4

2 1 0
                                    




Kiran sallar asuba na farko ne ya tashe ta
a hankali take kokarin mikewa Jin jiri na neman fadar da ita yasa ta komawa ta zauna rike da kanta dake mata ciwo addua ta karanta tare da shafawa a kanta sai a lokacin ta iya tashi zuwa toilet alwala tai ta fito sallaya ta shimfida tare da saka hijab raka'atainil fajr tayi ta zauna har aka tayar da sallah a masallaci ta bi jam'i
Ko da idar adu'o'i tayi ta koma kan bed ta kwanta

Ba ita ta tashi ba sai 11 na safe ringing din wayar ne ya tashe ta tsaki tayi ta sa hannu ta dauko wayar
ganin sunan dake screen yasa ta Sakin murmushi lokacin guda
Hello grannyy Ina kwana?
Ba lfy ba ace ki dawo garinnan ki kasa sanar dani
Haba granny na ba haka bane jiya fa I was planning to surprise gashi an bata mun surprise dina wa ya fada miki
Au sai an fada mun zan sani jikina ne ya bani kin dawo
Hmmmm ni dai ban yadda ba ay yau dawuri zan zo na wuni
Au wuni zakiyi ba kwana ba
Aaaa ay ba kwana ba watanni zanyi ta karasa fada tana dariya
Hira dai sukayi ba me tsayai ba ta kashe tashi tai zuwa toilet tai wanka ta fito
Sanya boubou tayi ta atampa tare da yin dauri ta fito
Good morning baba good morning mama ta fada tana karasa sakkowa kasa
Good morning Auta y kike tashi
Alhamdulillah
Baba fita zakayi
Eh Muna da meeting yau dawuri kinsan fa zabe ya karato
Hakane baba baka tsaya takara ba wannan karon
Ay har next government I'll stil be in the same position as senator sai dai ko Idan Ina so a canza mun
Aaa baba hakan ma yayi ay gwara a barma wannan ko mama
Eh gsky dai a hakan ma baka hutawa Ina ga an canza ma
Dariya yayi kafin yace
I'll get going and I might come back late
Toh Baba a dawo lfy
Allah yasa ya fada sannan ya fita

Breakfast ta koma tayi sannan ta dawo parlor
Mama yau zan tafi gidan granny dazunan muka yi waya
Ay dama nasan sai aysha ta fada mata kin dawo she has been expecting you ya kamata kije dama yau nake shirin tura ki
Amma fa mama kwana zanyi
Ay ko baki fada ba nasan hali bazata  barki ki tawo ba
Mstl ta daya da zaman gidan granny yanxu zata fara mun mgnr aure yaushe zanyi wa zan aura
Au ke baki so a miki wannan mgnr ay ko batayi ba ni zanyi how old are you ?  Shiru tai nata ce komai ba
Tambayar ki nake
23
Shine ke baza a miki mgnr aure ba anya kuwa lafiyar ki
Haba mama a bari na gama school mana
Anki a bari din nace anki a bari din

Tashi tayi tana kunkuni ta haye sama
Kayan ta hada a yer karamar trolly ta yafa mini mayafi tare da daukar car keys da wayar ta ta fito
Sakkowa tayi lokacin mama bata nan koma wa Dayan parlor dake kasa tayi nan ma haka
ganin haka yasa ta hawa sama parlor farko ta shiga nan ta iske ta da wasu baki sai koma PA din ta da alama meeting suke kan batun taimakawa mata da mama takeyi
Gaida su tayi sannan ta radawa mama a kunne cewar ta tafi gidan granny
A dawo lfy tace mata sannan ta fito
Deciding din tayi yau dayar motar ta zata hau da Baba ya bata last birthday ta
Bude booth din motar tayi tasa trolly kirar Luxes 2021 and edition gold in color tare da shiga gaban motar ta tada ta bude mata gate akayi ta fice a guje kamar zata tashi
Sai da tayi nisa sannan ta fara tafiya a hankali
Kunna karatun Sudais tayi tana ji har ta karasa Asokoro inda gidan yake horn tayi gateman ya bude
Parking tayi ta fito ko tsayawa daukar trolly batayi ba ta shige ciki
Grannyyyyy ta fada da karfi dai dai lokacin da ta karasa shiga ciki
Cen sai ga wadda take kira da granny ta fito karasawa tayi suka rungume juna
Kakata nayi kewar ki sosai
Ni da kika guje ni
Haba Kakata inji wa jiya da na dawo kwana daya nayi a gida nace ni dai gurin kaka ta zanzo
Shine zuwan naki ba jaka kenan ba kwana zaki ba
Haba ni na isa jaka ta na mota ba kwana ba kwana zanyi ay da kanki zaki kore ni

Jan hannunta tayi suka koma parlor nan ma suka cigaba da hira kamar yadda suka saba cen ta ce
Ni Ina Wannan mutumin naki
Wa kenan
Wanda kika fadan yana miki mgn amma har yanxu Baki san ko wane shi ba
Murmushin dake fuskar ta ne ya dauke ta dago a dan firgice
Bansan inda yake ba bana koma kaunar sanin haka Kakata ku bar zan cen shi
Meyesa baki son mgnr shi a ganina shi ne me sonki tsakani amma duk wannan samarin n a yanxu sai dai su dubi zubin da Allah ya miki ba wai har zuci ba ba wai sanin shi nayi ba amma a iya abubuwan da kike fadan shi ba mutumin banza ba ne ke da kanki kin sha cewar baya taba bari mummunan Abu ya same ki
Amma duk da haka....
Ki saurare ni da kyau Hafsah na fiki sanin rayuwa ba wai na yarda dashi fiye da ke bane Ina miki mgn from my own experience akan maza shekara ta nawa da kakanki amma kun taba Jin kanku bbu wanda zai ce gashi ya taba ganin mun samu mtls dashi har ya koma ga Allah koma ba wai bama samu sabani bane sai dai munsan yadda zamu yi sulhu mu bawa juna hakuri dukkan alamu sun nuna bawan Allah yana sonki so ne tsanani ba sau daya ba sau biyu ba yasha kare ki daga abubuwa kala kala dake kanki sai daga baya kike realizing hakan duk ya boye miki kanshi amma ya fada miki yayi hakan saboda yana gudun karki guje shi duk da hakan ba hujja bace amma ina so ki nutsu ki mgn dashi ki bashi dama ko da sau daya ya miki cikakken bayani kusan shekara 4 yana bin ki a tunanin ki wa zai bi ki har na tsawon Wannan lokacin ? wane wanda ba sonki yake tsakani da Allah ba zai jure jira har tsawon haka? Ke kanki kinsan bbu ba koma Ina cewa ki so shi ko ki aure shi bane sai dai Ina baki shawara a matsayi na na wadda ke don cigaban ki ba koma Ina cewa ki aureshi saboda Ina sonki dashi ba sai dai ki nutsu ki San wa zaki bawa dama a rayuwar ki saboda yanxu ne Zaki zabawa kanki rayuwar da zaki gaba....




Hafsah

Comments & like

Hafsah Where stories live. Discover now