DASHEN ZUCIYA PG 30

255 5 0
                                    

💔 *DASHEN* 💔
       *ZUCIYA*

   
   
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_👄

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘


         3⃣0⃣
_*This goes to basira one of our gigantic FAN Am here by saying my big condolence to you for the lost of our beloved brother may Allah forgive him may Aljanna firdausi be his final abode AMIN*_👏🏻




Wani murmushi tasaki tareda komawa kusa dashi ta kwanta amma gaba daya zuciyarta tana wajen baitu datake fama da ciwo k'warai Wanda Bisma tarasa dalilin hakan, bayan sun kwanta bacci ne BISMA ta lallaba ta mike tafara jero salloli tana yima baitu Adu'a wacce Allah yabata iko, Shiko NURU wani
Bacci yakeyi.

NURU yana zaune a kujera bisma tazo ta wuceshi tana murmushi nuru tana daga mata hannu cigaba yayi da karanta jaridarsa, bayan fitarta ne yaji karar waya tuni ya dauka ganin lambar bisma hello shine abun da yafara cewa Wanda yakira yace kazo wajen DANGASKE NIG LMTD wata motace tayi hatsari kuma inajin matar dake ciki ta rasu cikin rudewa nuru yace whatt!!!!!!!

W firgice ta mike yana salati juyawan daxaiyi yagansa adaki bisma kwance kusa dashi, tanata bacci cikin kwanciyan hankali.

Wani numfashi yasaki ya koma ya k'wanta yana mai ajiyar zuciya, amma kuma tsoro fal da fargaba acikin zuciyarshi.
Ba NURU kadai ba hatta ni humairah saida zuciyana ta karaya.

Da asuban farko Bisma ta tashi taga nuru zaune ya nade hannu cikin gaggawa ta matsa kusa dashi tana "NURU lafya kake? Dan Allah lafya dagani bakayi bacci ba dubi yadda idanunka suka kumbura sannan sukayi ja pls my dear husband tell me wat is the problem?"
NURU ya dago sai jitayi hawaye suna zuba kamar daman jira suke tayi magana.

Bisma ta kara rudewa "Ga gayamun abunda ke damunka Dan Allah"
NURU ya fashe da kuka yana cewa "Bisma karki barni bazan rayu ba kece mahadin zuciyana bisma don go and leave me I know definitely am gone too" itadai bisma a rude take tarasa dalilin dayasa NURU wayannan kalaman gamida zubda hawaye.

NURU yace "Nayi mafarki Bisma mai tsantsar rikitarwa, idan kikaji tilas zakiyi kokawa amma nabarwa zuciyana banaso kiji abunda zai tada miki da hankali" bisma ta rikemai wuya tace "you most tell me wat is happening" tana jijjigashi tana kuka.

NURU yace "Nayi mafarki Allah ya dauki rayuwarki shiyasa kikaga ina kuka don tabbas da ace ba mafarki bane bisma wallahi da tuni na biki na kashe kaina bisma inacikin matsanancin tashin hankali".

Bisma tayi wani ajiyar zuciya tace "Amma ka tadamun da hankali Wallahi, inace mutuwa akayi ka kasa gayamun, Wato kanaso kacemun tsoron mutuwa kakeyi? Toh Kasani "Kullu nafsin za'ikatul maut" dukkan mai rai mamacine kuma idan lokaci yayi babu makawa duk soyayyar dake a tsakanina dakai Kasani Allah daya haliccemu yafika sona kuma ina maraba da mutuwa akoda yaushe".

Zare ido NURU yayi yana k'ara sautin kukan sa Wanda nikaina saida nakara karaya da kalaman bakin Bisma, nikaina saida na goge wasu hawaye.
"Bisma kiyi fatan mu mutu rana daya karki tafi kibarni lokacin danake matukar son mu rayu da juna Kituna kina dauke da farincikin rayuwanmu, nidake bisma rana daya zamu rasu"

Bisma tayi Dariya tace "Kamanta yadda mutuwa take raba d'a da mahaifa haka take raba masoya, ma'aurata, abokai harda aminai NURU ba'a mutuwa sai lok'aci yayi idan Lok'acin ka baiyi ba zaka zauna daram a duniya Fatana Allah yasa mucika da Kalmar shahada"
Amin yace yana karewa bisma kallo mikewa tayi ta dauro alwala tace "Mai tsoron mutuwa tashi maza kayi sallah kar tazo ta riskeka yanzu don arana mutuwa tana  ziyartar kowani gida sau saba'in taga waye akan layi".

NURU yace "pls chapter close naga kinaso kimaida abun wasa" haka sukayi sallah kowa yafara shirin tafiya wajen neman halalinsa
Bayan sun gama cin abinchi ta mike tace "Nina tafi pls karufe koh ina kila bazan Dawo ba" NURU yakara kallon Bisma yace "madam zolayan ya isa haka"

Haka tafita tana Dariya amma wani kallo takeyi wa NURU, fitanta keda wuya NURU yakirata yace "Amma shine kika kasa shan maganinki koh kuma kindauko gashi kan dinning"

Oh barina Dawo insha haka bisma ta Dawo cikin gaggawa tasha maganin ta kalli NURU tace "Hankalinka ya kwanta barima kaga inzauna" guri ta nema tafara kiran Ummi tana sanarda ita halinda baitu take ciki sannan ta tambayi lafiyar Ruma kusan yan'uwa saida takira ta mike tace "Na wuce" NURU yace "Allah ya kaiki lafya".

Fitarda keda wuya nuru yakara kiranta yana cewa ki kulamun da kanki yana mata hiran soyayya sai Dariya takeyi, wani kara yaji Wanda lokaci Guda yadaina jin maganan Bisma yayi maganan duniya amma shuru kakeji, tuni ni humairah zuciyata ta tsinke na lallaba na ajiye wayata don ingarzaya ganin abunda ke faruwa.

DASHEN ZUCIYAWhere stories live. Discover now