DASHEN ZUCIYA Page 22------25

446 6 0
                                    

[2/10, 10:13 AM] Melody🎤🎤: 💔 *DASHEN* 💔
       *ZUCIYA*

   
   
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_👄

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘


         2⃣2⃣

Cikin sigar rudewa sukayi kansu, da gudu tuni aka sanarda yan'uwa kowa hankalinsa ya tashi tuni mahaifin Hamdan yafara daya Sanin abunda ya aikata cewa yake "Hamdan karka mutu kabarni cikin kunci, ka kadaine Dana namiji magajina yaza'ayi kazabi mutuwa akan Rayuwa saboda mace, kadawo Dan Allah Wallahi zanyimaka abunda kakeso zan yarda ka auri Rumaisa Tunda itace zabinka" kuka yakeyi wiwi inda yaya salim yaji kamarya shake mahaifin hamdan wani kukan kura yayi yace Wallahi baxan barkaba Kaine sanadin mutuwar kanwata Kasani koda rankata kaf abunda muka Tara zai kare sainayi kararka" mahaifiyar Hamdan tace "Hamdan karka mutu kabarmu cikin kunci da fargaba da mutuwarka kwara mu aminche da auren ka da Rumaisa Dan Allah kayi magana Hamdan munyi maka Alkawarin sama maka farinciki tun ranarda kazo duniya Dan Allah ka farfado pls and pls".

Shirin dibansu akeyi Tunda rai yariga da yayi halinsa hamdan ya bide ido Wanda suka kada sukayi jajir yace, "hajiya Ku aminche mun na auri Rumaisa itace muradina, karkuyi gaggawan rabamu, tuni sukaji wani irin dadi, lokaci gida Rumaisa itama ta bude fuska tana zubda hawaye da gudu ta rungume yayanta tace "Yaya Hamdan masoyina ne bayaso ya gujeni Lokacin da abu ya sameni ba laifin kowa yaya munyi hakanne don abarmu mu kasance tareda juna koda kowa zai tsaneni nasan hamdan will always be by my side we are bound to be together for life" share mata hawaye yayi tuni hamdan yaje wajen yaya salim Yana kuka yace "kayafe mun babban yaya banyi haka don muzgunama rayuwarka ba nayine don in sama ma kaina yanci sannan iyayena su aminche da aurena da Rumaisa" yaya salim yaji wani mugun tausayin Hamdan yace "karka damu aure dakai da Ruma babu fashi nanda sati biyu".

Nan kowa sai murna yakeyi amma ran mahaifin Hamdan baiso ba, lokaci guda yaji ya tsani Rumaisa da haka ya cusawa kuwa kin ruma, Bisma kuwa ba karamin tashin hankali tajiba da akace musu Ruma ta rasu haka ikram nabil kuwa ai kuka saikace Wanda komai ya kwance musu  haka su nuru sukaji wannan ciwon, Kausar kuwa ai yakasa koda kai ruwa bakinsa saida yaji comfirm komai yayi daidai, Nan aka cigaba da shirye shiryen biki masu gyran jiki aka kira nimadai ba'a barni a bayaba saida na tabbata nima an gyrani Kwarai saboda koh nima zanyi market,
Amma Rumaisa gaba daya bata cikin hayya cinta sabanin su ikram da bisma da suketa farinciki.
An kawo akwatina Wanda Yazama al'adar bahaushe Wanda inhar ba'ayi ba saiya zama abun zunde da gulma.

*KAMU*
Ranar juma'a ne kamu Anata shiri takota ina, ready made din kaya aka yimusu oda daga KANO harda hand fan da purse Wanda kudinsu yakai kimanin naira dubu sittin sittin, na Rumaisa yafita daban saboda arufe annoban daya sameta, mai dogon hannu akayi mata Farincikinta data daman ciwon banda fuska nan aka kira musu mai makeup HummiesTouch ce taxo ta gyra Amare Wanda yakai kimanin naira dubu hamsin hamsin saboda kwana biyu ne da ranan kamu da ranan biki.

Tuni yan'uwa daga dagin Ummi Dana daddy Dana mahaifiyar su ikram, anacan ana shirya wa amare gida, Rumaisa itama anan Gusau zata zauna amma anyi hakanne don dazaran anyi auren kasar Miami xasu tafi don ganin kwararren likita akan ciwon fata,
Don Hamdan bai yarda dawani zaman kauyen mada ba, haka aka fara shirin tafiya abun haushi abun farinciki, shine a dangin hamdan babu Wanda ya isa wajen reception dinnan, sai Yan tsiraru haka akayi kamu amare da angwaye abun azo a gani, haka aka yi taron aka watse cikin kwanciyan hankali.

*Ranan Biki*
An shirya tsaf ana hidimar biki, gida yacika misalin karfe biyu na rana ne aka daura aure.
*NURU ZUNNU-RAYN da Amaryarsa BISMA IMAM HASSAN*
Daganan aka dawo kan *HAMDAN MUNNIR HAMEED Da Amaryarsa RUMAISA IMAM HUSSAIN*
Bayan nan aka daura auren *KAUSAR ADAM Da Amaryarsa IKRAM IMAN HUSSAIN*
Dubban daruruwan mutane suka ziyarci wannan bikin har daga gidan gwamnati gwamna ya aiko Babangida Mayanan Gusau donya wakilceshi, haka akayita busa sarewa garin Shikafi ba masaka tsinke abunda zai baka sha'awa Shine yadda naga jar fata Wato turawa.

DASHEN ZUCIYAWhere stories live. Discover now