Dashen zuciya 36-----END

1.1K 22 1
                                    

aka NURU yaci gaba da harkokinsa amma yakasa sanarda Baitu cewa aurensu ake shirin yi nan bada jimawa ba, hajiya ce zaune cikin farfajiyar gidan inda yaranta mata masu aure wani gida suka kawo mata ziyara itada hajiya wacce akafi sani da Rabi, farace amma ba Sol ba, Ta auri Alhaji Usman Wanda akafi sani da ZUNNU-RAYN, Tun tana yar shekara sha uku haka tazo gidansa tazuba yaya har shida, batasan meye kishiya ba, bare yayanta Susan yan uba ba.

Baitu ce tazo wucewa ta gaidasu tana washe baki, mommy tace "Dadina da baitu ak'wai aukin dariya komai nata yana burgeni babu inda tabar Bisma, Shiyasa na labari ya iskeni cewa yaya NURU zai aureta hajiya bakiji wani irin mugun dadii danaji ba" hajiya tace "Uhumm kukenan daku kasan inda ke muku ciwo banda NURU gaba daya bayata yarinyarnan nidai fatana karya wulakanta yar mutane muji kunya".

"Hajiya kenan banda abunki ai inace zata tare a gidanta ne?"
Hajiya tace "Meeeeeh inji akuya ai cewa yayi tazauna damu Wato tayi mishi kan kanta toh zanyi maganinshi saiyazo dakanshi yace bani matata mutafi kannan Baitu zata koma" Ni'ima tace "Hajiya Wallahi haka za'ayi Wato yaganta Yarinya bata cika mutum ba to koh saiya yara".

Kowa dai acikin k'anninsa basuji dadii ba, shiyasa kowacce ta tofa albarkacin bakinta..... Haka sukayi hira harnawani lokaci harsuka gaji da jiran nuru kowacce mijinta yazo ya dauketa, baitu tashiga damuwa k'warai saboda zancen datakeji na aurenta da NURU yaxama dole insamu hajiya insan abunda ake ciki.

Washe gari Baitu ta shirya tsaf zasu wuce makaranta hajiya ta kalleta tace "ke ina zuwa?" Baitu ta kalli hajiya cikin Rashin fahimta "Hajiya mak'aranta zani mana"
"kizauna yau ya k'walam zatazo saboda shirye shiryen aurenki".

Baitu tasaki baki tace "hajiya wai waye zaiyi aure naji Anata zancen aure? Lallai Ashe munada shan biki baitu tafara murna duk tana sane takeyi don ya zuwa yanzu tasan komai, Hajiya ta zaunar da ita tace "Kece zakiyi aure zaki auri yaya nuru dafatan kina sonsa?"

Baitu ta kwabe fuska tace "nida yaya baya sona komai nayi ban iyaba nidai gaskiya saidai a chanza mun wani bashiba"
Tafara buga kafa tana kuka haka hajiya ta lallasheta ta kwantar mata da hankali harta aminche".

*SAURA SATI BIYU BIKI*
***********
Hajiya ta hado akwatina dagani na fade, ya k'walam kuwa tadanyi tanadi, gashi an asace musu shanaye inba hakaba sa guda ake yankawo a biki, haka iyayen bisma sunyi abun azo agani inta kama ayi gulma kayane nagani na fade saidai kash basusan cewa baitu bazata tareba amma duk bata baci ba haka aka ajiyesu inda bazasu lalace ba, Ummi tana masifan son NURU shiyasa bata mantawa dashi kusan koda yaushe saiya kai musu ziyara sannan ga kyauta dukda ba mabuk'ata bane, hajiya taji dadi tace "Haka akeson mutum yayi kyauta ta dama ba tareda Hagunsa yasani ba fatana Allah yayima wannan yaro albarka.

*KWANA UKU BIKI*
*********
Dayake ba wani taro za'ayi ba, Amma baitu taji gyra sai kunga kawayen baitu yan kuci kubamu wasu koh irgan dangi basu faraba, baitu tasha gyra iya gyra mommy da ni'ima sunyi kokarin yin mata komai, haka aka shirya k'asaitaccen walima acikin gida, Ango NURU in Baku labari yaki sanarda kowa sai wayanda sukeda link da gidansu, su hamdan da kausar sune kan gaba, haka aka shirya walima babu nuru, baitu bata damuba itada kawayenta sai hira suke suna dariya waaxin da akayi musu yashigesu kwarai, ba akan komai bane sai biyayyan aure Sanin kima da darajan miji yan'uwan miji, tsarekai daga fadawa halaka.
[2/22, 8:19 AM] Melody🤸🏻‍♀🤣: 💔 *DASHEN* 💔
       *ZUCIYA*

   
   
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_👄

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘

        3⃣7⃣

Haka aka watse kawayen amarya su Ashwa ana can ana ta hada hada, ya k'walam ce zaune tacewa hajiyan NURU "koh kunsan Baitu ba sunanta na Asali bane" hajiya tace "kai haba duk daukanmu ai sunanta kenan?" Ya k'walam tace "Ah ah sunanta *MUJEEBA JOOD'A*.
Tuni hajiya tasanarma NURU cewa baitu sunanta mujeeba haka aka sanarda kowa sunan Baitu na asali.
Kuma baitu tasan sunanta amma ta boye kai Fulani sai abarsu, NURU ne ke wannan maganan kuma a rayuwarsa yana masifan son sunan don har cewa tayi sunan yarsa tafari mujeeba dansa na biyu mujeebu, washe gari ajayiwa baitu kwaliya nagani na fade haka tadinga shigan kaya iri daban daban, misalin karfe biyu da rabi na rana aka saura aure
*NURU DA AMARYARSA MUJEEBA*.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 09, 2017 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DASHEN ZUCIYAWhere stories live. Discover now