DASHEN ZUCIYA

1.6K 59 2
                                    

💔 *DASHEN* 💔
       *ZUCIYA*

   
   
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_👄

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

1⃣

*FLORIDA united States*

"Bisma Kullun kara kyau kike gashi ana karatu amma ke kaman bakiyi sai wani kiba kikeyi, nikam kaman ana miya da namana, kinsan yau lectures dinnan damukayi wallahi bakiji yadda nikeji ba kamar in zura takalma na in gudu kasata Nigeria
Dayawa mutane suna ganin kaman cin banxane zuwa karatu kasar waje wallahi babu komai sai wahala, dadinshi dayane shekarun karatun badaya bane da gida Nigeria".

Itadai bisma kallonsa kawai tak'e duk yabi ya rude saboda karatu itakoh koh a jikinta don ita tafison tayita jin chargi a brain dinta, fashewa tayi da dariya lokacin da Hamdan yayi sipping ice-cream ya juyo da sauri kedawa
"Keda lafiyanki kuwa kiketa dariya kamar wata tababba?".

"Hamdan na lura gaba daya kai ragone, saboda Dan wannan karatun da kak'eyi shine duk' kabi kake damuna, Allah yabani hakuri nida nake karanta (MBBS Medicine) kuma gashi am still looking more healthier than you, kasan yadda nake kashe dare nake karatu wallahi bana samun cikakken bacci".

"Naji din ni ragone kek'uma ba Raguwa ba shiyasa naga Kullun tafe kike kamar wacce akayiwa sata, Kullun cikin sauri kike wai shin intambayeki mana?".

Gyra zama tayi ta juyo tana kallonsa "Ina sauraren ragon namiji"?
Wani littafi ya wurga mata ta tashi tana dariya,
"Joke apart Bisma wai meye dalilin ki na karatun likita?".

"Hamdan kenan inada dalilai masu yawa, tunda ka bukaci kaji toh yau zan warware maka komai, nak'asance Mara tausayi, sannan da wuya Abu baya sani kuka sai wata rana aka kwantar da Nabil dinmu a asibiti dake zamfara Gusau Wato federal medical centre, da shigarmu naga wata mata tanata kuka tana surutai, rungume da danta amma babu Wanda ya kulada ita bare yasan halinda take ciki, saboda talauci dayake tafe dasu Tuni na shagala da kallonsu wasu zafafan hawaye ne suka gangaro daga k'warmin idanuna".

"wani wawan shaka nayima wata nurse wacce taketa surfa musu Zagi, nace ke wace irin Mara imani ce? Wace irin dabbace ke wacce batasan darajan mutane ba?
Kina ganin wannan matar kika banzatar da ita bakiga halinda danta ke ciki bane?
Nasha Alwashi saina zama likita don intaimakawa marasa lafya da gajiyayyu".

"Tuni mutane sukayo kanmu suk'ayi mana cha sai a lokacin Ummi ta hangoni na shake Nurse cikin mutane ta kutso kai
"Bisma da lafiyanki kuwa malamar asibiti kika kama ma wuya?"
Ummi ki kyaleni da ita narasa meyasa wasu likitoci suke wasa da aikinsu Ummi Dan Allah dubi wannan yaron suma yakeyi amma anrasa wanda zai mishi gata? What a pity dagudu nabar asibitin, nayi waje ina kuka Bayan an gama duba Nabil ne muka koma gida".

"Nanna sanarda Abbeey cewa nidai aikin likita zanyi don in taimakawa mutane musamman ma talakawa masu karamin karfi nayi alkawari koda zan mutu ta hanyan taimakone saina yi karatun likita".

"Dayake shi mutunne mai son taimako haka ya goyi bayana har nazo kasar Florida USA Dan inyi karatun likita shiyasa kaga bana wasa da profession dina".

Hamdan shuru yayi yana jinjina k'wazo da jarumta irinnan Bisma,
"lallai kinada kyakkyawan niyya kuma insha Allah, Allah zai miki jagora Allah xai taimakeki"
"Amin" Bisma tace nan suk'ayi sallama da juna kowa ya wuce hostel dinshi cikeda kewan juna, Kullun haka suke haduwa har wata halak'a mai girma tashiga tsakaninsu Wato *LOVE* lokacinda Hamdan ya sanar da Bisma bakutar sa taji wani mugun dadi da mamaki Ashe amintarsu da Hamdan zai iya zama Soyayya?

DASHEN ZUCIYAWhere stories live. Discover now