5

2 1 0
                                    


Yana zaune gefen Baba kanshi a kasa
Kayi mgn mana Abdoul ya kayi shiru wani abunne ya faru?
Dama baba kan mgnr aure na ne
Me kace? Aure Alhamdulillah Allah mun gode ma yau kai da kanka
Bai ce komai ba sai shafa keyar sa da yake
Toh yar gidan waye?
Senator Ibrahim Dahiru
Kasa rufe bakinshi yayi saboda tsananin murna yana fadin
Ay da kayi mgn dawuri da tuni wani batun ake wannam abu na gida ay kamar anyi an gama ne amma wani hanzari ba gudu ba tasan da kai kuwa?
Aa baba bata sanni ba na fi so ayi mgn da manya kafin mu san juna
Wannan koma hakane in sha Allah zan samu mamanka muyi mgn ni da kaina zan jewa baban ta da mgnr sai dai ita din Allah yasa ya amince kasan yaran yanxu baa musu dole
Ay nima bazan so ayi mata dolen ba Idan har ta furta bata so ni koma zan janye mgnr in sha Allah
Allah ya shiga lamarin

.............................

Zaune take a cikin motar ta tana tunanin mgnr su da granny daxu
duk abunda ta fada gsky bai kamata tayi mishi mummunar fahimta ba amma Meye dalilinsa na boye kanshi daga gare ta? Ko dai bashi da kudi ne ko yana ganin baza ta amince mishi ba shiyasa ya biyo ta wannan hanyar? Amma hakan bazai yiyu ba sai me iko ne kadai yake iya sakawa ayi mishi sim ya koma zama anonymous bayan haka taya zai iya bin ta duk inda ta ke ko da kuwa ta bar kasar nan sau dayawa yasha fada mata ba shi yake ganin ta fada mishi ake toh wa ke fada mishi? Idan ba Wannan ne dalilin ba toh mene dalilinsa
daukar wayar ta tayi ta shiga gallery hawaye ne ya fara zuba a idon ta hoton Mahish take kalla a tuna last haduwar su take kamar haka:
               
                                  Flash back

Ina tsoron wani abu ya same ka banji zan iya jurewa danallah karka takura sai kaje gurinnan
Haba sweet kinsan bazan taba bari wani abu ya same ni ba ko dan ke ki kwantar da hankalinki I'll be extremely careful Idan naga ma abun zai kawo mtsl barin gurin zanyi na tawo
Ni dai shawara ya karkaje ko dan mutuminnan na fada na bin ka yake duk inda yaje
Ni dai Wannan mutumin naki anya kuwa mutum ne gaba daya kin bi kin tsorata da lamarinsa
Ay abubuwan da yake ne dole na tsorata dashi bbu wani abu nawa da bai sani ba abunda ke zuciyata ne kawai bai sani ba ko relationship dina da kai ya sani sannan koma ni ba wanda na fadawa ko fateeema bata sani ba ya koma yi mun warning kan na rabu da kai shiyasa nake tsoron ya ma wani abu
Duk abunda yake ji dashi na fi shi kome yazo dashi dai dai nake dashi ba dai mutum bane, ni kinga mu bar mgnr nan lokaci na tafiya yanxu haka zuwa nayi na miki sallama in sha Allah kwana 2 zanyi na dawo bazan jira su ba
Ya karasa fadin haka yana kokarin tashi
rike hannun sa tayi gam tana fadin
Tunda ka nace sai kaje toh Allah ya kiyaye hanya safe trip sweet Allah ya dawo mun da kai lafiya be safe wherever you're stay away from girls love you!
In sha Allah love you more!
Har ya shiga mota tana bin shi da kallo bata re da tasan haduwar ta na karshe dashi ba kenan
Juyawa tayi ta koma cikin apartment dinsu tana Jin fargaba da bata san dalilin ta ba
Bayan shigar ta da wasu hours wayar ta ya fara ringing ganin sunan mahish ya saka ta dauka cikin sauri sai dai abunda taji yayi matukar girgiza ta batasan lokacin da wayar hannunta ta fadi kasa ba ita ma tabi wayar
Bata kara sanin ina kanta yake ba sai bude ido tayi ta gan ta a dakin hospital
kuka me cin rai ne ya kwace mata
yanxu shkn ya kashe shi dama ya fada mata idan har bata rabu dashi ba ko ne ya same shi ita ce sila
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un me yayi ma ne yasa aka kashe ni mahishh
Ta fada da karfin gaske dai dai lokacin faterema ta shigo Jin muryar ta har waje
Danallah ki yi shiru kiyi hakuri in sha Allah komai zai wuce
Fateema ya kashe shi ya kashe Mahish dina Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un zuciyata zata fashe me ya mishi Meyesa zai kashe shi fateema Meyesa Danallah ya dawo mun dashi bazan iya jure wannan radadin ba my heart is burning I can't take this fateema
Ta karasa fada cikin muryar kuka da duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata
rike ta fateema tayi ita ma tana hawaye ganin yadda lokaci guda hafsah ta sauya sumbato ta ke da ita kanta bata san tanayi ba
Sai da suka tai kwana 3 a hospital ana kara mata ruwa kafin su koma gida
 

                               End of flash back

Hawaye ke zuba a idon ta tana tuna irin soyayya r ta da mahish shekara 2 kenan da faruwar hakan
A duk lokacin da ta tuna da cewar shi ya kashe Mahish sai tsanar mutumin nan ta karu a zuciyar ta taya zata bawa makashi dama?
Ta fada tare da goge hawayen fuskar ta
ajje wayar tayi gefe ta gyera steatbelt ta fara driving a hankali har ta karasa gidan su Ummi school friend dinta, kiranta tayi ta fada mata cewar ta fito ta karaso bata dade da ajje wayar ba ta fito
Hafsahtuu
Hajiya ummi ykk
Kalau kalau y Hutu
Alhamdulillah
Y karatu ance karatu a turkey ba wahala
Ah inji wa
Haka dai naji ance yafi karatu a china sauki ni bansan ma taya na yarda na tafi cen ba da ku na bi
Sai yau kika San haka ay tun kafin mu tafi nake fada miki abun da yanxu saura yen kwana ki mu gama gaba daya
Haka ne amma toh y Jin dadi kinga yadda kika yi bul bul dake gsky dole ki ban sirri ne kike sha
Na shiga uku ne kuwa zan sha
Toh ay shkn an kusa biki na
Haba Danallah
Wlh saura 2 weeks
MashaAllah Allah ya nuna mana
Ameen ya rabbi amma dai zakiyi ashobe
In sha Allah yaushe zaa siya ay naga ma kamar time ya kure
Ehmn ke ce ay Idan an miki mgn bakya reply shiyasa nan fada miki ba amma naso fada miki tun tan da aka sa rana
Toh dai yanxu yaushe zaa siya
Ay amma siya I think jibi zaa kawo irin na boxes dinnan na sa ayi amma nasa harda sunanki
Toh yauwa dai har zan ce ni koma nawa ne
85k da atampa,fabric sai material din bridal shower
Kinga Ina amsa sai gurin dinki tura miki zanyi ko cash
Aa dai gwara turawar
toh bari mu karasa inda zamu sai na tura miki Ina su Malika kuwa
Suna nan wlh bakwa mgn ne
Nayi loosing numb su duka tunda na canza
Ay kuwa suna neman ki don ku jiya da mukayi waya da Sakina ta tambaye ni ko kin dawo su ay sai next week zasu dawo
Sai ki ban numb su muyi mgn ko dayake ma suka dawo ay zamu hadu

Haka dai suka cigaba da hira har suka kara Cubans restaurant

Comments like & share

Hafsah

Hafsah Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang