ta yafa dan karamin mayafin ta tare da dauko jaka ta fito
Granny ni na tafi
Ina zuwa koma
Yau ne fa zanje orphanage
Oh haka ne na ma manta toh Allah ya kiyaye hanya amma karki dade na fada miki babanku zai zo Anjima
Toh in sha Allahu
side cheek kiss ta mata sannan ta fita
Motar ta ta hau tare da yin horn aka bude mata gate
tsayawa tayi a supermarket tayi siyayya me yawa daga nan ta wuce orphanage din da ta saba zuwa
Ko da isar ta parking tayi ta fito dai dai lokacin gate man ya karaso yana waje mata sannu da zuwa gaidashi tayi dake tsoho ne tare da bude jakar ta
ta fito da kudi da ita kanta bata san nawa bane ta mika mishi baki har kunne yana mata godiya bata son godiya ta fada mishi kamar yadda ta saba fada a duk san da taje
bude booth tayi ya fara fito da kayan da ta siya by mistake wata leda ta fadi kasa kayan ciki suka zube a kasa
Daddy i want this
saurin dagowa tayi ganin wake mgn nan suka hada ido da wani mutum da bata san wane shi ba sai dai taji wani abu game dashi da bazata iya fadin maanar sa ba
mai da kallon ta tayi kan yarinyar da ta ke nuna teddy da ta fado daga cikin ledar kayan da ta siya
Murmushi tayi tare da daukar teddy tana kokarin karasawa in da suke ganin ya ja yarinyar suna shirin barin gurin
Gashi
Ta fada da dan karfi da ke sun dan mata nisa
ba shiri ta kwace hannun ta daga nashi ta karaso a guje ta amsa teddy tana fadin Thank you aunty I love you
So cute ta fada tana dariya this's all yours karki bawa kowa ta karasa fada tare da sakar mata murmushi me sace zuciya
Thank you thank you ta fada tare da yi mata peck a hannu
Juyawa tayi tana shirin tafiya sai koma ta dawo
Daddy might scold me ta fada tana miko mata teddy
Dagowa tayi tana kallon mutumin da take kyautata zaton shine daddy da shima kallonsu yake
Uhm zata iya amsa ? ta fada kamar me tsoron mgn
Nodding kanshi kawai yayi bai ce koma
Don't scold her please! bata jira taga me zai ce ba ta mai da kallon ta kan yarinyar
Daddy said you can take it Oky?
Thank youuu aunty you're so beautiful can I hug you once ?
Dariya tayi kafin tace
You're beautiful too sure!
Mini hug sukayi wa juna sannan ta juya ta tafi a guje zuwa inda motar su ta ke
Juyawa tayi ganin gate man din ya fara shigar da kayan ciki ita ma ta kwashe wasu zuwa ciki..



Hafsah!

Comments like & share

Hafsah Where stories live. Discover now